MAHREEN PAGE 1

244 18 5
                                    

💅  *MAHREEN*  💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



PAGE 1

*Assalamualaikum makaranta novels d'ina Kuna Ina? ku marmatso ku ji ga sabo ya zo da zafin shi, kar ku bari a yi babu ku, coz I promise you wannan salon daban ne, Kun kuwa San in na ce daban ne daban d'in ne ko? Ki hanzarta kar se an yi nisa ki ce a baki daga farko. Allah ya bani iKon rubuta alkhairi ya baku iKon d'aukan abin alkhairi a rubutun nan mai albarka. Son so fisabillah❤️✍️*

Kowanne d'an Adam ya na fuskantar jarabawar rayuwa gwargwadon yanda Allah mad'aukakin sarki ya hukunta kuma ya tsara masa,ni MAHREEN na sani Kuma na yi Imani da Allah, na yarda cewa qaddarar rayuwa ta ce ta zo a haka, ba zan iya sauya dik abinda Allah ya hukunta zai same ni ba, sanin haka ne ya sa a kullum nake miqa cikakkiyar godiya ta a gare shi, nake neman taimakon shi akan dikkan wani abu a rayuwa ta komai girman shi, Kuma komai qanqantar shi.

Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi a daidai lokacin da na gama wanki na a maqotan mu, na tattara robobi na da na d'auraye na had'e su waje guda, tsugunnawa na yi a bakin rijiyar na fara wanke qafata da fuska ta da ruwan da na zuba a buta.

Ba zan tab'a manta wannan babbar ranar ba a rayuwa ta, mai d'imbin tarihi, rana ce mai matuqar mahimmancin a gare mu da ni da Yah Maheer d'ina.

Yammace sakaliya, garin na kano ya yi dad'i saboda yanayin da muke ciki na sanyi,na jima da dawowa gida inda a can gidan maqotan mu na baro wanki na da basu bushe ba, na taho gida domin na yi wanka na ci abinci na yi kwalliya kamar yanda na saba, fitowa ta daga wanka ba jimawa aka d'auke wutar lantarki, cikin Jin haushin d'auke wutar da aka yi na miqa hannu na janyo 'yar qaramar fitila mai d'auke da batira guda uku, kunna ta na Yi, nan da nan kuwa haske ya gauraye d'akin mahaifiya ta Wanda yake d'auke da makeken gado da duk Wani abu da ake da buqata na yau da kullum kadaran kadahan dai, domin mu ba masu kud'i bane, sannan ba talakawa bane, mu na da rufin asiri daidai misali alhamdulillah.

Kallon fuskata na yi a madubi Wani qayataccen Murmushi ya k'wace mini hushirya ta ta bayyana, idanu na masu zara zaran gashin Ido suka qara haske a cikin hasken qaramar fitilar.

Hoda na d'auka na shafa sannan na Saka janbaki na goga Kwalli tare da taje gira ta da ke Cike da gashi Mai kyau, ban jima da kammala Kwalliya ta ba na duba wajen window na ga yanda gari ke qara yin duhu, cikin sauri na miqe na d'auki kaya na na Sanya Wanda ya kasance leshi ne ja da adon farar fulawa da fararen dutsina, sai na ja farin mayafi na na yafa, qofar parlourn Mama na zo na ja na tsaya Ina tinanin wa zai raka ni deb'o kaya na a duk fad'in gidan nan?

Hayaniya na dinga jiyowa a qofar gida alama ce ta cewa mutanen gidan mu da d'aliban da ke zaune a unguwar mu Wanda ke karatu a makarantar BUK sun hallara Dan yin sallar magariba, yayata na hango Mai Suna Ummul khair wadda muke Kira da Addah Ummu ,wajen ta na nufa  cikin karya murya da langwabar da Kai irin na mai neman alfarma na ce,

"Addah Ummu Dan Allah ki raka ni na deb'o kayana gidan maman Ihsan, kin San ba zan iya zuwa ni kad'ai ba tsoro nake ji"

Yanda na shagwab'e fuska da murya ne ya Sanya ta kallo na Cike da hara ta dungure min goshi sannan ta ce,

"Mu je, 'yar rainin hankali, matsoraciyar kawai, kin San ba Zaki Iya zuwa ba ki ka bar wankin naki ya Kai war haka, ko me ma ya Kai ki yin wanki a can oho ga gidan ku se kin je Wani wajen Allah ya shirya ki"

Ni dai ban ce mata komai ba duk surutu na, saboda kar ta qi raka ni, se kawai na yi gaba na Jira ta ta shirya ta zo mu wuce, Ina tsaye na ji Yara na murna da Kiran

"Yeeehh ga Yah Maheer...ga Yah Maheer"

Murmushi na yi, na kauda kai na, Ina hasaso kamalar shi, cikin zuciya ta babu komai banda girmama kirkin shi da mutuncin shi, mutum ne shi mai halaye kyawawa, irin kyawun da sai mutum ya jima ya na bincike kafin ya samu me irin halayyar shi, a Ido idan ka gan shi sai ka ji girman shi da kwarjinin shi sun baibaye ka, balle ya bud'e baki ya yi magana, a Koda yaushe maganar shi Cike take da Kamala,ilimi, wayewa, da Kuma sanin ya Kamata.

MAHREEN Where stories live. Discover now