MAHREEN PAGE 14

39 11 3
                                    

💅   MAHREEN   💅









WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 14










Qafafun Suwaidatu na gani daf da inda na sanya pillow, a hankali na ke bud'e ido na yanda ba zata gane idon nawa biyu ba, kallo na ta yi na d'an wasu daqiqu kad'an sai ta juya ta koma parlour cikin sand'a, da ganin haka sai na ji jiki na ya yi mugun sanyi, na kasa yarda da abinda na gani.

Menene ma'anar yi min sand'a?
Me za a aikata min?
Me ke faruwa?

Wad'annan tambayoyin na dinga jerowa kaina, tashi na yi a hankali nima na zauna yanda ba za su ji ni ba, na kai kunne na wajen prlour dan na ji me za su tattauna akai na, ji na yi murya qasa qasa Suwaidatu na sanar da su cewar bacci nake, da jin haka suka d'auki cin nama na.

Ina zuba musu abinci kad'an,
Ina wa Isma'il fad'a kamar ni ce gaba da shi,
Ina hana shi tab'a abubuwa sai in ta masa gori akai, sauran abubuwan da ban san sanda aka yi su ba.

Ita kuma Suwaidatu sai cewa ta yi ai bana wasa da ita sai dai na ja Hauwa'u d'aki mu yi ta hira, ko in Yah Maheer na nan mu bar ta a waje mu shige d'aki.(Yaran da har 'yar carafke muke yi da yar burum burum da sauran wasanni na yara)

Shawarwarin yanda za ta dinga kula da kan ta da kuma abinda za ta dinga yi min idan haka ta sake faruwa a tsakani na da su ta basu, sannan ta musu sallama ta tashi zata tafi, na so matuqa a wannan lokacin na je na tinkare su da maganar amma na danne na ci gaba da baccin qarya na har ta fita, abun na raina ya na b'ata mim rai na kasa cire maganganun su a raina har dare.

Yah Maheer ya tafi qauyen da ya samu aiki dan ganin yanayin wajen dan haka a daren haka na kwana cikin baqin ciki ban samu mai kwantar min da hankali ba.

Washegari da sassafe na yi wanki na shanya a igiya na hau yin sauran ayyuka na raina a matuqar b'ace wanda ya sanya Suwaidatu fara shan jinin jikin ta, domin kuwa hatta da murmushi kasa yi mata na yi, saboda qaryar da ta min, ban tab'a banbanta ta ita da Hauwa'u ba, iyaka watarana ina kiran Hauwa'u d'aki dan ta taya ni gyaran d'akin da ita Suwaidatu ba zata iya ba, kuma ba dan komai nake hakan ba sai dan Suwaidatu ta yi qarama ba zata iya ba, sannan ko ba komai Hauwa'u na da wayon ta zata koyi wasu abubuwan, barin ta kuma da muke yi mu shiga daki ni da Yah Maheer banga dalilin da zai sa na shiga d'aki da ita ba a wannan shekarun da ta kai shekara goma ba,to menene laifi a cikin hakan har da za a yi gulma akai?

A haka cikin tunani da b'acin rai na kammala aiki na har girkin rana sannan na shirya dan tafiya makaranta ina fita na ci karo da Isma'il na wanki a tsakar gida, nan da nan baqin cikin abinda suka yi ya taso min na kalle shi na kalli igiyar da na yi shanya se na ga ba rabin kayan da na shanya, sauran kuma da ke kai an matse su waje d'aya,cikin b'acin ran da na jima ya na nuqurqusa ta na ce,

"Kai Isma'il uban wa ya ce ka kwashe min kaya a igiya ka cukurkud'a min wannan?"

Da tsananin mamaki ya miqe tsaye ya na kallo na, ci gaba da karkad'a qafa ta na yi na harare shi na bud'e qofa na wuce makaranta raina na ci gaba da b'aci, ina zuwa makaranta Mommy (principal) ta ce ba makaranta, nan da nan kuwa na hau haramar komawa gida, a lokacin nan akwai wata 'yar ajin mu Maman Zaid ta kalle ni ta ce yau dai baki yi fara'ar da ki ka saba yi ba a koda yaushe, yaqe kawai na mata na ce ina zuwa, da sauri na koma gida ina addu'ar Allah ya sa Isma'il be fita ba, ina shiga gidan kuwa na tadda shi ya na ci gaba da wankin shi amma rantsi da alama baqiqairin yake shima saboda abinda na masa kafin na fita, ina shiga har zan wuce na shige cikin gidan na dawo baya na kalle shi na ce,

"Ammmmm....Yauwaaa ka fad'a wa Maman ku in ta qara zuwa ku ka yi gulmata a parlour na abun ba zai mana kyau ni da ita ba,ta yi na farko na kyale ta yi na biyu na kyale amma duk randa ta yi gangancin yin na uku wallahi rai sai ya yi bala'in b'aci saboda shi babba kama girman sa yake, in ko yaqi yaro ba zai ji kunyar bi ta kai ya take ya murje da qafar shi ba" (na yi alamar takewa da murjewa da qafan)

MAHREEN Where stories live. Discover now