MAHREEN PAGE 18

43 14 0
                                    

💅 MAHREEN 💅


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



PAGE 18:



Gidan Kabeer suka je inda suka tarar da wata cousin ɗin su Abubakar ɗin ta je itama ziyara, nan fa aka haɗu aka dinga yi da ni, Habibah kuwa ta dafa shinkafa da miya da nama zuqu zuqu, ta d'ebo masu, su na ci suna min qafi kala kala,wai ni MAHREEN ce ban iya abinci ba banda kwab'a ba abinda na iya, Abidah ce ta kai lomar shinkafa bakin ta sai cewa ta yi,

"Yanzu ma fa da na je taliya ta dafa tsabar ba a san kan girki ba wai ta watsa su karas da kabeji da green beans a ciki, girki ba daɗi ba komai Salam"

Abubakar kuwa bud'ar bakin shi sai cewa ya yi,

"Ai se ma ta yi tuwo, haka za ka ji shi kataf ba bu dad'i,miya kamar ruwa ga baqar rowa, a wani ɗan qaramin kwano take zuba mana, kamar ita ke nemo hatsin"

"Ai gaskiya Yaya Babba na hakuri, ko dake an ce so hana ganin laifi, shi baya ganin laifin ta sam "

"Ni nake da wannan matar ai waje road zan ce mata,ba zan d'auki nonsense ba"

Hira ta yi hira, Habibah na ta jin su ta na nad'ewa ta na saka su a aji kala kala,dan kuwa ita da wayon ta kuma dama a shirye ta zo.

Qazafi kala kala haka suka yi min suka tashi ya maida ta gida, (har a wajen Allah na yafe Allah ya yafe mana dukkan kurakuran mu baki ɗaya ya jiqan wanda suka gabace mu)

Abubakar be dawo gidan ba se dare, ina nan na ajiye masa ragowar ɗan wake da taliya saboda ban sake yin wani girki ba shi ne dai.

Makaranta kar ku manta Yah Maheer a wannan lokacin qaramin ma'aikaci ne mai ɗaukan dubu ashirin a wata, ga shi ya na ciyar da mutane har biyar watarana sama da haka tunda a kullum se an yi baqi, abu ne me tsananin wahala mu kwana mu tashi ba a yi baqi ba,ya ilahi ina ake so ya samo kuɗin da zai yi wadaqa da facaka da kuɗi?

Ina nan ina ci gaba da kyautata wa kowa zato ba tare da na san ana gefe in an haɗu ana zagi na ba, Allah ya hore min fuska me yawan fara'a da hannu mai kyauta daidai qarfi na, duk abinda mutum ya ga ban bashi ba to fa tabbas bani da shi kuma Yah Maheer ba shi da shi, to dole na hakura tunda ba a kyauta da babu.

Ana haka matar Isma'il ta haihu, ta haifi 'yarta mace, kyakkyawa mai kama da iyayen ta, Habibah ce ta biyo min muka je har gida muka musu barka da sanya albarka, a lokacin Habibah na ɗauke da cikin Yaron su na fari, tin a wajen wasu ke min addu'a wadda se daga baya na fahimci har da baqar magana.

"To kema Allah ya baki rabon in kuna so dan yanzu wasu da kan su suke hana kan su haihuwar"

A lokacin nan wayo na da hankali na be bani wai baqar magana ake faɗa min ba duba da cewa wasu ma ni ban san su ba ya akai su suka sanni? Haka muka yini musu muka koma gidajen mu.

Ba a jima da haifar Amaturrahman ba Abidah ta haihu yaron ta namiji,nan ma ban bata lokaci ba wajen dibar jiki muka je gidan nata barka,anan ne nake jin za a yi suna, bayan mun tafi bamu sake komawa ba sai ranar suna,duk wani abu da za a yi haka aka dinga maida ni baya ina ji ina gani be dame ni ba a wancan lokacin dan ban ma fahimci wai ana sane ake min abu dan raina ya ɓaci ba, akwai yarinta sosai da kuma rashin ɗaukar abubuwa da mahimmanci idan ban gane inda suka dosa ba.

Bayan gama suna da sati biyu Yah Maheer ya zo min da albishir ɗin samun aikin shi a Kebbi state, shine dalilin da ya sa na ga ba ya zama sosai a watannin nan, dik da ban taɓa zuwa garin Kebbi ba amma ya bani labarin garin a takaice,se na samu kaina da yin murna sosai da farin cikin za mu koma can da zama, haka kawai na ji na gaji da garin Bauchi,Yah Maheer da ya ga murna ta ta yi yawa sai ya tsaya kawai ya na kallon yanda nake ta tsallen murna ina rawa, da na gaji kuma na haye gadon na faɗa jikin shi na kwanta ruf da ciki muna fuskantar juna,hannu na na sanya cikin gemun shi ina tajewa a hankali idanun mu na sarqafe da na juna na lankwashe murya irin yanda yake so na ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now