💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 11:
Gidan Gurama shine gidan da muka fara shiga kamar yanda aka umarce mu,gida ne na fulani dan kuwa ka na shiga za ka ga hakan saboda mutanen gidan suna da hasken fata da qaramin jiki irin na fulani, sai da mu ka dinga bi sashe-sashe muna gaishe da mutanen gidan har sashen kawun shi wanda yake qani ne ga mahaifiyar Yah Maheer ba tare da na san alaqar da ke tsakanin su ba a wannan lokacin, ya na da matan aure guda biyu da yara masu yawa, ina gama gaishe su muka fita muka tafi gidan Addah Ummu, murnar da na yi na ganin ta ba kad'an bane, domin kuwa ta haifi Ahmad dama ban samu zuwa suna ba,hakan se ya sanyaya min zuciya ta,a kan Ahmad na fara d'aukan jarirai saboda ina matuqar jin tsoron tab'a su motsin su a hannu na firgita ni yake, se gashi na d'auki yaron na riqe kamar ba zan ajiye shi ba, Addah Ummu ta ji dad'in gani na itama sosai, muka zauna muka sha hira na ci abinci a gidan ta na yi nak sannan muka mata sallama muka shiga gidan Sarki dan gaishe su, daga nan muka yi ta shiga da fita zuwa dangin Babana na jiki da kuma dangin Yah Maheer d'in.
A matuqar gajiye muka dawo gida ranar ana daf da kiran magariba, bayan na gaishe da mutan gidan tare da isar da saqon gaisuwar mutanen da muka je wajen su,se na cire takalmi na na dakko slifa na da na zo da shi dan sakawa a tsakar gida, hijabi na na cire na yafa a igiya sannan na d'auki buta na zaga bayan gida, ina fitowa na d'aura alwala na ja hijabi na na d'auki jakata da na yasar a tsakar gidan na shige d'aki, Ummeeta na can sashen su itama a gajiye.
Sallahr magriba na gabatar sannan na jingina da kujera ina fidda numfashin wahala, tinda uwata ta haife ni ban tab'a tafiyar qasa irin wannan ba, ko ina na jiki na ciwo yake min, gashi wanda zan zubawa shagwab'ar baya nan, ko ina ya tafi oho? Tinda na fita sau biyu ya kira ni, rashin samun wanda zan yi wa kukan na gaji da rashin samun Yah Maheer a gida se ya had'u ya haifar min da fushi mara dalili, Allah Allah nake ya dawo ya tadda kalar fushin da nake shi na bari na da ya yi na gaji.
Wani irin tuwo me rai da motsi aka ajiye a gabana ga dakakken yajin daddawa da ya sha maggi har da farin maggi mutumi na, ga man shanu an zuba masa, qamshin tuwon nan ne ya sa na ji duk wata masifa da fushi da na kinkima wa kaina na gaira babu dalili ya zagwanye, jan kwanon na yi na yi bismillah na hau danna tuwon nan a ciki na ba qaqqautawa,bayan gidan Addah Ummu duk inda muka je aka bani abinci bana ci kunya nake ji, in ko ruwa aka bani gidan be min ba se na tsoma baki na a ciki na yi kamar sha nake na dire kofi ko kwanon,in kuma gidan ya min sai na sha na qoshi, shine dalilin da ya sa na dawo da muguwar yunwa a tumbi na marata kuma fal fitsari .
Ina tsaka da cin tuwo aka kawo wutar lantarki wadda tinda na je ba a kawo ba, gashi dama muna cikin watan maulud ne an kusa mauludi,dan haka dama tinda muka je kad'e kad'en waqoqi na tashi sama sama saboda rashin wuta, ai kuwa ihun yara da matasa ne ya karad'e garin, ni kaina se na ji ni ina ta murna saboda wutar lantarkin da aka kawo, kafin kace me garin ya kacame da kad'e kad'e da waqe waqen yabon Annabi yanda ka san a cikin gidan aka kunna, nan da nan kuwa kaina da ke matashin ciwo ya dauki babban ciwo, a hankali na ci gaba da danna tuwon nan har na qoshi, tashi na yi na fita domin wanke hannu, Zainab na gani qanwa ga Yah Maheer 'ya a wajen Mama, kiran ta na yi na nuna mata robar wanka na ce dan Allah ta zuba min ruwa a ciki, na watsa, babu b'ata lokaci kuwa ta d'auka ta wuce bakin rijiya, kafin in gama shirin wanka in fito ta cika min robar ta kai min, godiya na masa ina tsokanar ta da cewar,
"Kin fanshi yayan ki, na gode"
Wanka na na yo ina mamakin yanda ake qure kid'a a ko ina ba tare da tinanin maybe akwai marasa lafiya, ko wanda suke karanta qur'ani a wannan lokacin ko sallah, ko bacci da dai sauran ire-iren wadannan uzirin da ba su son hayaniya,da so samu na ne da sun rage kid'an tinda nima ina sauraran kid'a amma qarar ta yi yawa, haka na gama wanka na na fito na yi alwala sannan na wanke baki na na koma d'aki,sallah na yi sannan na yi shirin bacci dan yanda nake ji na in ban bacci da wuri ba kai na zai iya tsage min gida biyu, tinda na saba baccin rana amma ban yi ba, na kuma saba da in yi zamana ina hutawa ta to ga yawo nan na sha na gaji.
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....