💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 10:
Watan mu uku mu na tsikarar amarcin mu da tsinke ba tare da wata matsala ko damuwa ta gifta mana ba,Yah Maheer ya yi nasarar wayar min da kai ta hanyar nuna min cewar Ustazai su ne gidan soyayya kulawa qauna da tarairaya,ya yi qoqari ya kafa kan shi a jaririyar zuciya ta ta yanda bayan qima daraja da kirkin shi da nake gani akwai wani lamari mai girma da ni kaina ba zan iya bayyana shi ba ko na yi bayani akan shi game da abinda nake ji akan Yah Maheer, a hankali na fara mantawa da komai da kowa da ke cikin zuciya ta, na maida hankali wajen biyayyar aure.
Ba tare da mun sani ba ashe ran Goggon shi wato qanwa ga mahaifin shi ya b'aci sosai akammu, ta na ta fad'a akan bamu je garin mu ba,labarin ya riske mu ta wajen qanin shi inda ya ce mana, Goggo fa ta ce,
"In ba ya raina mutane ba ace har yanzu wata uku kenan da yin bikin su amma be ga damar ya d'auki matar shi ya kawo ta garin nan ba ya nuna ta a dangi, wanda itama dangin ta ne ko ba komai ta san mutane tinda ba a nan ta tashi ba, to ai shikenan, in ya ga dama ya kawo ta, in be gadama ba ya riqe ta a can ya cinye"
Sanda muka ji labarin nan dariya kawai Yah Maheer ya yi, dan shi be cika announcing abu ba in zai aikata se dai kawai a ga ya yi, kwana uku da yin haka ya same ni ina zaune ina kallon wa'azin shaikh ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya masa rahama) wanda Baban mu ya ke bamu in an yi mana aure, (tare da wa'azin Shaikh Bn Uthman Kano na Tara Na Ma'aurata) suna na ya kira wanda ya sauya min tin ina watanni biyu da zuwa gidan, wato "Baby Na"
"Na'am Husband?"
"Ki shirya inshaa Allahu gobe juma'a za mu je gida LK (Liman katagum)"
"Allah ya kaimu, amma da ka sani ka sanar da ni da wuri,"
"Kar ki damu kawai ki shirya gobe za mu tafi"
"Allah ya kaimu"
Ba b'ata lokaci na shiga shiri, na had'a mana kayammu a akwati guda, hatta da wanda za mu saka na ajiye mana da takalmi da komai da za mu buqata, duk na had'a, dan ni ina da wani hali bana yin abu a makare, ina fara shirin yin abu kafin lokacin abun a koda yaushe, saboda bana son jira, ba kuma na so a jira ni.
Washegari kuwa kamar yanda ya yi alqawari muka samu adaidaita sahu ya kai mu tashar zuwa qauyen mu, baya ya kama mana gaba d'aya, dan haka mutum biyu kawai aka jira suka shiga gaba mota ta tashi sai LK.
Da yake ranar kasuwar mararraba ne mun sha wahalar cunkoson hanya kafin muka samu muka isa da yammar ranar, jiki na sanye da wata koriyar atampa wadda ta qara bayyana haske da kyawun da na qara, nan da nan gida ya d'auki murnar yara da manya ga Yah Maheer da Aunty Mahreen, murnar da har gobe idan na je yaran nan na yi saboda qauna ce Allah ya sanya a tsakanin mu ta musamman (Ummeeta da dikkan yaran gidan ku Allah ya yi maku albarka)
Sai da na fara gaishe da Mahifin Yah Maheer wanda ya kasa b'oye farin cikin gani na, ya tambayi lafiya ta, ya tambaye ni ko ina waya da mutanen gida suna lafiya ko? Na tabbatar masa da komai da kowa lafiya qlou, sannan na shiga d'akin Ummaa muka gaisa wadda ita na sani a matsayin mahaifiyar shi, wanda a wannan lokacin ban san takamaimai cikakken tarin asalinah mahaifiyar shi da ta haife shi ba,ina ka saka ina ka aje aka shiga yi da mu, abinci kala kala,saboda dama duk ranar juma'a sun fi yin girki na musamman saboda suna bawa ranar girma da daraja.
Sai na ji ciki na ma ya cushe na kasa cin abincin sosai,saboda ganin yawan shi, bayan na kammala cin abinci na yi sallahr la'asar na huta ne Umman su ta sake shigowa ta zauna fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi wanda ni a ranar na fara ganin ta, ita kuma ta jima da sani na,gaisuwa ta sake dasawa a tsakanin mu sabuwa, (abinda na kula mutanen garin mu na girmama gaisuwa) ni d'in ma sake duqar da kaina na yi na gaishe ta, Mama ma ta shigo, (matar Baban Yah Maheer) muka sake gaisawa,tin a wannan lokacin na fuskanci wani yanayi a fuskar Maman, wanda ba zan iya nuna yatsa na akai ba, dan kuwa muryar ta da fuskar ta a sake suke a gare ni amma haka kawai zuciya ta bata nutsu da gaisuwar da muka yi wa juna ba kamar akwai fake caring da take nuna min ban dai gama ganewa ba, tsarabar da na zo masu da shi da yaran su na miqe na bud'e akwati na na dakko na bawa Umma, murna ta yi ta kalli kishiyar ta ta ta ce,
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....