MAHREEN PAGE 19

44 12 0
                                    

💅   MAHREEN   💅




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







PAGE 19 :


Kamar daga sama na ji Yah Maheer na min tambayar da ta d'aure min kai,

"Baby na anya kuwa ba family planning ki ke yi ba shi yasa har yanzu ba ki samu ciki ba?"

Ji na yi kamar ya buga min guduma akai na, cikin tsananin mamaki da tunanin ina ma shi ya san wani abu wai shi family planning nake kallon shi, ni kaina dika dika nawa nake da zan san wani planning? A ina zan je a min shi? Sannan ta ina ma zan fara, gaba ɗaya sai na zama speechless.

Ganin irin halin da na shiga ne ya sanya jikin shi yin bala'in sanyi, nan take nadamar yi min wannan tambayar ta bayyana a fuskar shi, juyar da fuska ta ya yi dan na kalle shi da kyau, domin tinda ya mun tambayar na kalle shi ina so na tabbatar shin da ni yake ma wannan tambaya ko mistake ya yi ya kira suna na? Ina tabbatar da cewa da ni yake sai na kau da kai na gefe wasu hawaye masu zafi na dukan kunci na, wato shima rashin haihuwa ta ya fara damun shi har da zai zarge ni da yin planning kenan, ba laifi.

"Baby na Please say something, tambaya kawai na yi, saboda d'azu muna hira da abokai na ake maganar planning ya na sa wasu matan su jinkirta haihuwa, ni dama ba wani abu zan ce maki ba, alfarma zan roqa dan Allah in ki na yi ki dena ki bari ko haihuwa ɗaya ne a qalla mu yi se ki yi ɗin, dan Allah"

Yanayin yanda ya yi maganar se ya sanya ni jin matsanancin tausayin shi da ni kaina, ni dai na san bana planning, ban san a ina ake yi ba, ban san ya za ai na je na ce a min planning ba, ta ina zan fara ban sani ba,Allah shine shaida ta akan hakan,ta ɗayan bangaren kuma sai na ji tausayin shi wataqila zai ga duk abokan shi da qanne matan su na ta haihuwa shi kuma shiru har wannan lokacin,ban ce masa komai ba na miqe na wuce zuwa wanka, shima be tsayar da ni ba, dan ya kasa karantar halin ma da nake ciki balle ya san me zai min.

Ina wanka ina kuka, se da na yi na qoshi sannan na kammala na fito a lokacin qarfe ɗaya na dare ta gota, ko da na shiga dakin sai ya taso ze min magana, doguwar riga ta na ja na zura na sanya hijabi na,na tada sallah ban kula shi ba.

Ina sallah ina hawaye, bayan na idar ne na daga hannaye na ina addu'a, nan da nan jikin shi ya qara yin sanyi, sai ya durqusa ya riqe hannaye na ya sanya su a bakin shi ya na sumbata hawaye na zuba a idon shi, sosai.

(Masu cewa qarya ne namiji baya kuka saboda soyayya, ko dan ya ga matar shi na kuka, ko dan bata da lafiya da sauran su to su ne maqaryata, dan mijin ki baya kuka akan ki na cikin wani hali mara kyau does not mean cewa mijin wata ba zai yi mata kuka dan tana cikin wani mawuyacin hali ba, maza kala kala ne, kamar yanda kowa da halittar shi haka kowa da kalar zuciyar shi, da kuma yanda qarfin soyayyar shi take da qarfin zuciyar shi akan soyayyar nan tashi) kallo na ya yi a raunane sannan ya ce,

"Baby na dan Allah ki dena kuka, ki tsaya ki fahimce ni.....ni ban san ma me zan ce maki ba....amma dan Allah ki manta da maganar da na miki, Allah ya bamu zuri'a mai albarka a lokacin da ya fi alkhairi"

"Ameen"

Shine abinda na ce kawai na ci gaba da addu'a ta sannan na tashi na haye gado na juya masa baya, na matse can qarshen gado,wanka ya fita ya yi ya dawo, ya tarar da ni ina shan majina da alama kuka nake har a wannan lokacin,wanda ni kaina na rasa na menene, kawai na san dai zuciyata ta quntata da tunanin da ya yi na cewa zan iya yin planning ko haihuwar fari ban ba.

Sallah ya yi shima ya hau addu'a kafin ya idar ma na yi bacci,a qa'idar shi in Ina bacci baya tashi na, hasali ma dan kar a tashe ni ya na iya zama a parlour ko wane ke nema na zai ce bacci nake ba zai tashe ni ba, amma se gashi ya kasa hakuri se da ya tada ni cikin marairacewa ya ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now