MAHREEN PAGE 4

48 16 0
                                    

💅  *MAHREEN*  💅




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




PAGE 4

Mama ce ta dawo hannun ta d'auke da robar da na dafa fried rice for the first time a rayuwa ta, sai dambu Shima ranar na tab'a yin shi, ko ci ban yi ba, dama na ajiye ne da safe na dumama na ci har na tafi da saura makaranta, bashi ta yi ta ce,

"Maheer ga wannan ku tab'a ba Wani yawa ne da shi ba, in ta gama gugar ta dora maku ko taliya ne ku qara da shi,da ka sani tinda ku ka taso sai ka yi waya ka Sanar da zuwan ku a aje maku abinci na musamman, yanzu gashi ka zo da baqo gidan ku ba abinci"

"Ahh Mama kar ki Wani damu, ai a qoshe ma muke amma zan Kai mana wannan d'in mu ci ba sai ta yi Wani abincin ba, muna godiya sosai Mama da kulawa, Allah ya Saka da alkhairi,"

Wani haushi ne ya kama ni har cikin raina ban ji dad'in basu abincin nan da Mama ta yi ba,kallon shi na yi ta qasan Ido na na ga ya na kallo na ya na Murmushi, daure fuska na yi na tura baki na gaba,ai ba wai burge ni ya yi ba dan ya ce kar na yi girki, dama Mama ta Saba in dai ya zo gidan nan daga makaranta haka zata dinga zaqulo abu ta na bashi, gamu a cikin gidan bamu San da Wani abun bama, watarana Kuma miya za ta sa na zauna na soya masa ko cin-cin,gashi ban Isa na Yi miyar yanda na ga dama ba sai ta sani a gaba ta ce,

'Ki bar miya ta soyu ta yi yashi-yashi saboda haka ne zai sa baza ta lalace ba, bankawa miya wuta ba shi ne girki ba, ki sa wuta kad'an ki sa hakuri da nutsuwa a girki sai ya Bada ma'anar da ake so'

Ina tsaka da tinani na ji Mama na yi musu sai da safe, shi Kuma ya shige da kwanukan abincin d'akin samarin gidan mu da ba kowa ciki sai baqon shi da tinda su ka gaisa da mama ya koma d'akin, da damar yayu na sun tafi makaranta hakan ne ya sa d'akin ya zama ba kowa a ciki sai su.

"Ke har yanzu baki gama gugar ba?"

"Na gama Mama" na fad'a Ina tura baki, dan kuwa qiris ya rage na fara zubar da hawaye, ban yi shiru ba kuwa se da na mata magana akan abinci na da ta bawa d'an ta ba tare da an nemi izini na ba, Ina Saka Kai na a pillow zan kwanta cikin duhun da ya gauraye d'akin sakamakon kashe wutar lantarkin da muka yi na ce,

"Mama ban fa ci abincin nan ba ko d'and'anawa ban yi ba, Kuma baki ga wahalar da na sha ba gidan Aunty Salamatu kafin na iya dafawa, gashi kin basu abincin dika"

"MAHREEN abinda ka bayar shi ne naka, ki yi hakuri gobe zan baki indomie a cikin na makarantar su Sa'eed se ki dafa ki tafi da shi shikenan?"

Ba haka na so ba Sam, dan ni na so na ci shinkafar da na dafa wadda ake wa laqabi da fried rice tinda ban tab'a dafa irin ta ba da kaina sai ranar.

"Subhanallahi kin ga mun manta ko ruwan sha ba mu basu ba, dazu na ce ki kawo ruwa ki ka Kai a kofin silver nan gashi kafin ma mu tashi sun shanye shi, ki je ki d'ebi Wani ki Kai musu"

"Mama tsoro nake ji,"

"Mu je zan tsaya a soro ki Kai musu"

Haka kuwa aka yi, ko da na Kai musu ruwan sun cinye abincin tasss Suna zaune su na hira, Yah Maheer zaune yake daga shi sai gajeran wandon su irin na masu bautar qasa, Jin sallama ta ne ya sanya shi yafa farar rigar a kafad'ar shi, tin da na shiga idanun shi ke Kai na, kamar ba zai d'auke su ba,kwanukan na tattara na tambaye su ko akwai Wani abu da suke buqata? Da kan shi ya min alamar babu, kunyar yanda ya ke kallo na ta had'e baki na gumm waje guda, dan kuwa ban sake magana ba na fita na koma wajen Mama da ke tsaye a bakin qofar shiga gidan mu ta na Jira na, sai da ta sake yin addu'a sannan ta rufe gida muka shiga ciki.

Ko da na kwanta na kasa cire tinanin kallon da Yah Maheer ya ke bi na da shi, kallo ne da ban tab'a ganin ya yi min irin shi ba sai watarana da ya shigo cikin gidan d'iban ruwa a bokiti na yi sauri na je na karb'a zan ja mashi daga rijiya, amma ya qi sakin bokitin ya kafe ni da kallo ya na fad'in in barshi ya gode.

MAHREEN Where stories live. Discover now