💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 6:
"Matsalar da ke tattare da ke mana ! Wannan ai babbar matsala ce a ce mace ta na tsallaken jinin al'ada, ya kamata a shawo kan matsalar tin kafin ta girma"
Kallon na fahimci maganar ki na mata, damuwa ta kuma sai ta qara yin gaba, saboda ina tunanin wad'anne kalolin matsala ne nake tattare da su? Ina ma zan samu me yi min bayani ya fayyace min komai, lallai da na samu nutsuwa, amma babu komai, a yau ba sai gobe ba zan tinkari Mama da maganar.
Bayan na koma gida da dare kamar yanda muka saba kwanciya, cikin duhun da d'akin ya yi sakamakon kashe k'wan wutar lantarkin da mu kai,na d'aga kai ina kallon Mama da ke ta jan carbin ta, domin ta saba da hakan dik daren duniya sai ta yi tasbihi ba adadi sannan ta dora da ayatul kursiyyu cikin carbi ko kuma bacci ya dauke ta ta na tsaka da yi, gani na yi hankalin ta na can kan abinda take yi,ina jin nauyi da shakkar tambayar ta game da wannan matsalar tawa, duba da cewa a wannan lokacin ba cikakkiyar shaquwa a tsakanin mu da ni da ita, ba ma fayyace wa juna yanda muke ji game da junan mu na soyayyar dake tsakanin uwa da 'ya kamar yanda ya kamata,iyaka na san ta na iya qoqarin ta na ganin ta yi mana duk wani abu da ya zama dole ta min shi a matsayin ta na uwa, tinanin ranar da na fara yin period ne ya d'arsu a raina.....
Bana mantawa ina makarantar boko aji hud'u na dawo gida zan yi fitsari se na ga jini, na hau kuka a sirrance ina cewa na ji ciwo a wajen, Addah Ummu ita na samu da maganar ina ganin jini, nan take ta hau dariya ta na cewa na girma, Addah Ummu ita ta koya min yanda zan kula da jiki na, da yanda ake wankan tsarki, sannan ta sanar da Mama, da dare muna kwance kamar yanda muke a yanzu Mama ta kalle ni ta ce,
'To Mahreen na ji labari wajen Ummu cewa kin fara jinin al'ada, ina so ki sani a yanzu kin tashi daga yarinya kin koma babba, alqalami ya hau kan ki, aikin ladan ki daidai yake da irin aikin ladan da zan yi, aikin zunubin ki daidai yake da aikin zunubin da zan aikata,yanda Allah zai bani lada in na bauta masa da gaskiya, kema haka Allah zai baki lada in kin bauta masa da gaskiya, yanda Allah zai bani zunubi ya sani a wuta in na aikata zunubi kema haka Allah zai maki, yanzu an bud'e maki littafi a wajen Allah, idan ki ka furta kalma d'aya sai an rubuta ta, idan ki ka fad'i me kyau a baki lada, idan ki ka yi mara kyau a baki zunubi, sannan ki sani kamar yanda zan d'auki ciki in haihu, haka kema duk sanda ki ka tsaya mu'amala da namiji wanda ba mijin ki ba kema zaki dauki ciki ki haihu, ki tsare mutuncin ki, ki kare martabar ki, kar ki zama ki na wasa da maza ko ki na bari maza na wasa da ke, namiji in ba muharramin kin ki bane(Mahaifi, yaya da ake uwa d'aya uba d'aya, ko wanda aka had'a uba kawai, ko wanda aka had'a uwa kawai,ko qanin uwa ko qanin uba, ko kakannin wajen uwa da uba, wanda a yanzu zamanin nan da muke ciki su kan su ba abin yarda bane)ko hannu kar ki bari ya tab'a maki, saboda had'uwar hannun ku waje d'aya kamar aikata zina ne kuma aikata zina babban haramun ne,Mahreen ki ji tsoron Allah a dik inda ki ke a kuma duk halin da ki ka samu kan ki, sai Allah ya so ki, kuma ya kiyaye ki daga dikkan sharri, kina ji na ko? Na ji ta ce ta koya maki yanda ake kulawa da jiki, da kuma wankan tsarki, akwai wasu abubuwan da zan koya maki a hankali inshaa Allahu, Allah ya muku albarka baki d'aya'
'Ameen' shine abinda na amsa da shi a wancan lokacin, to yanzu gashi an ce akwai matsala idan bana yi akai akai anya in sanar da Mama kuwa ko dai na yi shiru, ko na bari sai na je gidan Inna ta se na fad'a mata tinda ni na fi shaquwa da ita sama da kowa, ba abinda nake b'oye mata duk wani sirri na da ya kamata Mama ta sani da Innata nake yin shi sai dai in bama tare, shahada na yi na tashi zaune sosai na ce,
"Mama? Ko kin yi bacci?"
"Na'am ido na biyu, ya aka yi?"
"Uhmmm damaaa...damaaa ina so immmm na maki wata magana ne,"
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....