💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 35:
"Na ga kana fara'a sosai halan ta samu ne? Yeeeehhhh ta samu Alqur'ani da ganin ɗan bakin nan naka kamar tsohuwa za ta ce yuthuufff akwai magana ciki nai"
Dariya ya yi tare da kada kai, a duniya ya na so ya ga ina barkwanci to fa zai ta dariya se da ya gama dariyar ni kuma na gaji da juye juyen rawar sannan na zauna ya kalle ni ya ce,
"Kai jama'a Allah ya maki sauqi, wato ni dai na zama bani da sirri har abinda ke zuciya ta ma se kin zaqulo shi, to zauna ki ji me ke sa ni murna"
Dariya nima na yi na zauna a gefen shi na mimmiqe qafafu na da nake jin su kamar ba a jiki na ba tin daga qugu na har yatsu na, juya wa kadan na yi mu na fuskantar juna Yah Maheer ya ce,
"Alhamdulillahi... Alhamdulillahi..... Alhamdulillahi....wannan shi ne abinda zan fara faɗa kafin na miki albishir, sannan zan gode miki kema saboda hakuri da ki ke yi da ni ki ke jure babu na da kuma samu na, tohh kin san dai gidan nan ba namu bane kuma ko bajima ko ba dad'e za mu bar gidan nan ko? (Kada kai na yi ina sauraron shi) to Allah ya nufa na sama mana gida a can Alieru quarters amma one bedroom, na so na sake samo mana a two bedrooms ban samu ba three bedrooms Kuma kin san kuɗin ya yi yawa, dan haka daga nan zuwa Monday za mu koma can da zama, kin ga mutanen nan sun mana qoqari, kar tun ana ganin mutuncin mu mu saki jiki mu yi ta zama a zo abu na sabani ya shiga tsakani, sun yi mana abinda ba zamu taɓa manta wa da shi ba har abada, dan haka tun yanzu mu yi qoqari a rabu lafiya ko? Shi yasa ki ka ga ina farin ciki"
Har cikin zuciya ta na samu kai na da farin ciki nima, ban damu da one bedroom da ya ce zamu koma ba, dan na san gidajen area ɗin ba masu munin da mutum zai qi su bane,ba laifi iyaka daki ɗaya ne se parlour kitchen da babbar tsakar gida,akwai ruwan pampo suma kuma akwai wuta, dan haka ba wani abu da nake da buqata da ya wuce hakan, cike da murna na rungume shi ina hamdala, sannan na ce,
"Gaskiya ba abinda za mu ce wa Allah sai godiya, su kuma su Bashar Allah Ubangiji ya biya su da babban gida a aljannah ya saka musu da dukkan alkhairan shi, Allah ya raya musu zuri'ar su da imani, dole ne duk sanda suka shigo gari mu zo mu yi godiya ta musamman har gida"
"Kwarai, ni fa in Ina masu addu'a har rasa me zan roqa masu nake saboda iya rufin asiri sun mana shi a sanda bani da gidan da zan saka iyali na, bani da kuɗin da zan nemi gidan da zan saka iyali na, bani da komai zuciya ta na quna ta na cike da rad'ad'in rashi da mu ka yi na muhalli, bawan Allahn nan ya share min hawaye, dan haka ba zan taba dena yi masu addu'ar alkhairi ba inshaa Allah"
"Gaskiya dai kam Bashar mutum ne har ma da qari Allah ya baka ikon kyautata masa kaima "
"Ameeen"
Hira mu ka ci gaba yi, daga baya mu ka koma d'aki dama kayan mu ba a watse suke ba, kowa kayan shi na cikin jakar shi, inda ni da Yah Maheer namu ke a haɗe waje ɗaya Suwaidatu nata ke cikin jaka, dama ba wani kaya ne da mu ba sosai a gidan, a can gidan Maman Ameenah ne mu ke da sauran 'yan tarkacen mu har da fridge da TV na se DVD, dan haka sai mu ka sanya rana dan na je na kwashi kayan nawa mu kai can inda za mu koma.
Washegari na tashi da wani irin tari busasshe in na fara sai na ji kamar numfashi na zai ɗauke, a haka na shirya muka tafi gidan Mama ni da Suwaidatu, mu na zuwa Ameenah ta tarbe mu hannu bibbiyu Mama ma ta ji daɗin ganin mu haka zalika Baba, gaishe su mu ka yi aka zauna hira,anan nake sanar da su zamu dawo nan, amma can bangaren one bedroom, murna suka yi da jin haka a qalla mun dawo kusa, dan ni a garin Kebbi nan ne nake dauka a matsayin gidan mu,muna hira nake sanar da su zan kwashi kaya na ne mu kai can gidan, Mama ta ce ,
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....