MAHREEN PAGE 22

53 14 5
                                    

💅   MAHREEN   💅







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







PAGE 22:





A can mu ka qarasa yinin ranar har na samu yin baccin rana, bayan na tashi ne na ci shinkafa da wake da ta ji man quli shanana da yaji me dad'i,naa ɗauki yayar shi kamar uwa saboda babbar mata ce sosai ɗan ta na fari ma ya na mata har biyu, ta na da jikoki, dan haka ba qaramar mata bace babbar mata ce, akwai 'yar kunya a tsakanin mu, duk so na da qauna ta da wake da shinkafa ban zage na ci gaba ɗaya ba, bayan mun yi sallar la'asar ne muka yi mata sallama mu ka tafi.

A hanyar mu ta koma wa ne muka shiga gidan qanwar Babana Goggo Talatu da gidan cousin ɗin Yah Maheer wato Umman Bello,tinda a hanya suke mu ka gaishe su daga nan muka faɗa gidan Addah Ummuna,anan na baje komai nawa mu ka ci mu ka sha muka yi hira sosai, bamu bar gidan ba sai bayan magariba,sannan muka tafi gida.

Ko da mu ka koma gida Ummeeta ta yi sashen su nima na wuce namu, zaune na tadda Baba ya na ta jan carbi su Ummah kuwa sun tasa tuwo a gaba za su ci, gaishe su na yi sannan na samu waje na zauna ina jiran Baba ya idar na gaishe shi,se na kula Isha'i yake jira dan haka ba zai magana ba se ya kammala abinda yake se na miqe zan shiga d'aki, ban kula da sababbin takalman da ke a bakin qofa ba sai da na shiga ciki na tadda matar Abubakar wato amarya Mommy, cikin washe baki na ce,

"Ahhh mutanen Bauchi yaushe ku ka zo?"

"Tin dazu muka zo ku na can ku na yawo"

Kalmar yawo ta sa na shiga tunanin wannan ta san yawan dangin mu kuwa? Anya wannan ta iya magana kuwa? To ko zancen akai ta yi a gidan cewa na tafi yawo? Zan gani a fuskar Baba bari ya gama lazimi na gaishe shi, dan shi baya boye min komai,duk da be taɓa min faɗa ba amma in be ji dad'in abu ba ina ganewa.

Tinda na kula Mommy kamar bata iya magana ba a hirar da muka ɗan fara da ita, se na fara iya baki na saboda ina da wani hali, na tsani a cab'a min magana, kuma bana son mutum ya dinga magana da raini a ciki yanzu raina zai ɓaci, amma in na kiyaye jan doguwar hira da mutum sai a zauna lafiya ban hasala ba ballantana na faɗa wa mutum ba dad'i nima.

Abinci na na gani a gefe, shafa ciki na na yi da yake a cike maqil da shinkafa da Miya da lettuce da tumaturi da albasa, Se soyayyan kifi wanda na ci a gidan Addah Ummuna, duk so na da tuwo haka na kalla na kyale dan ba zan iya ci ba, ina nan zaune aka kira Isha'i nan da nan kuwa Baba ya tashi ya fara sallah, (Ba ya zuwa Masallaci saboda bashi da lafiya)Nima fita na yi na yi alwala na dawo d'akin Mommy na kwance ta na danna 'yar qaramar wayar ta, sallah na tada nima na yi qasaru, ina idarwa na samu waje na zauna ina tasbihi ga Allah, a sannan ne ta tashi ta je ta yi alwala ta dawo ta yi sallah itama,ina nan zaune na ji muryar Baba ya na faɗin.

"Kun dawo?"

Da sauri na je bakin qofar dakin na durqusa na gaishe shi ya amsa min cikin sakewa da fara'a, ji na yi raina fesss ba abinda ya dame ni tinda kowa ya sauya min a gidan shi kaɗai ne be sauya min ba dan haka nima ba zan damu da fushin kowa ba sai nashi.

Mu na nan zaune Yah Maheer ya dawo, direct dakin Baba ya shige Abubakar kuma ya shigo inda muke, nan fa suka fara wani wasanni da Mommy a raina dariya kamar zan yi yaya, saboda abun se ya min wani banbarakwaiii,yi na yi kamar ban gan su ba na buɗe jaka ta na dakko littafi na da biro na hau rubuce rubuce na da na saba,sun kula da cewa gaba ɗaya hankali na baya kan su, domin da gaske ina fara rubutu hankali na ya bar kan kowa a gidan,saboda ni in na sa rubutu na a gaba to fa shi ne a gaban nawa, gajiya suka yi da wasannin nasu ya samu waje a kujera ya zauna suka ci gaba da hira, ba jimawa Yah Maheer ya min waya, na duba jaka ta na zaro wayar, ina ganin sunan shi a jiki na yi murmushi, a raina na ce,

'Dan Baba se yanzu za a kira ni kenan'

Da sallama na ɗauki wayar shima ya amsa min ta can bangaren,a hankali ya ce,

MAHREEN Where stories live. Discover now