💅 MAHREEN 💅
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 15:
"Mahreen kin san yanzu haka daga gidan Maman Humairah nake? Mu na hira take bani labari shine na ce bari na zo na fad'a maki, duk da dai na bata amsa"
"Me ya faru Yaayah Maimunah?"
Cikin qaguwa da son jin labarin na ke tambayar ta, Maimunah ta gyara zama ta kalle ni sannan ta ce,
"Maman Humairah ke tambaya ta wai jiya da daddare da misalin sha d'aya na dare da 'yan mintuna Baban Humairah ya fito zai rufe musu gida ya na tsaye ya na addu'a a jikin qofa se ya hango wata mata da lullub'i durqushe a jikin windown kitchen d'in ki,se ya fara tunanin ko d'aya daga cikin mu ce ta yi fad'a da mijin ta shine ta fito waje? Tinani ya yi ko zai kira Maman Humairah ne ta je ta tambayi matar in ta ji mune kuma matsala aka samu se su shiga a daidaita, ba a bar mace a wannan daren ita kad'ai a waje ba, qifta idon nan da zai yi ya sake bud'e su akan matar se ya ga wayam ba kowa, abun ya yi mugun bashi mamaki, har bud'e qofar ya yi ya ga ko zai hango ta tana shan kwana amma be ga kowa ba, shine na ce mata gaskiya ba mu bane, dan ke mijin ki ma baya nan, ni kuma lafiya qalou muka kwana da Yaya,wataqila wata ce ta tsaya amma ba mu bane,"
Wani irin abu na ji ya dira akai na me nauyi na tashin hankali,
'To ko dai matar da ya gani bayan ta ga an gan ta shine ta shigo min d'aki na? To wacece? Aljana ce ko mayya ko me?'
Nan da nan tsoro ya kama ni, tinanin mafita ya baibaye ni, ya zan yi na kub'uta daga maimaituwar abinda ya faru daren jiya?
"Amarya ki na ji na kuwa?"
Cikin in ina da saurin baki na amsa ta da,
"Uhmm...ehhh...ina jin ki...gaskiya dai ba...baaa mu bane...wataqila wata ce zata wuce se ya gan ta"
"Nima dai haka na ce mata,"
Hira muka ci gaba da yi, wadda fiye da rabin ta hankali na baya kai sam sam.
A haka na qarasa satin nan ba wani sukuni, babu bacci, babu nishad'i,kuma na kasa sanar da kowa, na kasa sanar da Yah Maheer saboda kar hankalin shi ya tashi gashi ba a kusa yake ba ya na nesa, na zama kamar wata bugaggiya saboda rashin bacci, qasa da saman ido na ya yi dark circle saboda rashin bacci, gani kullum cikin kasala nake.
Ranar juma'a da ta kama ranar dawowar Yah Maheer ban b'ata lokaci ba wajen shiga kitchen na tsara masa abinci daidai qarfin mu, sannan na sha wanka na fesa kwalliya, masha Allah nan da nan se ga Mahreen mara nutsuwa a 'yan kwanakin baya ta d'auki saiti, Maimunah kuwa tsokana ta ta hau yi wai yau Oga ze dawo kenan shine aka sha kwalliya haka.
Murmushi kawai na saki a sanda na ji hakan, da misalin qarfe sha d'aya na rana sai ga sallamar Yah Maheer ta karad'e kunnuwammu, cikin tsananin murna da d'okin ganin shi na fita daga parlour na tsaya a bakin qofa ina jifan shi da kallon na yi kewar ka, leben baki na ne ya fara rawa sannan ya kyab'e irin na shagwab'abbun nan masu son yin kuka,lokaci d'aya nan da nan ido na ya cika da hawaye ya fara sintiri a kumatuka na masu yalwa, kai kawai ya ke kad'a min alamar ah ah kar na yi kuka, da sauri na qarasa na rufe tazarar da ke tsakani na da shi, ya kuwa sake jakar shi a qasa ya rungume ni, mun kai mintina biyu zuwa uku a haka kafin na duqa na d'auki jakar tashi mu shiga d'aki,sabuwar maraba Yah Maheer ya karb'a daga waje na, sannan muka zauna a bakin gado, hannu na sanya na cire masa hular shi sannan na b'alle masa mab'allin rigar shi, wuyan shi ya samu sassauci daga matsewar da ya yi.
Da kyar Yah Maheer ya barni na tashi na kawo masa ruwa da abinci, babu b'ata lokaci kuwa ya hau ci ya na santi, ya na tsaka da cin abincin su Suwaidatu suka dawo daga makaranta da misalin sha biyu da rabi, gaishe shi suka yi suka shiga suka d'auki kayan su da za su sauya,nan ya dinga tambayar su ya makaranta da bayan rabuwa su kuma suna bashi amsa.
![](https://img.wattpad.com/cover/340061313-288-k899525.jpg)
YOU ARE READING
MAHREEN
RomanceA Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishadantar Kuma ya ilmantar da ku....ku biyo ni ku ji yanda MAHREEN ke Shan gwagwarmayar rayuwa....