Hey lovliess😍😍...na ce bari mu ɗan shaqata da hotunan Main Role leaders na labarinmu😅...ku gani ku tofa albarkacin bakin ku before we dive in to the story💃💃💃
1) Nazifi Bala Mai Kalwa
Sarauyi mai cikar kamala da nagarta, ga haƙuri da karrama mutum, fara'a kamar gonar auduga, babu ruwansa da faɗa, ya sha ilimin addini yay maƙil, yay wa ibada riƙon gamgam, magajin mhaifinsa a iya mu'amala da sanin ya kamata...kyakykyawa ne sosai ba zaka ce ɗan ƙasar hausa ba ne.2) Sadeeq Abubakar Jadda(SJ)
Saurayi mara son hayaniya, miskili, ga zafin kai, babu fara'a, ba ya son mutane sam, zai iya tashi ya kwana bai kula kowa ba hatta da iyayensa, ra'ayinsa kawai yake bi ba ya bin ra'ayin kowa, ba ya so a tambaye shi haka ba ya so yay tambaya, ba ya bayani bai kuma so a tsaya yi masa, yafi son zartarwa kawai, abin da sam bai yarda da shi ba a rayuwarsa ita ce SOYAYYA, kuma abin da yafi bawa amanna aikinsa da baccinsa, sai dai kuma in har ya ƙwallafa rai akan abu to sai ya sameshi hankalin kowa zai kwanta, kuma da mutum ɗaya ne ba ya shiri wato MAHIFINSA, in yana wuri mhaifinsa ba ya zama, haka shima in mahifinsa na wuri ba ya zama.3) Sa'id Salman Madobi(Yashaik)
Yashaik kenan, zazzafan namiji kamar wuta, kaifi ɗaya a magana, mai siyan faɗan da bana shi ba musamman a in da yaga babu adalci, tsayayyan namiji mara kara da alkunya balle kawaici.
YOU ARE READING
ƘAYAR RUWA Book 1 Complete
FanfictionThe story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'anar da ke girgiza duniyar wasu ma'auratan, ta kuma haifar da motsi mai ciwo gami da harbawa a zuƙatan...