24

180 10 0
                                    

ƘAYAR RUWA 24.
*MAFARI...*
Ta dabo ci gari, garin da ba kano ba dajin Allah, jalla babbar hausa, yaro ko da me kazo anfika, tabbas a duk inda kaji anyi irin wannan kirarin a kaf faɗin duniya, kasan ba da kowanne gari ake ba face garin kano da ake yiwa laƙabi da tumbin giwa, garin da ya amsa wan nan sunan, musamman idan aka yi duba da yawan al'ummar da ke cikin garin, ƴan asali da kuma zuwo daga ƙabilu daban daban, garin da ya tara manyan Malamai, ƴan kasuwa, Attajirai, ƴan siyasa, Dattawan arziƙi, Sarakai, Makarantun boko da na addini, garin da yay shura wajen haɓɓakar kasuwanci da kamfanunuwa.

A tarin unguwannin da ke cikin garin kano, unguwar yakasai na daga cikin manyan anguwanni wadda ake kira da Yakasai rabin birnin kano, idan muka tattara zuwa makarantun da suke cikin garin kano da bamu san iyaka adadin su ba, Shekara secondry school na ɗaya daga cikin makarantun sakandire ta gwamnati da ke a cikin anguwar ta yakasai, me ɗauke da ɗalibai maza da mata. Ɗaya ga watan octoba ita ce ranar da duniya ta shaida a matsayin ranar murnar samun ƴanci na ƙasa najeriya, a bisa girman ranar ga ƴan ƙasa yasa hutu ke ta'allaƙa ga dalibai, ma'aikatan gwamnati, kamfanunuwa masu zaman kansu, har ma da wasu daga cikin ƴan kasuwa.

A yau da ya kasance talatin ga watan Satumba, daga cikin harabar makarantar sakandire ta shekara, ɗalibai ne ke ta dabdalar shigewa cikin ajujuwa bayan kammala taron asambili da akayi, mafi yawanci fuskokin su ɗauke da farin ciki saboda murnar hutun da aka basu na tsawon kwanaki biyu sakamakon murnar zagayowar ranar ƴanci na ƙasa. tun bayan komawa aji kowanne ɗalibi ka kalla zaka ga zaƙuwa a fuskarsa na son a buga ƙararrawar tashi domin tafiya gida. Ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai aka buga ƙararrawar tashi, kuma a wannan lokacin ajinmu SS2 mune muka fara fitowa.
Sunana Sa'ida Salman Madobi, shekaruna goma sha biyar a duniya, ina ɗaya daga cikin sabbin ɗaliban da aka kawo watan da ya wuce da na baro makarantar Aisami na dawo nan ta shekara. Ni ɗin ba doguwa ba ce haka kuma ba gajeriya ba ce ina da matsaikacin tsayi me kyau gami da dirarran jiki na jan hankali, ina da cikar halitta ta ko'ina, doguwar fuskata na ɗauke da dogon hanci da madaidaicin baki da kuma irin idanun da ake kira da sexy eyes, ba zan ce ni kyakykyawa ba ce can amma dai ba na cikin sahun munana ina da kyawuna daidai misali, hasken fatata ba irin hasken nan ba ne sosai kuma ba baƙa ba ce ni, sai dai na ɗauko ɗabi'ar mahaifiyata na bala'in haƙuri da sanyi. ban da yawan magana ina son shiru a rayuwata ni kam, dan ina iya zaman minti talatin a wuri ban magana ba duk kuwa irin surutun da ake yi, wannan dalilin ne yasa wasu ke cewa ina da girman kai wasu kuma su ce saboda ƴar gidan masu kuɗi ce, basu san ni ɗin ƴar masu rufin asiri ba ce, kuma ba komai yasa ake min kallon ɗiyar masu ƙumba ba sai dan zubina da irin shigata ta uniform da jakar makaranta da yanda na ke fesfes, da Yayana da ya ke kawo ni a motar uban gidansa idan ya kai yaransa makaranta, wannan yasa da yawa ke tunanin Abbaana wani Alhajin Neran ne.

Sunan Mahaifina Malam Salman, Asalinmu ƴan ƙauyen Madobi ne daga baya kuma karayar arziƙi da mahaifin su Abbaanmu ya samu yasa muka dawo nan cikin kano da zama, tun lokacin ina cikin zani. Abbaana yana kasuwancinsa anan kasuwar kurmi shi da ƙaninsa Baba Sabi'u in da su ke siyar da citta da kayan ƙamshi na abinci, yanzu haka kuma sun koma ƴan tebura anan bakin asibitin Murtala suna siyar da atamfofin leda turmi da falle falle. Mutane da yawa sun shaidi Mahaifina akan kirkinsa da dattakonsa, duk wanda ya san Malam Salman Madobi zai buɗi baki ya ce maka mutum ne na gari wanda ya san darajar ɗan Adam da kyautatawa, ba a taɓa jin kansa da kowa rayuwarsa kawai yake yi shi da iyalansa da ƴanuwansa, ga shi da ƙoƙarin taimako.
Mahaifiyata ita ɗaya ce matarsa Sa'adatu muna kiranta da  Ummani, ita kanta jama'a na shaidarta da halin kirki da sanin yakamatarta, kowa kuma zai ce maka Ummani bata da wani farin ciki sama da taga ta taimaki wani da ke cikin tsananin buƙata duk da itama ɗin ba shi ne da ita ba, akwai ta da halin kawaici da kauda kai gami da masifaffan haƙuri da ka iya hallakar da ita, amma banda idan aka taɓa ƴaƴanta, duk haƙurinta da shirunta ajiye shi take a wannan fannin ko da za su samu saɓani da mahaifina, akwai soyayya me ƙarfi tsakanin iyayena da kuma fahimtar juna, kyautatawa da rufawa juna asiri.

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now