*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(18)*
Barinsa wajen na nufi bene nima, gaba ɗaya na manta da batun wani wanki, sai munafukar yarinyar ce take cewa da Iyam wai na tafi na bar mata kaya. ita kuma ta ce ta ƙyaleta da ni zamu zuba. ni kam ban tsaya ba nayi ɗaki ina jin babu daɗi a raina, zama nayi saboda raina ya ɗan yi sanyi amma har ga Allah na jima ban ji ɓacin rai ba irin na yau.
to ni wankinma bai cin min rai ba kamar zuba abincin in kai mata kuma ta karɓa tana min dariya, in wanki ne dama tunda Iyam ta dawo ta hana badawa da guga tace masa gatan yayi min yawa komai sai a kashe kuɗi ayi min banda aiki sai kwanciya, don haka bisa umarninta kar a ƙara bayar da wanki a gidan, kayan wankin guda nawa su ke da ni ba zan wanke ba sai dai ai ta ɓarnar da kuɗi ni babu tausayi saboda ban san wahalar da yake sha ba kafin ya samesu, to in dinga ƙwarara jiki ina motsawa, haka ma fa firij tasa an ɗauke na kitchen an kai ɗakinta, duk su lemo da nama in ya kawo sai yanda ta bani, duk sona da maltina yanzu sai haƙura na ke yi saboda idan naje karɓa ta dinga mita kenan.Da rana ina cikin wankin sai ga shi ya shigo yana faɗin,"wanne irin rashin hankali ne wannan? Kin bar tukunya zata ƙone kin taho wani aikin na daban, ki bari ki fara kammalawa da ɗaya mana, wannan ai ba dabara ba ce. kin san yanda gas ke kara tsada kuwa, wallahi za ki ja na koma ajiye miki buhun gawayi".
Da alama bai san wankin na waye ba shiyasa, Na tsame hannuna a ruwan da sauri, ta gefensa na wuce na nufi kitchen ɗin, ina zuwa na tadda ruwan zafin ko tafasa bai yi ba, ni dai dama nayi mamaki domin kuwa nayi ƙasa da wutar sosai, kai bawa dai da komai kayi sai ya zama laifi, nufinsa da yay maganar in tsaya masa bayani ya hasala ya gaggaya min babu daɗi. ina kitchen ɗin ya dawo ya sameni, ya ce in fito falo na iske shi, sauri sauri na wanke shinkafar na zuba na fita, yana tsaye hannayensa harɗe ta baya, hannun kujera na zauna ina ce masa,"gani".
kuɗi ya miƙo min tare da cewa,"akwai abunda ya taso min na ke so a taya ni da adu'a, ga wannan dubu talatin ne, idan kin gama aikin sai ki leƙa gidan Malama Hadiza, akwai buhun shinkafa da wake na bayar akai gidan, idan kin je sai ki tambayeta adadin kuɗin da ake buƙata, jallof ne za'ai da ƙosai da kunu ayi sadaƙa".
ina kallonsa na kai hannu na karɓa na ce,"Allah ya karɓa ya biya buƙata".
Ko amsa ni bai yi ba, ya nemi kujera ya zauna ni dai na bi sa da kallo don naga kamar yana cikin damuwa. sannu a hankali na ce da shi,"ko wani abu ne ke faruwa?". ba tare da ya kalle ni ba ya ce,"plazar cikin gari gwamnati ke son rushewa wai filinta ne".
na ce,"to subhanallahi, Allah ya saita al'amura, kar ka damu insha Allahu zata dubeku ta bar muku abinku, adu'a ce kawai zata yi aiki".
ya amsa da,"ilahee ajib".
na buɗi baki da niyyar in wata maganar wayarsa tayi ƙara, ido ya ɗago yana kallona bayan ya gama kallon screen ɗin wayar, a hankali yace,"ki bani wuri".tashi nayi na bar masa wajen na koma bakin ayyukana, sai dai tuni na shiga damuwa da lamarin plazar da ya faɗa min, tabbas aka rusheta ba ƙaramin asara zai yi ba, don duk ita ce jagaban kasuwancinsa. nayi nisa a wankin sai ga Fati da kaya a hannu, tana zuwa tsabar rashin mutunci ta watso min su cikin ruwan wankin, raina ya ƙuntata na waiga a fusace sai zuciyata ta taushe ni kawai na ƙyaleta, don yanzu ina magana tashin hankali zai biyo baya.
"ki wanke min fuskar da hannayen da kyau".
ta ce da ni cikin gadara da nuna rashin kunya, ban ce mata komai ba har ta fita. kafin na gama wankin har na gama girki dama saboda haka nayi dabarar haɗa aikin biyu, kar in kai dare ban gama girki ba Iyam ta ɗaga min hankali da cewar na bar yara da yunwa, tayi nata mai gidanma yay nasa.
Nayi sa'a kayan su ka bushe da wuri. na ɗebo shanyar na linke na ajiye su akan kujerar falo, ina jiran nayi wanka na ɗan huta sai na zo na goge, kafin na bar wajen sai ga Iyam ta fito ta zo tana cewa,"gugar kuma fa bayan ga wuta nan kika wani linkafesu kika yasar da su anan koma ki kai min ɗaki. Ko ajiye min kika yi na zo na goge da kaina?".
YOU ARE READING
ƘAYAR RUWA Book 1 Complete
FanfictionThe story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'anar da ke girgiza duniyar wasu ma'auratan, ta kuma haifar da motsi mai ciwo gami da harbawa a zuƙatan...