*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
'''for your business advert chartup 09030398006.'''
______________________________
*(10)*
Cikin farin ciki na ci gaba da shirina, har da kayan da zan bayar a ƙauye duka na haɗa, ban san lokacin da zaman zai ɗauke ni ba tun da bai ce ga iyaka adadin kwanakin da ya bani ba, dalilin da yasa na tabbatar da na ɗauki duk abin da zan buƙata kenan. har wani ɓari na zuciyata ma na faɗa min wataƙila tafiyar da zanyi tafiya ce ba ta dawo ba, imma mutuwa ta ɗauke ni imma kuma sanadin zaman auren kenan. jikina naji ya mutu gaba ɗaya sai dai kuma ba wani jimawa naji wani ƙarfi ya ziyarci jikina na musamman, dan ma banda isassan lafiyar da ƙarfin zai tasiri sosai a jikina.bayan duk na gama fitar da kayan can compound na dawo domin rufe ƙofar ɗakin, sai dai a lokacin da na ɗora hannu bisa hannun ƙofar zan jawo, idona ya maƙale akan cikin ɗakin na kasa ƙiftawa na wucewar mintuna uku. zuciyata ta matse, ƙirjina yay zafi, gabana yay mummunar faɗuwa, hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ruwan hawayen da na tsayar na ce ba za su ƙara sauka ba a yau sai ga su tamkar an kunna famfo. cikin mutuwar jiki da fargaba na janyo ƙofar na rufe ina mai juya mata baya, yacca na ke sakkowa daga matakalen benen kamar marar lakka a jiki, kalamansa ne su ke maimaituwa cikin kaina na inje har sai randa ya neme ni, cikin raina sai na ke jin shikenan wannna tafiyar tafiya ce da ba zan ƙara waigowa na kalli wancan ɗakin a matsayin ɗakin aurena ba, sai na ke jin kamar ya furta min kalmomin saki ne kuma saki na har abadan ɗin da ba zamu ƙara rayuwa tare ba, na ke jin sai dai na fara amsa sunan tsohuwar matar Nazifi ba matar Nazifi ba.
sam bana wani gani da kyau na ƙarasa na ce da mai gadi ya tayani fidda kayan waje, idan an sami adaidata sahu ya taimaka ya taro min. kamar ya san abin da yake faruwa na ga jikinsa duk yay sanyi har ya gaza haƙurin furta min lafiya dai ko Hajiya?, na ɗaga masa kai ina riƙe yanayina da cewa,"ana biki ne a gida zanje in kwanaki".
anan bakin gate na tsaya ina jiran ya dawo daga samomin adaidaitar, shiru shiru babu labarinsa kawai na gaji na samu wasu yara na ce su ɗaukar min jakunkunan su kai min titi, muka dandale yanda zan biya su sannan su kai gaba ina biye da su a baya.
sai bayan zuwana titi na tuna da babu fa ko sisi a hannuna, mafi kusa na samu shagon p.o.s na je na ciri kuɗi dubu huɗu, kuɗin da Abbaa ya turo min ne jiya da daddare, banda Allah yasa ya turo min da ban san ya zan yi da tafiyar ba, dole sai dai in tafi a ƙasa don ba zan dai je gidanmu in ce a bani kuɗi zan bawa me machine ba, ko a rayuwar baya ban yi haka ba balle yanzu, ba zan iya tonawa kaina da mijina asiri ba.na sallami yaran na tsaya nan jiran samun mota, na mance gaba ɗaya ban saka niƙabi ba ga zafin rana sai dukan fuskata ya ke. na tsayar da masu adaidaita sahu sun fi shida babu wanda ya tsaya, duk wanda na cewa makwarari sai ya ce ba can yay ba, a taƙaice dai sai da na shafe mintuna kusan sha biyar tsaye kafin na samu wani ya tsaya, shima bayan na gama yi masa kwatancen in da zai kaini sai yace kai ba zai shiga ciki ba, har yay gaba kuma sai ga shi ya dawo yana cewa in shigo.
zan tsaya ciniki ya ce ba matsala abun biya ba zai gagara ba muje kawai, da kansa ya taimaka ya saka min kayan a ciki, wasu ƴan mintuna su ka kawomu ƙofar gidanmu don tun da muka taho bai yi tsaye tsaye ba, in an tsayar da shi ba ya tsayawa, har na ce masa ya ƙara samun passenger ya ce a'a babu matsala yafi so ya sauke ni tukunna.
ya sakko min da kayana, Yaran da suke can ta gefen gidanmu na kira na roƙe su suka shigar min da kayan cikin gida, su ka barni ina ƙoƙarin baiwa mai adaidaita kuɗinsa, sai dai kafin ma na kai ga buɗe jakar naji ya tashi machine ɗin yana shirin tafiya.dakatar da shi nayi da cewa,"ban baka kuɗin ba".
ya ɗan leƙo kai yana cewa,"Hajiya ai an biya".
"an biya?". na tambaya da mamaki. kafin na ƙara cewa,"kaman ya an biya Malam, ban baka kuɗi ba fa tun da muka taho kace ne in bari mu ƙaraso".
YOU ARE READING
ƘAYAR RUWA Book 1 Complete
FanfictionThe story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'anar da ke girgiza duniyar wasu ma'auratan, ta kuma haifar da motsi mai ciwo gami da harbawa a zuƙatan...