*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(22)*
Ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawa shi kaɗai yasan irin zafi da raɗaɗin da zuciyata ke yi a wannan lokacin. Haka na ci kukana na gode Allah kafin in miƙe da ƙyar in wanke fuskata a cikin sink ɗin kicin, kaina kuwa kamar zai tsage saboda azababben ciwo, ga jikina da ke karkarwa kamar me shirin kwancewa zazzaɓi. Abincin da na gama haɗawa na kwasa, sai da na haɗe har da nawa na juye a ciki don sam bana tunanin a yau dai wani abu shi abinci zai shiga cikina, ai ko yawun bakina jinsa na ke tamkar maɗaci.
Ina shiga ɗakin Iyam na aje mata abincinta, kallo ta bini da shi da mamakinta na ganina fess kamar ba wadda miji ke ƙara aure ba, kuma saboda an fi son ganinka a ƙuntatace har ce take to Allah sa ba mugun abu na ƙulla ba don ita bata taɓa ganin wacca za'a kishiya na harkokin gabanta ba rai fess a ranar biki.
Na fito ina ƙwala kiran su Rumana Iyam ta leƙo tana shaida min ai da su aka tafi jiya, ta faɗa tana ta ƙare min kallo gami da ƙara cika da mamakina, kicin na koma na aje abincin na su kana na koma ɗaki, ina shiga kuwa na tarar da wayata na ƙara da sauri naje na ɗauka sai dai ganin sunan da ke kan screen ɗin yasa ban ɗaga ba._"zan yo hayar ƴan daba mu zo gobe"._
Maganar ta Safiyya a jiya ta haska min cikin kai, don haka kawai na mayar da wayar na ajiye, na sani Safiyya me matuƙar damuwa da damuwa ta ce, tana kira ne don taji a wanne hali na ke, to sai dai raunin da ke tare da ni ba zai iya ɓoye halin da zuciyata ke ciki ba wanda ko da na faɗi akasin hakan don ɓoyewa za'a ƙaryata ni, kuma ina tsoronta da ta ƙara tambayar adireshin gidana don Safiyya na daga cikin mutanen da ke tabbatar da maganarsu idan sun faɗa, ko bata zo da ƴan daba ba to tabbas zuwanta sai ya haifar da rashin daɗi. Sai bayan kiran ma ya katse na ga ashe tun kusan da na fita ne ta ke kira miscalls goma haka ta bar mini, na shiga message ina duba saƙon da ta turo._"Beb na kasa yin breakfast, zuciyata taƙi yarda da cewa Nazifi ne zai yi miki kishiya, don Allah ki ɗaga kirana ko ki turo min da address na gidanki, yanzu haka ina shirin baro legos nan da awa ɗaya da mintuna zan shigo kano jirgi zan biyo, kuma don girman Allah ki daina kuka na sanki sarai, am on my way to na zo nayi haukar da zata sa a fasa auren nan yau"._
Girgiza kaina kawai nayi ina sauke numfashi a fili na furta Allah ya sanyaya miki. Ina kwance nayi nisa cikin tunani Ummani ta kira ni, Allah sarki uwa muryarta kawai ya shaida min cikin damuwa take, bayan mun gama gaisawa ta tambayeni babu dai wata matsala ko na ce mata ehh babu komai har ma na shaida mata masu tada hatsaniyar basa gidan jiya Yaya Babba ya zo duk ya kora su sai dai ban sani ba ko sai anjima za su zo amma dai yanzu daga ni sai Iyam ne sai baƙin ƙauye mutum uku da suka zo. Sai sannan naji natsuwa ta samu a muryarta tana aduan Allah yasa ma su tsaya a can gidan su yi bikinsu, haka tayi ta min hira duk dan ta ɗebe min kewa, katin wayarta ma ya ƙare kuma babu jimawa ta ƙara kira wai har ta bayar an siyo mata katin ɗari biyu, haka muka ci gaba da wayarmu na shagaltu a labarin rayuwarta da take bani, har sai da taji an fara yi mata warning kana ta ce to ko ta turo min Hindatu da Sa'adatu su tayani zama zuwa yamma sai su dawo na ce mata a'a kar su zo a sami matsala tunda duk suma zuciyarsu a wuya take. Nan ta shiga nanata min da cewa in ƙara haƙuri da kauda kai cikin maganganunta na kwantar da hankali da sa natsuwa da haka mu ka yi sallama.
Wajen sha biyu na rana gida ya fara cika da mutane, ashe biki sosai Iyam ta shirya matsayinta na uwar ango dan har sai da ta kai an wangale gate, waɗanda su ka fara zuwan duk ƴan uwa ne irin na nesa sai jama'arta na tsohuwar unguwarsu, kan kace kobo gida ya ɗinke da hayaniyar jama'a kace auren fari ne ko kuma zata aurar da ƴar autarta ne. Da kanta ta zo har ɗakina karon farko tun zamanta a gidan tace na sauko na tayata karɓar baƙi kafin ƴaƴanta su zo, bayan fitarta na daɗa gyara jikina tukunna na fita, tunda na sakko ido yayo kaina ni kuwa na mayar da komai ba komai ba kamar yanda mahaifiyata ta ce da ni, don haka cikin fara'a da mutuntawa muka gaggaisa da mutanen da na samu a falo sannan na wuce ɗakin Iyam, can na sameta sunata hidima ita da muƙarrabanta, na ce mata gani me za'ai, tayi min nuni da kulolin abinci tace in ke zuzzubawa ga plate ina kaiwa baƙi. Kamar na juyawata na koma ɗaki ganin an raina min hankali amma haka na daure kawai na shiga buɗe kulolin ina zuzzuba abincin, alala ne da dambu aka yi sai lemon zoɓo da na jinja, idan na zuba kamar faranti biyar sai in ɗauka in je in raba kana na dawo, hidimar baƙin nata dai ta dawo hannuna gaba ɗaya kuma ko kaɗan ban bar wani shaida da za'a karanci ƙunci da kishin da ke danƙare a zuciyata ba balle aji daɗin yaɓa min magana amma a haka ma ban taira ba, don ina jin ƙusƙus ɗin wasu na cewa ko dai ba na son mijin dama ko kuma akwai abunda na ƙulla don haka banza dai ba zan ke wannan sabgogin ba.
YOU ARE READING
ƘAYAR RUWA Book 1 Complete
FanficThe story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'anar da ke girgiza duniyar wasu ma'auratan, ta kuma haifar da motsi mai ciwo gami da harbawa a zuƙatan...