17

78 10 0
                                    

*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''

*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(17)*
To haka dai na ke ta zaman babu daɗi, duk wani nawa da ya kamata ya zo gidan in gansa inji daɗi Abbaa ya hana domin da kansa yasa aka kira masa me gadi da shi Nazifin ya faɗawa me gadin duk baƙon da aka yi ya tambaye shi wurin wa ya zo, in dai wurina aka zo to kar ya bari a shiga. to Yashaik ɗin ma da yake zuwa ya daina, in ya zo dai faɗa ne ke kawo shi to amma a haka na ke farin ciki.
ta ɓangarensa yanzu ba na da wata matsala tunda babu abunda ke haɗamu, daga wajen Iyam ne dai da kuma ƴan uwan nasa abun babu sauƙi matsalar ta tsananta har tafi da, sun matsa min sosai cin mutuncina su ke yanda suka so. duk abunda su ke min haka nake shanyewa in hana kaina damuwa tun da dai haihuwar ba ni zan bawa kaina ba, haka kuma shi da su ke yi akansa ɗin ba ya yi min, tunda ba shi su Atika ya rage nuna damuwa akan rashin haihuwar.
Maman Yasmin kuwa ranar ta saci hanya tazo ta dinƙa faɗan maita da rashin zuciya irin nawa ne yasa na ke zaune a gidan, in bar musu gidan mana rabuwa da Nazifi ai ba shi zai hana ni ƙara yin aure ba. na ce mata sam ba rashin zuciya ba ne ina gudun bakin mutane ne da kuma ɓacin ran iyaye, domin duk ranar da Abbaa ya tashi zai ce min babbar biyayyar da zan masa ita ce na zauna gidan mijina, Ummani kuwa da ta tashi yi min nasiha zata fara ne da haƙuri sannan ta tafi ga batun babbar suturar Ƴa mace shine aure, kuma gidan miji shine mafi daraja wajen ƴa mace.
Yau ya kama lahadi, na tashi da sha'awar yin jan lalle, dama zan je kitso in sha Allah daga can zan wuce ayi min ko iya hannaye ne, da yake muna da taron suna ranar laraba jiya Ummani ta kirani take faɗa min Asiya ta haihu ƴar ƙanwar su Abbaa wacce su ke uba ɗaya, haihuwar sosai ta sakani farin ciki kuma a sannan nima na cire tsammani akan ba zan taɓa haihuwa ba, domin kuwa Asiya ta riga ni aure ita shekara goma kenan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar, babu irin tsangwamar da bata sha ba don zan iya cewa har gwara ni, tunda ita sau biyu mijin na sakinta, ga kishiya da ta sanyota gaba, da yake Allah ne mai bayarwa komai kuma Lokaci ne sai ga shi yanzu Allah ya bata, ni ma Allah yasa ina da rabo, ya bani ko don masu goranta min da ganin ni na gaza.
bayan na shirya na fito domin naje na yi ayyukan da zan yi, a falo na tarar da su gaba ɗaya a zaune, dama tun zuwan Iyam gidan duk ranar Lahadi yini su ke a falo gaba ɗayansu, in ba yaran ne za su wuce islamiya ba, shi kuwa tun can asali lahadi ranar hutawarsa ce da lokacin iyalinsa balle yanzu da mahaifiyarsa ke gidan, in ba masallaci ba ko ƙofar gida ba ya leƙawa. ni dai in ka ganni a falon to zirga zirgar aiki ce don ba na zama balle raina ya ɓaci, idan tana zaune na zo na zauna don tayata hira in ba ya nan sai ta kama faɗin kana zama tare da surukarka waje ɗaya saboda rashin ɗa'a, idan kuma shine zaune a falon babu ita na zo na zauna sai ta kama bambamin ai bani da kunya ba ni da tarbiya dole sai na nuna mata ƴar zamani ce ni, ina faman liƙewa miji alhalin na san tana zaune cikin gidan saboda dai ba na son zamanta so na ke ta bar gidan. ranar har ce tayi da shi ita akan lamarina na ƴan iskan mata sai ta iya tattarawa ta tafi, banda tana ganinsa kusa da ita kullum hankalinta na kwanciya ai tuni ta kama gabanta, yay ta bata haƙuri ni kuma ya sameni yace ko magana na ke son yi da shi in ke iske shi ɗakinsa kar in ƙara zuwa gareshi idan suna tare da mahaifiyarsa.

Yanzunma kallo su ke yi sai dai ita da shi suna hira jefi jefi, yaran ne hankalinsu ya tattara ga tv, nayi sallama su ka ɗago su ka kalleni, a daƙile Iyam ta amsa shi kuwa sai tsareni da ido yay, sannu da hutawa nayi mata domin mun rigada mun gaisa tun ɗazu, na tambayeta abinda take so a dafa da rana tace faten tsaki amma yaji gyaɗa da ganye na ce to, miƙewa nayi na wucewata kitchen ban bi ta kansa ba da bakinsa da naga yana son magantuwa da alama. tun zuwanta na daina dafa son ran kowa sai na tambayeta me take so a girka, har ga Allah jinta na ke yi kamar uwata, kullum ƙoƙarina in kyautata mata amma sam ba na tsira, komai na yi bana burgeta balle yay mata daɗi, burinta ta kushe ni kawai, ku san kullum sai ta faɗa min bata sona bata son zamana da ɗanta, maganar tun tana damuna ma har na daina jinta, takurawar da baiwar Allah nan ke min yayi yawa, ta hana ni shan iska kwata kwata, ta hana na huta na sake, magana tsakaninta da ni daga gori sai cin mutunci da zarafi, kuma duk wannan abubuwan da take min daidai da rana guda ban ji ina so na mata rashin kunya ba ko na ƙi bin umarninta, uwa ce ita ko bata haife ni ba ta haifi mijina.

ƘAYAR RUWA Book 1 CompleteWhere stories live. Discover now