*ƘAYAR RUWA*
FitattuBiyar 2023.
'''Reposting'''*©️Halima.hz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
______________________________
*(13)*
Tare mu kayi wankan da shi, kuma tun a banɗakin labari ya fara canjawa, ko da muka fito tuni na kasa daurewa salonsa, ni dai sai in ce rabon da mu mu'amalantu irin ta yau tun daren farko na, shi kansa ba ƙaramin gigicewa yay ba da yanda yaji ni tamkar sabuwa a leda.
yana ta aikin sauke nauyayyan numfashi ya ke min godiya da sa albarka, wannan kam lazim ne duk lokacin da ya samu natsuwa tare da ni.can kuma ya fara surutan,"Habibty ba ki canja ba, kina nan da daɗinki sai ma ƙara daɗin da kika yi, kinsa naji daɗin da na jima banji ba, ina sonki Habibty, ina sonki, Allah yasa da rabon samun zuri'a mukawa".
hawaye ya fara zubo min, ba komai yasa ba sai tuna baya, lokacin da muke zaman lafiya cikin tsantsar so da ƙaunar juna, lokacin da ko ɗaga murya ba ya yi min, in laifin nayi kuwa cikin kwantar da murya zai min faɗan ya kuma gyara min kuskurena.
sai da cikakkiyar natsuwa ta tabbatarwa kowannenmu kafin muka yi wanka kana muka dawo muka kwanta. lafe na ke kawai a saman ƙirjinsa idanuwana a lumshe, baccin na ke so nayi amma yaƙi zuwa, ba zan taɓa iya musalta daɗi da farin cikin da na ke ji ba a cikin a raina sai dai sam na gaza bayyana hakan a saman fuskata da yanayina. shima shiru yay yana shafa gashin kaina, da ɗaya hannun kuma yana shafa fuskata da tattausan leɓe na, a hankali ya hura min iska a kunne yana ƙara rungumeni jikinsa, muryarsa kwance cikin taushi ya kira sunana."Habibty". na amsa da,"ummm Hubbi".
"ba ki haƙura ba har yanzu? ba ki bar fushin da ni ba?".
"na daina mana Hubbi".
"to amma ai ni kin ƙi nuna min, yanayinki sam babu hakan, ki saki jikinki plss ba Nazifin da ya canja miki ba ne cikin wasu ƴan watanni, wannan Hubbinki ne tun na aure. na sani na saki ɓacin rai har adadin hakan ba zai ƙirgu ba, amma kiyi haƙuri da duka kuskurena, ki yarda da ni kinji, mu komawa rayuwarmu ta baya, rayuwar ma'aurata mai cike da tsantsar so da ƙaunar juna, kwanciyar hankali da shimfiɗadden zaman lafiya".ni dai nayi masa shiru kawai, domin mamaki ne da rashin yarda a raina, gani na ke kawai saboda wata manufa ya ke son sasanta komai, don har yanzu babu ainihin muryar Hubbi a dukka kalamansa da yayi, kuma har yanzu babu wannan haƙiƙanin son da yake nuna min idan muna tare.
"Habibty ni dai na san dukka abubuwan da na ke yi miki wanda basu dacewa, kuma nayi alƙawarin gyara su, to amma kema ina so ki faɗa min me kike so na gyara?".
hawaye ya cika idona na ce,"Hubbi ni so na ke ka dawo mai kulawa da ni da tausaya ni, kuma ka ke min adalci wurin tsayawa ka fahimce ni a duk san da saɓani ya gifta, sannan ka bani damar zama uwa mahaifiya wacce ta tsuguna ta nayi naƙuda bayan ɗaukar cikin wata tara akan Rumana da Atika, ba zan cutar da su ba kamar yanda ba zan so in ga sun halaka ba, in suka yi ba daidai ba akwai buƙatar a gyara musu, don haka kar ka tsammaci gyara tarbiyarsu wurin tsawatar musu da zan yi yana nufin bana ƙaunarsu. wallahi ina ƙaunar su Hubbi tun da aka ce an baka su, kaima ka sani ina tsananin sonka, da kai na ke so na ƙarasa rayuwata, don Allah kar ka kuma goranta min akan ƴaƴan nan, sannan don Allah da Annabinsa Hubbi ka faɗa min sakamakon da asibiti su ka bayar...".
kuka yaci ƙarfina nayi shiru, da sauri ya ɗora haɓarsa saman kaina yana ƙara rungume ni, shiru na ƴan sakanni ya ce.
"insha Allah ba zan kuma yanke hukunci ba tare da na tsaya na saurareki ba, kuma insha Allah ba zan ƙara nuna miki cewa su Rumana ba ƴaƴanki ba ne, na ba ki izini daga yau kiyi musu duk yanda kike ganin za kiwa yaron da kika haifa da cikinki, na damƙa dukkanin tarbiyarsu a hannunki domin ina da tabbacin za ki fini iyawa, abu ɗaya kawai zan fiki akansu shi ne so, kuma ke za ki zama shaida akan yanda na ke so yara. batun kuma gwajinki sakamako ya nuna lafiya lau kike ba ki da wata matsala lokacin haihuwar ne kawai bai yi ba, ni da ke duk lafiya muke Allahne bai bai kawo mana ba".
YOU ARE READING
ƘAYAR RUWA Book 1 Complete
Hayran KurguThe story is a long journey of twisted fate, humiliation, sacrifice, betrayal, victory, Epilogize...INFERTILITY gajeriyar kalma ce me ƙunshe da ma'anar da ke girgiza duniyar wasu ma'auratan, ta kuma haifar da motsi mai ciwo gami da harbawa a zuƙatan...