PAGE 05

507 14 0
                                    

Eman...🥀

Page 5

girgiza kaina kawai nakeyi wanda ya mini nauyi, ina kokarin mikewa tsaye ko ganin gabana banayi saboda duhun daya mamaye mini ido,sama sama naji Abba nacewa"Eman. "sai yayi shiru yarasa me zai ce mini banda hawayen dayake fitarwa.
Ban San inda nake jefa kafafuwana ba burina kawai nabar falon da gidan baki d'aya,gabadaya kaina ya kulle,nakasa kuka nakasa cewa komai banda zuciyah ta dake kokarin tarwatsewa,Abba ne yayi hanzarin rik'o hannuna da karfin gaske,cikin rashin kuzari nake kokarin k'wace ma rik'on shi,ina kallon Alhaji marshal uku uku suka bar falon batareda cewa komai ba,hakan ya tabbatar mini Na rasa Aliyu rabuwa ta har abada!.zubewa nayi duk kokarin Abba Na riqe ni,na zuba ihu wanda ya sa su umma da sauran mutanen gida shigowa falon babu shiri,cikeda farin ciki mummy tace "an fasa auren ne?"tafada tana sakin k'ayataccen murmushi,mama dake gefenta tayi saurin tab'a ta tana nuna mata abba da idanu,mutuwar tsaye yayi ganin farin cikin mummy afili,wanda hakan ya matukar b'ata mishi rai,bai bi takanta ba ya tallafo Kan eman yana fadin"Ku kaita ciki"shine abinda ya furta tareda zama ya rike kanshi me mugun ciwo,Afiya da mama ne suka kaini bedroom dina ina turjewa,sai alokacin nafara kuka mai tsananin ciwo da karya zuciyar me sauraro,wanda yake fitowa daga can kasan zuciyata,sakin muryata nayi iya karfina ina rera kuka wanda ya karad'e gidan baki daya,cikeda takaici umma takalleni tace"ku kyaleta ta tafi duk gidan uban da zataje"tafada cikeda bakin ciki mai tsanani tareda shigewa bedroom dinta tana fashewa da kuka mai tsanani,wani irin zafi kirjinta ke mata,eman taja mata bala'i da masifa arayuwa,gashi tana d'and'anar bakin cikinsa.
   "Kuka dai baze dawo miki dashi ba,gara ma kidaina tara ma kanki gajiya,kin bi kin cika gida da ihu saikace kukan ne zai dawo miki dashi,Aliyu dai kin rasa shi har abada".cewar Mama tana sakin k'aramar dariya,mummy da shigowarta dakin kenan tace"angama mana iyayi zaayi aure abar'ya'yan mu zaune agida,ashe an b'oye mugun hali ,shima duk yaranmu yarasa wacce zaiso sai Eman,aiga irinta nan,".tafada suna kwashewa da dariya itada mama,Afiya tace"namu ake gani,wacce ake ma ganin salihar itace yar hannu numba d'aya,amma dayake 'yar so ce Abba cewa yayi bai yadda ta aikata ba".

Mummy tace "wannan matsalar shice,ya yarda ko kada ya yadda bazai canza mana ra'ayi ba sannan duniya bazata daina ganin aibun taba,wannan lamarin ba karamin dadi ya mini ba,ace Eman tayi aure kina zaune gida kin kusa cimma shekaru talatin aduniya,ni rashin auren nan naki na damuna..."saurin kame bakinta tayi ganin zatayi tab'argaza agaban eman wacce sam bata cikin hayyacinta bare ta fahimci me suke fad'a.
Hannun Afiya taja suka wuce b'angarensu domin ta hango ma afiyar abu mai d'orewa,wanda idan ta jirjirce yazama gaskiya ba karamar riba zasuci ba.
Da kallo mama tabi mummy sannan tayi kwafa ta wuce b'angarenta,so take ta hararo abinda mummy ke kissimawa acikin ranta.
Shigowar Abba ce tasa umma d'ago da jajayen idanunta tana kallonshi,ya zauna gefenta yana cewa"kiyi hakuri fatima komai mai wucewa ne,nasan kina cikin bakin ciki amma kada kiyi neglecting parental duties dinki,Eman bata kyauta ba amma tana buk'atar ki akusa da ita,tana buk'atar support dinki domin tana cikin gararin rayuwa,ayanzu ne yakamata ki tsaya mata idan kowa ya matsa daga gefenta,barinta haka nan shine zai jefata cikin matsala,dan Allah kiyi kokarin danne zuciyar ki kifita hakkin yarinya".
"Tsakanina da Eman saide kallo,ta dasa mini bakin cikin da bazan tab'a mantawa dashi ba,wllhi ko kallonta bana sonyi,ji nake kamar naita dukanta ko hakan zai sassauta mini zafin da zuciyah ta keyi".
Yace"abinda yafaru kaddarar Eman ce,kidaina furta mata kalamai marasa dadi,sanin kanki ne basu da hijabi agareta,ki daina fushi da ita,kila idan kikayi hakan rayuwarta tasamu daidaito".
Cikeda b'acin rai tace"Dama ina rayuwarta zata samu daidaito tana k'untata mini ni mahaifiyarta".
Cikeda b'acin rai ya ce"matsalata dake kenan,bakida fahimta,sannan bakisan girman lafazin uwa akan d'anta ba,kifara yin tunani kafin ki furta ma eman kalma mara dadi domin duk yadda kalmar zatayi affecting dinta kema sai kin samu rabonki,domin saikinfi kowa shiga tashin hankali,shiyasa nake shawartar ki akan ki rungumi yarki,toh ma idan bakiyi ba wazaiyi?wa take dashi daya fiki?".
Tace"wanda ta baiwa ragamar tarwatsa rayuwarta mana".
Yace"har yanzu kina kan bakarki kenan?".
Tace"dan Allah Abba kayi hakuri,bazan iya abinda kakeso ba".
Yace"eman fa yarki ce,karki gujeta kamar yadda mahaifinta da danginsa suka gujeta,yakamata ta samu sassauci ta wajenki".
Kallon shi tayi batareda tace komai ba domin wani haushin eman takeji mara misaltuwa.

Wata jarka mummy ta jawo tana fadin"sha wannan"Afiya tace"ni wallahi nagaji da shan abubuwan nan,gashi basa aiki ".
Cikeda b'acin rai mummy tace"an fada miki nima asan raina nakeyi,ace shekarun ki 27 amma ko kare bakida shi,wannan bakin jini dame yayi kama?maganin farin jinin ma baya miki,wannan lamarin dole saina mike tsaye nayi kamar inayi".
Afiya na tura baki tasha ruwan tana yatsine fuska,mummy tace"na rasa me uwarta ke ba Eman,shegen farin jininta har yayi yawa,yarinya yar 21 ta gigita kowa,shiyasa nayi farin ciki da faruwar wannan abun,ko banza za'a daina cewa anasonta ".
Afiya tace"gata bawani shahararran kyau ba,dame tafimu?".
Adaidai lokacin rafee'ah,Sadiya da Afeefa suka shigo,wani bakin ciki ya turnuqe mummy,ga 'yan mata masu kyau masu jini ajiki babu aure ,gashi babu wacce bata isa yin auren ba.dole ta tashi tsaye akansu zuciyarta tabata shawara.
Tab'angarena bansan wainar da ake soyawa ba,kuka kawai nake yi mara sauti,ayanzu I don't know my purpose of living,sai da magrib na miqe jiri Na d'ibana nayi sallah,bansan wacce addua zanyi ba banda istigfar,shi narinqayi har akayi sallar isha,ahankali na kwanta akasa tareda lumshe idona dasukayi luhu luhu,Amir ne ya shigo da karamin tray ahannunshi yace"Ya eman tashi ga abinci".yafada yana zama agefena,Sosai yaji tausayina,hakan yasa ya miqar dani zaune yana fadin"sorry sister,dan Allah kici abincin"ganin nayi mishi banza yasashi mikewa yafice,b'angaren Hjy kwaise yaje inteesar da Afnan na cin abinci,inteesar tace"ya jikin eman?anjima zamuzo mu dubata ".
Cikeda alhini yace"Dan Allah Ya inteesar kuje wurinta,ita kadaice kuma tak'i cin abinci".adaidai lokacin Salima ta shigo falon,ko bi takansu batayi ba ta wuce wurin eman hankali tashe.
Da damuwa ta kalleni tace"tashi zaune eman,magana zamuyi".hawaye masu zafi suka zubo mini,na tabbatar akan Aliyu zatayi maganar,har raina banason jin abinda zata fad'a,ganin bance komai ba yasa ta miqar dani zaune,tace"eman..."
"Dan Allah karki min maganar fasa aurena"na katseta ina kara fashewa da kuka mai sauti,rungume ni tayi iya karfinta,tace"ba maganar zan miki ba eman,hakuri zan baki akan abinda yafaru,dama can Allah bai qadarta akwai aure a tsakanin kuba,kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai,shi zai miki magani".
Bakina Na rawa nace"Ya Salima wallahi ban aikata ba,sharri suka min,sun cuceni bansan yadda zanyi da rayuwata ba".
"Shhhh eman kibar wannan maganar zamu yita nan gaba,yanzu ki daure kici abincin ki samu karfin jiki".
Haka ta dage naci abincin raina baiso ba.ita tasani nayi wanka na shirya cikin pyjamas dina sky blue color.Nayi kuka Sosai a wannan daren wanda ban tab'a yi ba cikin rayuwata.

Washegari
Da misalin k'arfe 9 nafarka kasancewar sai da asubah na kwanta,ahankali na bud'e ido ina kallon dakina duk abubuwan dasuka faru suka fara dawo mini,hawaye na cigaba dayi tareda mikewa tsaye,tunanin Umma nakeyi wanda yake kashe mini kuzari,saboda nasan halin Umma dakuma yadda relationship dinmu yake,atsorace na fita falo saina tsaya turus ina kallon Anty habiba da umma suna magana,hawaye na bin kumatun umma tace"jiya banyi bacci ba saboda tashin hankali,eman ta cuceni habiba,ki duba bak'ar wahalar dana sha agidan babanta mara misaltuwa,gashi ta d'ora daga inda ya tsaya,suna gana mini azaba,ya zanyi da wannan bakin cikin habiba?ya zanyi da rayuwata? Na tabbatar suna can suna zagina,sannan abin bakin ciki wai sun bar mini ita,ya zare hannunshi daga kanta,eman tasan cewar kad'an babanta ke jira yayi tijara shine tajawo ma kanta masifa,yanzu Aliyu yafasa auren ta waye zai aureta?haka zata karashe rayuwar ta kenan?".
zubewa nayi akasa ina sakin kuka mai sauti,umma ta watso mini harara yayinda anty habiba ke kallona cikeda bakin ciki,kukan dana keyi ne yake b'ata ma umma rai,acewarta kukan munafurcine dan A tausaya mini nakeyi,da fada tace mini"tashi kibar min falo".
Ina kuka nace"umma dan Allah kiyi hakuri"ashe maganar danayi tunzura umma nayi,ban lura da tasowarta ba sai saukar duka naji takoina,dukana take Sosai Anty habiba na tayata domin tafi kowa cin burin bikina,ina sane naki tashi saboda nabaiwa umma damar dukan nawa,tunda shine take ganin idan tayi zata samu sassauci acikin zuciyar ta.anata tunanin kuma tana ganin tsantsar raini ne,wato bata isa daniba kenan ko zata kashe ni bazan bar mata falon ba,azuciye tayi wurgi dani jikin bango tana huci,saida anty habiba ta tsorata da yanayin umma,ban taba ganin zallar fushinta ba irin na ranar,cikin d'aga murya take ce mini"tashi kibar min falo,banason ganinki,get out of my sight".tafada da karfi Sosai wanda hakan ya janyo hankalin su Mummy,da sauri ta fado cikin falon tana kallon drama acewarta,goshina daya fashe Na rike ina sakin kuka mai sauti,hakan yasa anty Habiba kamani tashige dani daki ganin mama da hjy kwaise sun shigo.
"Lafiya nake jin tashin muryarki?"hjy kwaise ta tambaya tana tsare umma da idanu,mummy ce tayi saurin cewa"ita da eman ne,baki ga dukan data mata ba har dasu fasa goshi,shide duka baya gyara yaro".mummy tafada tana guntse dariya,mama ce tajata suka koma main parlour domin suyi dariyarsu da hujja.
Hjy kwaise tace"Assha,fatima baa ma yaro haka,duka da zagi banaki bane,jawota zakiyi ajikinki kusamu fahimtar juna,duk gidan nan wa kikaji tana fad'a da d'anta asarari?bakya gudun bakin mutane akan yarki?dan Allah ki gyara"cewar hjy kwaise.
Abinda ke kara k'untatawa umma rai kenan,nasan sarai yadda suke takun sak'a da kishiyoyinta amma na jawo mata abin magana.


https://arewabooks.com/book?id=64a568cb8194f8956681682b

https://chat.whatsapp.com/JBW41FiQjju590lKMlEoay
(Ga masu son shiga group dina).

EMAANWhere stories live. Discover now