EMAN...PAGE 24
Kallon fuskarshi tayi with a weird look and surprised facial expression,karo na farko data kalle Shi kenan tunda yafara driving tasa kanta a titi to avoid eye contact wanda for sure xai sata xama uncomfortable,kallonshi tayi for a very long time tana d'ora abubuwan dayakeyi akan mixanin hankali,he's a mad and obsessed lover,fahimtar hakan yasata sassauta murya tace"bud'e min kofa".tafada atakaice,baice mata komai ba illa kallonta daya cigaba dayi kamar wani tsohon maye,tayi mishi kyau ne na tashin hankali,shifa ko maganar data mishi yanxu bawani jinta yayi Sosai ba,he's lost at the moment,ya nutsa can cikin duniyar sonta,Shide yasan abu biyu yayi alokacin,nafarko shine locking motar na biyu kuma kallonta wanda baya gajiya dashi,shifa idan kallon eman aiki ne he'll apply for the job and work tirelessly 24/7 batareda ya dauki leave ba,ganin he's lost in thoughts gashi kuma kallon dayake mata nasata jin wani iri yasa tace mishi"ni ka bud'e min kofa,jirana sukeyi ".tamkar da gunki take magana kawai ya mata shiru sai kallonta yake,batada option din daya wuce had'e kanta da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya,tunaninta na tabbatar mata Sadeeq is obsessed with her,abubuwan dayakeyi sun tabbatar da hakan, tausayin shine ya narke mata axuciya saboda ta kalli ire-iren movies na obsessed lovers,kuma duk wanda ta kalla basa gamawa lafiya,is either of the two kodai su rasa wanda suke son ko kuma they end up hurting either their lover or themselves,by now rayuwarta is just like a movie wanda a Hollywood xasu bashi tambarin blockbuster,Cikin wata irin weak voice yace"bana son ki tafi ne"saurin dago da fuskarta tayi tana xaro ido tace mishi"why?but i have to "yace"ban gaji da kallonki ba Eman,sannan bana son kiyi nisa dani ayanxu,ina son ki kasance tare dani akowani lokaci".Sosai gabanta yafadi tafurta innalillahi wainna ilaihi raji'un,wani irin bala'i ne wannan?atake idanunta suka cicciko da ruwan hawaye,sai ta kasa cigaba da kallon shi saboda tsantsar tausayin shi dake ratsa xuciyarta da jikinta gabadaya,Eman mutum ce me shiga damuwa idan taga makusancinta acikin matsala,hakalinta baya tab'a kwanciya sai an samo solution,balle yaya Sadeeq wanda ya mata alheri masu yawa arayuwa,fahimtar matsalar shi yasa tace"bawani dadewa xa'ayi ba,kaga gabadaya sunxo ni kadai suke jira"kallonta yayi tareda yin karamin murmushi,ya duba wayarshi dake ring sannan ya kalli Eman,baxai iya amsa kiran ba sai kawai ya maida wayar ya ajiye,asanyaye kuma atausashe yace"you can go"tareda unlocking motar,da sauri tafita tana sauke ajiyar xuciya,sai kuma ta juyo asanyaye tana kallonshi,ganin ita yake kallo har lokacin yasa xuciyrta breaking into tiny pieces,saide ta tabbatar ma kanta kome xai faru baxata tab'a amince mishi ba,that she promised herself.Dr Ansar Clinic ya wuce yana jin ciwon kai yana saukar mishi,koda ya shiga consultation room kallon tsanaki dr Ansar ke mishi,ya duba blood pressure dinshi yaga yayi rising Sosai,can yayi karfin halin cewa"saifa ka rage tunani da shiga damuwa Sadeeq,rayuwar nan gabadaya yar hakuri ce,kowa daka gani yana cikin matsala in one way or the other,amma idan kace xakayi focusing akan matsalar without solution akwai damuwa Sosai,kaga yanxu jininka ya hau fiyeda last week,and I warned you akan ka daina yawan tunani,kaje wurin therapist din danayi maka recommending?".shiru Sadeeq yayi alamar baije ba kenan,dr Ansar yakara mishi prescribing antihypertensives,Yana fadin"ka riqa shan maganin ka akan lokaci sannan kayi kokarin rage damuwa for your own sake,karkaje garin neman gira arasa ido,kada garin tunanin duniya ka rasata gabadaya,you're digging your own grave Sadeeq,ka kiyaye don Allah"dr Ansar yafada in a pleading tune,murmushi Sadeeq yayi aranshi yace ga babbar maganin damuwa ta da bakin ciki Eman,afili kuma yace"in shaa Allah Dr,thank you "daga nan pharmacy ya je yasiya drugs din ya ajiye acikin compartment dama anan yake ajiyewa saboda bayason kowa yasan da ciwon nashi,balle fauxa wacce yasan itama damuwar xata shiga Sosai,gida ya koma ya kwanta yacigaba da aikin tunani,domin bai ga ta yadda xa'ayi ya daina ba,idan anga ya daina shine ya mallaki Eman.
From a far Fauxa ta hango Eman wacce tayi isolating kanta agefe daya,Tai ta mamaki sannan ta karasa inda take,ganin ta nisa cikin tunani yasa Fauxa dafa shoulders dinta tace"Eman are you okay?"tausayin Fauxa ne ya cika mata xuciya,hawaye suka taru acikin idonta,bata san ya Fauxa xataji ba idan tayi finding out abinda ke faruwa,amma ta tabbatar Fauxa baxatayi recovering ba inde ta gane halin da Sadeeq yake ciki akanta,damuwa ce tayi mata yawa amma babu ta yadda xata fadama Fauxa her exact problem even though tana son fada mata kodan ta sauke nauyin daya tsaya mata akirji for 2days now,"magana nake miki Eman,what's wrong with you?"bakin Eman na rawa tace"banida lafiya ne"tafada tareda fashewa da kuka,saurin rungumeta Fauxa tayi tana jin hawaye na kokarin xubo mata saboda Fauxa mutum ce me tsananin tausayi,sun dade ahaka sannan Fauxa taja Eman suka fita daga hall din,parking space sukaje ta bud'e musu mota suka xauna tanata kallon Eman din tace"meke damunki?"asanyaye Eman tace"headache ya Fauxa,ji nake kamar kaina xai tarwatse,I'm in pain,in so much pain"tafada tana fashewa da kuka mai tsuma xuciyar me sauraro,tagaji ne iya gajiya,she's too young for this,tana cikin tsananin damuwa,Umma ce taxo ran Fauxa,ta tabbatar sunyi magana da umma ne,sai alokacin tayi data sanin fadama Firdausi problem dinta,taji wani guilt da kunya suna rufeta,ta manta wacece Eman and what she's going through,asanyaye tace"Eman ki kwantar da hankalinki,nafada miki I'll always be there for you koda gabadaya mutanen farko dana karshe xasu matsa daga gefenki ,kinada Fauxa kuma in shaa Allah baxanyi k'asa a gwiwa ba saina tabbatar komai ya Daidaita acikin rayuwar ki,dole xanyi ma umma magana,kinyi k'ank'anta da wannan tashin hankalin"itadai Eman kallon Fauxa kawai takeyi tana tunanin meyasa good people ke yawan shiga matsala?wani pharmacy Fauxa taje suka siyo paracetamol,saida ta tabbatar Eman tasha tabata abinci sannan suka cigaba da sisters night din,even though Fauxa ta lura da yadda Eman is not socialising.
Kamar yadda yamata alkawari past 8pm ya gama shiryawa cikin wani milk color yadi me kyau da tsada,ya dora hula akai wacce tayi mishi masifar kyau,baxai tuna when last yasa kaftan ba,saboda inde kaganshi da kaftan to yana nigeria ne,ko Sallah ce taxo saide yasa jallabiya,kallo daya xaka mishi ya tafi da tunaninka harma da nutsuwar ka,ga kyau ga kudi gashi dogo mai good structure atsaye,gashi ya iya gayu ga beautiful accent,komai ya hada saide shi mutum ne me fara'a amma kuma yanada saurin fushi,yana da anger issue fiyeda misali,yana cikin fesa turare Hajiya kwaise ta shigo tana murmushi,ita kanta yayi mata kyau,tace"Ina xuwa haka?"yana murmushi yace"Mami will always be Mami"tayi murmushi tace"as long as bakada aure yanzu nafara maka irin wannan questions din,koda kayi auren ma ba dainawa xanyi ba".yace"haka ake so ai,iyaye su riqa sanin whereabouts din yaransu"tace"good boy,now tell me where are you going to?"yana murmushi yace"to see a friend "hajiya kwaise tace"ok,Allah ya dawo dakai lafiya,idan dare baiyi ba xamuyi magana in shaa Allah"da toh ya amsa sannan yafita,itace ta rufo mishi part din saboda 'yan biki dasuka cika gidan,motar shi Mercedes Benz AMG ya shiga yana driving calmly,dayake basuda wani nisa yasa in few minutes ya karasa gidan su Yasmeen,ko kuma nace mansion dinsu Yasmeen,har ciki ya shiga yayi parking sannan ya kirata,tana ganin shine tafito cikin tafiyarta ta big babes asalin ajeboter,har entrance ta fito cikeda farin ciki,she can't wait to see Al'ameen,shikam har lokacin yana cikin mota saide waya yakeyi da Mr linc,ya dauki kamar five minutes sannan yagama wayar yafito yana tafiya majestically,Yasmeen na tsaye tana blushing,shima murmushin yakeyi yana mata kallon kauna,tace"welcome sweetheart "tana gaba yana binta abaya suka shiga parlorn,ganin babu kowa yasashi rikota yana bata tight hugg,sun dade rungume da juna kafin suyi breaking hugg din,ya xauna yana fadin"I miss you so much Yasmeen"tace"I miss you too,this time around baxan yarda da wannan dadewar ba"yace"worry not,this time around I'm moving things to the next level in shaa Allah,kinga tare xamu koma and you'll have me all for yourself,always and forever my Yasmeen"wani farin ciki Yasmeen ta tsinci kanta aciki tace"I love you Al'ameen,I love you so much,always and forever "Louisiana pasta da Lasagna tayi serving dinshi saboda he's a pasta person,sai strawberry daiquiri da Virgin mojita,gefe kuma snacks ne da spicy deep fried chicken,tana cikin xuba mishi abincin yace"where's mommy and Aya?"tace"sun fita,ni kadai ce agidan"jinjina kai yayi yana cin abincin suna firar su ta soyayyah.
Tunda suka fara tafiya Eman tasa kai a titi tana kallon moving vehicles,tunani kawai takeyi yayinda Fauxa ke driving tana kallonta time to time,cousins din su Fauxa dake bayan motar sai hira sukeyi suna complementing pictures and videos dinda sukayi,gaban Eman ne yayi tsananin Faduwa ganin sun shigo layin gidan,take taji wata sabuwar damuwa ta dirar mata,wannan ne karo na farko da xataje gidan in more than a Month or two,tana son ganin Umma amma kuma tana tsoro dakuma shakkar me xata tarar daga wurin Umma da ma sauran mutanen gidan,saida xuciyarta takusa fasowa daga kirjinta saboda damuwa,Fauxa tayi parking tana karantar reaction din Eman,tana yin parking Al'ameen ya shigo shima,ganin shi yasa tayi saurin fita daga motar saboda basu samu damar haduwa ba tunda yaxo,rungume fauxa yayi yana fadin"Ina kika shiga?"mariya da xuwanta wurin kenan tace"ohh ita kadai kagani kenan ko?"tafada tana hararar shi,kowa yasan special place din da fauxa keda shi axuciyar Al'ameen,Shide bai ce komai ba illa kallon mariya dayayi yana murmushi,sai kawai ta shige ciki tana amsa kiran Hjy kwaise,Dan juyowa Fauxa tayi tana kallon Eman wacce har lokacin ke cikin mota ta nisa Sosai cikin tunani ga damuwa written all over her face,da dan karfi tace"Eman,fito mana"sai alokacin ya kalli direction din da eman take,tafito ahankali tana tafiya kamar me counting steps,asanyaye ta daga ido karaf suka sark'e acikin Na Al'ameen wanda yake kallon ta yana tuna maganar da hajjo tafada masa,ya ji mata babu dadi Sosai musamman daya ganta cikin damuwa yanxu,saide baice mata komai ba haka itama ta saukar da idanunta kasa,fauxa taja hannunta suka shiga ciki,part din umma suka nufa duk su ukun,saide fauxa tana tsakiyarsu,afalon Umma suka xauna by then hawaye sun fara xubo ma Eman,she really wants to see Umma amma tana fargabar hada idanu da ita,asaman carpet Eman ta xauna arakube kamar xata shige cikin kujerar,Fauxa kuma tashiga bedroom din umma yayinda Al'ameen ke kallon Eman din yana mamaki,hawayen dasuka kasa daina xubo mata yake kallo,shi mutum ne mai fushi amma yanada tausayi,farar daya yaji tausayinta,yana imagining kamar shine fa yanxu ace Yasmeen tace baxata aure shi ba,bai san adadin tashin hankalin daxai shiga ba arayuwa,yana mahaukacin sonta fiyeda misali,kamar me counting words yace"I'm sorry for what happened Eman,khair In shaa Allah"cak tunaninta ya tsaya,ta dago ido tana kallon shi da dan mamaki,daga farko bata gane me yake nufi ba,saida tadanyi tunanin few seconds sannan ta fahimta,wato har an fada mishi abinda yafaru da ita kenan?take taji xuciyrta na suya,tana data sanin abubuwa masu yawa,ta samu kanta da kasa bashi amsa,shima dayake ba jiran amsarta yake ba sai kawai ya maida hankalinshi ga Tv,cak umma ta tsaya sanda ta ga Eman xaune afalon,kallo daya tayi mata taga hawayen dake xubo ma yarinyar ga damuwa abayyane asaman fuskarta,tafi seconds goma tana kallon Eman din sannan takarasa falon tana fadin"Sannu da shigowa Son,dazu naje part dinka baka nan"maganar umma ce tasa Eman saurin dago ido tana kallonta,taga gabadaya hankalin Umma nakan Alameen tana mishi murmushi,wani xafi Eman taji aranta amma ta daure tace"Ina yini umma"da "lafiya lau"ta amsa ,fauxa dake tsaye tana jin babu dadi,tarasa menene problem din umma arayuwa,sai kace ba musulma ba,gabadaya akan Eman bata san miye yadda da kaddara ba,
Kitchen umma ta wuce fauxa kuma ta xauna akusada Al'ameen tana kallon Eman,shima kallon Eman din yayi ya kalli fauxa baice komai ba,saide ya fahimci akwai matsala atsakanin Eman da Umma,wayar Fauxa ce ta fara ring,koda ta duba Sadeeq ne me kira,da hanxari tayi picking ta lankwasa murya tace"Yes sweetheart!"ta daya bangaren yace"hala a can xaku kwana?"tayi dariya tace"ka ganmu agida,tunanin kwanan mukeyi"gaban shine yayi mummunan faduwa domin abubuwa ne masu yawa ke axalxalar xuciyar shi,yana son ganin Eman sannan yanason suyi magana koda da safe ne idan fauxa ta fita,tunda yakoma gida yaxama restless,he's having obsessive thoughts about Eman,and the need to be by her side to protect her akowani lokaci,ga tsananin kishinta daya ke ji alokacin,ba tunanin da beyiba akan Maxa nacan suna Kallon Eman din,dakyar ya iya controlling kansa bai koma hall din ba,jin yayi shiru yasa tace"why are you silent?"da mamaki ta cire wayar daga kunnenta jin ya kashe batareda yace komai ba,ta kalli Al'ameen wanda ke kallonta shima,saide baiyi magana ba saita sauke ajiyar xuciya kawai.Sadeeq na kashe wayar ya dauki car key yanajin xuciyar shi Na kokarin fashewa saboda damuwa ya tafi can gidan domin dauko su.Lafiyayyiyar noodles Umma ta kawo musu da indian chai,inde girki ne umma lamba daya ce,dan awurinta Fauxa ta koya abinci har ma ta kware Sosai,haka Eman ma ta iya girkin fiyeda misali.Al'ameen yace"Umma I'm full,xan sha tea din kawai"asaman carpet Fauxa ta ajiye musu abincin,tana kallon Eman tace"xo muci".murya adashe Eman tace"bana jin yunwa"Kallonta Umma tayi cikeda mamaki,fauxa tace"bafa wani abin kirki kika ci ba awurin,kici sai ki kara shan maganin"murya a kausashe Umma tace"idan bataci yanxu ba xata nema anjima,ita yunwa ay ba sa'ar kowa bace" fauxa ta marairaice tace "bata jin dadi ne"shiru Umma tayi tana kallon Tv,Shide Al'ameen mikewa yayi ya wuce part dinshi,Fauxa tabishi da kallo,can itama ta mike tabi bayan shi,afalo ta tarar dashi ya mike kafa yana danna iPad,tashiga bakinta d'auke da sallama sannan ta xauna,yace"Fauxa ya akayi?"tace"shawara naxo nema"sai kuma tayi shiru tana tunani,yace"I'm all ears"asanyaye tace mishi"ko kuma mu bari sai an kammala biki kawai"Shide kallonta yakeyi can yace"ok Allah ya kaimu".
Fauxa na fita Umma ta mike tana fadin"idan kin gadama Hajjo na ciki ki shiga ki gaisheta"tana kaiwa nan ta koma bedroom,jiki asanyaye Eman ta shiga dakin,ta tarar da Hajjo na kwance tana bacci,ta dade Sosai tana kallon tsohuwar sannan ta fito,cikeda mamaki take kallon Sadeeq xaune afalon, Suman tsaye tayi gabanta na tsananin faduwa,sai ya mike yaxo daf da ita yana kallon fuskarta,yana son saka kwayar idanunshi acikin tata amma hakan ya gagara,sai jujjuya ido take batason yayi nasarar sark'e idanunsu awuri daya,ratsawa tayi ta gefen shi xata wuce yayi nasarar damko chantily veil dinta,akuma daidai wannan lokacin umma tafito daga dakinta,gabanta yayi mummuman faduwa,taji tsayuwar na neman gagararta,anya ba gixo idanunta suke mata ba?sadeeq ne rike da mayafin Eman?me hakan ke nufi?wani jiri ne ya fara d'ibarta tana jin bakin cikin Eman ne xaiyi ajalinta.#obsession#
#betrayal*Zaynab Yusuf ✍🏼
09037909996

YOU ARE READING
EMAAN
Romancedelve into the interesting story of emaan and alameen hate-love story which will get you in suspense from start to finish and every other emotion.