PAGE 72

489 11 0
                                    

EMAAN....PAGE 72

Written by Zaynabyusuf✍🏼

Cikin lilac color posh and expensive abaya Rafee'ah ta shirya,tana tsaye agaban mirror tana starring kanta cikeda birgewa,she never tot for once rayuwarta xata canza haka,she must say her life couldn't be better at the moment,domin sayyid yana iya bakin kokarin shi ganin yayi placing smile asaman fuskarta,nude makeup tayi applying kana ta yafa veil din abayar tana sakar ma sayyid dake tsaye abayanta kayataccen murmushi,ta bangaren shi kuma yana amsar sakon murmushin nata ta cikin mirror,ta baya yayi hugging dinta tightly yace"har kin gama?"murmushi tayi tace"yes dear,zamu iya tafiya"ba musu ya riko hannunta suka sauka kasa yana fada mata kalaman soyayyah suka shiga cikin black color Range Rover dinshi,yana driving calmly yake bata labari mai sanyaya rai da sanya xuciya nishadi har suka karasa gidan Abba,with so much care yace"i hope everything is fine dear,idan ma akwai wani problem pls don't hesitate to call me immediately kinji ko?"saida yayi maganar sanann gabanta yayi tsananin faduwa,saboda tun jiya mummy ke kiranta awaya wai tana son ganinta tayi missing dinta,Rafee'ah bata kawo komai cikin ranta ba illa farin ciki mara fasaltuwa daya mamaye mata xuciya,Sayyid ya riko both hands dinta yayi pecking sannan yace"my regards to everyone pls,idan nadawo anjima xan shigo"gyada mishi kai Rafee'ah tayi tace"take care hubby,I love you "saida ya lumshe idanu sannan yace"I love you more"kana ya bita da rakiyar idanu saida yaga ta shiga ciki sannan ya juya motar ya tafi,da sallama Rafee'ah ta shiga main parlon saide babu wanda tagani illa musaddiq dake kwance asaman kujera yana game a iPad,cikeda fara'a yaron ya gaisheta tace mishi"umma na nan?"girgixa mata kai yayi yace"no she went out not too long "tace"when is she coming back?"musaddiq yace"tace min in 2hours time in shaa Allah "gyada kai Rafee'ah tayi tashiga part din mummy,cikeda damuwa ta karasa ciki tana kallon mummy da Rafee'ah sun hada kai sai dirxar kuka sukeyi,musamman mummy data fita acikin hayyacinta da nutsuwar ta,saurin rungume ta Rafee'ah tayi ruwan hawaye suna cika mata idanu,with a trembling voice tace"mummy meya faru?"sai alokacin mummy ta kalli Rafee'ah wacce ta canza sosai within few days,dalilin daya sa hankalin mummy yad'an kwanta kenan,saide batace komai ba illa kallon Rafee'ah data cigaba dayi wacce ke goge mata hawayen da suka b'ata mata fuska,muryar Rafee'ah na rawa tace"mummy pls tell me what happened?"sabon kuka mummy ta fashe da shi instead of answering Rafee'ah,wannan dalilin ne ya sake tayar da hankalin Rafee'ah sai ta koma kan afiya tace"Wai meya faru ne dan Allah?"bakin afiya na rawa tace"we've been exposed Rafee'ah..."hawayen dake makale a idanun Rafee'ah ne suka zubo mata,dama irin wannan ranar take jiye musu kenan,ranar yin nadama abisa abubuwan dasuka shuka,afiya tacigaba da cewa"yanxu kowa yasan nice nayi ma emaan sharri,nice nasa aka dora hoton fuskarta asaman those dirty pictures na prostitutes,ni ce na fita da ita aranar duk dan plan dina yatafi acikin tsari yadda kowa xai yadda without second thought ,hatta abubuwan da aka gani acikin bedroom dinta nice na ajiye su saboda hassada xata auri Aliyu dan gidan Mukhtar Marshall,sai gashi Allah ya bata yaya alameen wanda hatta mukhtar Marshall din bai kaishi arxiki ba da tara abin duniya..."ta nisa kana tacigaba da cewa"itakuma mummy dama abba yasan duk abubuwan datakeyi,shine yace mata ya jingine aurensu xuwa wani lokaci..."dafe kirji Rafee'ah tayi cikeda tsantsar damuwa tace"innalillahi wainna ilaihi raji'un "."Abinda nake jiye muku kenan,ranar jin kunyah da yin nadama alokacin da nadamar batada amfani,yanxu wa gari ya waya afiya?akullum wannan ranar nake kokarin nusar dake amma kika gagara fahimtata all thanks to mummy dake zugaki akowacce dak'ik'a na tafiyar lokaci,amma hakan bashi ne xaisa kiyi blaming dinta 100% ba,saboda ke me hankalice yakamata kiyi tunani mai zurfi kafin ki gabatar da komai acikin rayuwar ki,idan kika kalle ni nikaina babbar example ce awurinki,babu yadda mummy batayiba akan relationship dina da sayyid,sai na xauna nayi tunani mai xurfi gameda hakan,na dauko reasons din mummy Na dora su akan mixanin hankali,sai naga reasons din nata are not valid,kai tsaye nayi duba ixuwa nagartattun halayen sayyid,nayi watsi da batun dukiya saboda arxiki na Allah ne,kuma sayyid nada ilimi da aikin yi wanda xai rikeni daidai gwargwado,daga karshe me ya faru?ashe sayyid is from a wealthy family,kinga ni tsakani da Allah naso shi saboda kyawawan dabi'unsa kuma koda ace sayyid dagaske middle class dinne banida matsala da hakan,xan cigaba da alfahari da kasancewata mata agareshi""alokacin da kikaga kowa baida xance saina emaan ba hassada yakamata kiyi ba,sannan ba tsanar ta yakamata kiyi ba,xama xakiyi ki karance ta sosai sanann ki lura da abubuwan datakeyi masu kyau wanda yake rud'ar mutane har suke haukacewa akanta akallo naxahiri tun kafin su mu'amalanceta,kinga ni I don't care about that ko kadan shiyasa lamarin bai taba zuwa raina ba,saboda akoda yaushe I always try to be myself arayuwa,babu ruwana da kwafar wani ko kuma naji cewar wani ya fini,idan ma wani ya fini ay nima na fi wasu koba haka ba?tunda ke haka xuciyarki take you should've learned from her bawai ki rika kulla mata sharri ba,naji dadi kin fahimci hakan da wuri tun kafin lokaci ya kure miki,you still have time to mend your ways afiya,and i wish you all the best in your changing process"daga haka wurin mummy ta koma wacce har lokacin take zubar da hawaye tace"karki damu mummy khair in shaa Allah,as long as kin gane kuskuren ki kuma you're ready to become a better person ina ganin bai kamata ki dinga kuka ba,addua xamu dage dayi har lokacin da xuciyar Abba xata sauko yadaina fushi daku,kuma inada yakinin Abba xai yafe miki in shaa Allah"wannan maganar ce tasa mummy shanye kukan data keyi,ta rungume Rafee'ah tana cewa"I'm sorry for everything daughter,dan Allah kiyi hakuri"tana nadamar abubuwan data yi abaya,saurin girgiza kai Rafee'ah tayi tace"it's okay mummy,I love you "....

EMAANWhere stories live. Discover now