PAGE 29

341 11 1
                                    

EMAN...PAGE 29

  Eman ta kalli Sadeeq cikeda mamakin ganin ya rame Sosai in two days kamar wanda ya daɗe yana jinya,tsugunnawa yayi ya ɗauko textbooks ɗin still yana kallonta da idanunshi masu cike da tsananin kaunar ta,she was dumbfounded kawai kallon shi takeyi,gyara tsayuwar shi yayi yace"why are you punishing me?do you think I deserve this kind of punishment ?"idanunta ne suka ciko da ruwan hawaye,saboda yadda yayi tambayar dole ya karya maka xuciya,"kinyi tunanin xan rabu dake just like that after what happened?you really think so?"nan ma shiru tayi tana kallon yadda hawaye suka cicciko a idanunshi ,before you know it sun fara xubowa,runtse ido tayi tana jin wani xafi yana addabar xuciyarta,"talk to me pls,maganar ki xata sa naji sanyi araina, i miss you so much Eman,I Miss everything about you,kallon fuskarki,talking to you,dropping you at school and everything,I love you so much,more than anything in this life".Hawaye ne masu xafi suka xubo ma Eman,saide har lokacin she couldn't say a single word,toh mexata ce mishi?tasan duk maganar daxata fito daga bakinta baxata mishi daɗi ba,saboda she'll never accept his love,gara ta mutu batayi aure ba akan ta amince ma soyayyar shi,yace"nasan Fauxa will understand me,it's not what you're thinking,nida Fauxa are doing good,babu wani abu daya canxa,kinga first mission accomplished kenan ko?"yacigaba da faɗin"remember I told you sai inda ƙarfina ya ƙare,I mean what I said,then why are you treating me this way?ni ina can ina wahalar yadda xamu kasance tare ke kuma in the other hand kina axabtar da xuciyata,all I need from you is support Eman,idan kikayi supporting dina kin gama min komai arayuwa,ni kuma hakan zai ƙara mini himma wurin cimma k'udirina akanki"goge hawan dake xubo mata tayi sannan tace"kayi hakuri yaya Sadeeq,nima I mean what I said,baxan iya abinda kake so ba,fatana shine Allah yabaka hakuri dakuma juriyar rashi na,Allah ya sassauta maka ya cire maka sona acikin ranka cirewa ta har abada,sannan ya ƙara dankon soyayyah tsakaninka da Ya fauxa,nikuma ya kawo min wanda yafi xama alheri acikin rayuwata,wanda baxai sa ni cikin damuwa da tashin hankali ba,ayanxu farin cikina yafiye min komai aduniya,saboda nobody is responsible for my happiness,sannan baxan taba farin cikin kasancewa tare dakai ba,kayi hakuri"tafaɗa tareda amshe books ɗin daga hannunshi,he was lost at that point bai ma san ta ƙarba littafin ba,saboda gabaɗaya baya cikin hayyacinsa,maganganun Eman kamar ruwan dalma yake jin xubar su acikin xuciyarshi,ta gefenshi ta ratsa xata wuce yayi saurin riƙo veil din abayar ta,hakan yasa mayafin ya warwaro Allah yasa akwai hula akanta,yace"zan iya kneeling anan agaban kowa da kowa idan hakan xai tabbatar miki da yadda nake ƙaunarki,akan sonki ba irin kukan da banyi ba,akan kaunarki ba irin damuwar da ban shiga ba,akan kaunarki na ƙi bin shawarar mahaifiyata da tace na hakura dake,akan ƙaunarki na faɗa ma matata cewar I'm in love for the second time,even though nasan hakan xaiyi hurting ɗinta beyond repair,hakan xai iya lalata relationship ɗina da ita,yet I told her because I'm madly in love with you,rashin ganinki is my worst nightmare Eman,dan Allah find a small spot in your heart for me".Kuka ta fashe dashi sosai tana jin soyayyar Sadeeq  ta xame ma rayuwarta bala'i da masifa,wannan wace irin ƙaddara ce?"Kinsan I hate seeing you cry,it's breaking my heart,dan Allah ki daina"Kamar ɗaukewar ruwa yana magana ta daina kukan,saide bata ce mishi komai ba taƙara juyawa xata wuce,ya sha gabanta akaro na biyu,yana kallonta da idanunshi that are full of love for her,samun kanta tayi da kasa hada ido dashi,saboda these days idan tana kallonshi tana jin xuciyarta na yin laushi and she doesn't like that,yace"Look me in the eyes Eman"gabanta ne yayi mummunan faɗuwa,kamar yasan abinda take gudu kenan,cikeda dakewa ta aro jarumta sannan ta xuba idanunta acikin nashi tana kallo,yayi nasarar kashe mata jiki da wani irin mayataccen kallo mai tsayawa axuciya da ruhi,Sosai gangar jikinta ke amsar kallon nashi amma taƙi nuna mishi hakan a xahiri,shikuma dama abinda yake so kenan,tace"if you don't have anything to say ni xan wuce class,already an fara lectures "kamar me counting words ya kalli soft lips ɗinta sannan yace"I love you "yafaɗi hakan yana girgixa kai alamar tabbatarwa,jin I love you ɗin tayi har kasan xuciyarta,yau ne karo na farko dataji hakan acikin xuciyrta.taɓangaren Al'ameen yana xaune cikin mota mamaki ne ya kusa yin ajalinshi,gumi na karyo mishi duk da ACn dake cikin motar,har wani rufe ido yake yana buɗewa saboda tsananin mamaki,xuciyar shi kuwa kamar an cinna mata wuta sai balbala take,this is the highest level of disrespect dakuma disloyalty,yakasa apprehending abinda ke faruwa tsakanin Sadeeq da Eman,tausayin Fauxa kamar xai fasa mishi xuciya,he can't imagine halin daxata shiga idan ya faɗa mata cewar Sadeeq da Eman are in a relationship,cikeda ƙunar xuciya ya fito daga motar yana tafiya ahankali duk yadda yake ji da kuxari yanxu ji yayi jikinshi yayi wani irin sanyi,gwiwoyin shi sun sage,fuskarshi kawai xaka kalla ka tabbatar yana cikin ɓacin rai mai tsanani,musamman idanunshi dasukayi jajir suka ƙanƙance,Basu lura da tahowar shi ba har lokacin daya tsaya agefen su,Sadeeq yace"I'll forever love you Eman,and I'll fight everything that comes my way ahanya ta ta auren ki...."saukar wani mahaukacin naushi asaman fuskar shi ne yasa shi yin shiru yana jin shi wani sama-sama kamar aduniyar gajimare,kafin ya tabbatar da abinda ke faruwa Al'ameen ya shaƙe mishi wuya yana faɗin"kafin ka kashe Fauxa ni xan kasheka!i'll kill you right away before you kill my sister, you ungrateful bastard!"yafaɗa yana jijjiga Sadeeq da ƙarfin gaske,kuka Sosai Eman ta fashe dashi ganin yadda Al'ameen ya shak'e wuyan Sadeeq,tayi sauri riqe hannayen Al'ameen tana cewa"karka kashe shi,ba abinda kake tunani bane..."bangaje ta yayi ya watsar agefe yana faɗin"how dare you lay your filthy hands ajikina,how dare you touch me?"yafaɗa yana komawa kanta,"kinyi tunanin kema ƙyaleki xanyi?shashasha wacce batasan halacci ba,dama hausawa sunyi gaskiya tsintacciyar mage bata mage,kuma makashinka yana tare dakai,Abbana ya dauƙo ki tun kina yarinya yayi miki komai arayuwa,bai banbanta ki da ƴaƴanshi na cikin shi ba,ya gatanta ki ya dawo dake mutum mai daraja,ya fito daku daga ƙasƙantacciyar rayuwar da kikeyi agidan mahaifinki,ashe babanki yasan mugun halinki shiyasa yake treating ɗinki like trash,ashe yasan ke ɗin macijiya ce kuma macuciya ,axxaluma,mara imani da tausayi, i promise you you'll pay for this "yafaɗa yana nuna ta da hannu yana jijjiga kai alamar tabbatar wa,Sadeeq ne ya shiga tsakiyar su yana watsa ma Al'ameen wani irin kallo yace"how dare you insult her?"shiru Al'ameen yayi yana mamakin furucin Sadeeq,mamaki yahanashi cewa komai,"Eman itace wacce nake so kuma nake da muradin aure,kuma xan tabbatar da babu abinda zai hanani aurenta,not even you or anyone else ".Al'ameen yace"baxaka aureta ba,that I promise you,I don't care about your whatever disorder,amma nayi maka alƙawari idan ka auri Eman sede a lahira idan anayi,akan hanyar ka ta auren Eman saina xame maka ƙaya ta takawa,akan hanyar ka ta auren Eman saina xame maka dutsen tuntuɓe,akan hanyar ka ta auren eman saina xame maka Fitina da tashin hankali,mark my words"yafaɗa yana nuna shi da hannu cikeda ɓacin rai,yacigaba da faɗin"and don't you dare tell Fauxa about this even in your wildest dream"yana kaiwa nan ya juya furiously.Saurin riƙo shi Sadeeq yayi yace"who gave you the right to interfere in my affairs?waye kai daxaka faɗa min yadda xan tafiyar da al'amarin gidana?Fauxa is my wife,get that into your head,she's my wife and I'm warning not to interfere,saboda xaka sha mamaki fiyeda tunanin ka"wani bakin ciki ne ya turnuƙe ma alameen xuciya,abinda ke ta xarya acikin ranshi kenan,yasan Fauxa na bala'in son Sadeeq ba lallai bane tayi abinda xai ɗora ta akai,cikin dauriya alameen yace"you're going to die a miserable death saboda Fauxa will never accept this stupidity,gara ka mutu akan Fauxa tashiga halin dakake son saka ta aciki,I hate you Sadeeq,I hate you to the extent da ko ganinka bana son yi,you're a bloody ingrate me manta alheri,kuma mugu axxalumi me shirin haɗa bala'i da masifa,Allah baxai baka damar nan ba,I'll make sure kaida Eman saide kallo daga nesa,that I promise you for the second time,sannan cin amana da kukayi you'll surely pay for it,xan nuna muku Fauxa nada gatan da babu wanda ya isa ya ɓata mata rai ya xauna lafiya,not even you,her crazy husband "yana gama faɗin haka ya juya ya shiga motar shi ya harba kan titi kamar xai tashi sama saboda takaici,itadai Eman statue taxama awurin,wani bakin ciki na taso mata tace"ka kyauta min,dama abinda kake so kenan,ka ganni cikin matsala da tashin hankali,you've succeeded in ruining my life,all thanks to you Sadeeq "tafaɗa tana fashewa da kuka mai tsanani tana jin xafin kalaman alameen har ƙasan xuciyarta,xata  wuce ta gefenshi ya ƙara shan gabanta akaro na uku,muryar shi na rawa yace"kiyi hakuri Eman,I didn't me to hurt you...."saurin dakatar dashi tayi tace"spare me!,you love me you can't live without me bla bla bla nagaji da sauraren maganganunka,nagaji da jinsu"bata jira amsar shi ba ta wuce abinta tana jin xuciyrta na suya.
Afalon ƙasa ya tarar da Fauxa,tana sanye da wata pink colour short gown,ta saki dogon gashinta wanda ya sauko har bayanta,idanunta nakan waya,daga gani message take turawa saboda gabaɗaya hankalinta na kan wayar,ƙamshin exclusive turaren wuta ne ya sashi lumshe idanu(Bakhoor incense place 09037909996) ya rungume hannu akirji yana kallon Fauxa,saida tagama sending message din sannan ta juyo asanyaye saboda jikinta na bata someone is starring at her,babu komai akan fuskarta ta illa ruwan hawaye dayake xubo mata,saurin xama yayi agefenta ya jawota xuwa jikinshi feeling relieved,ahankali kuma yakai lips dinshi saman kunnenta yace"I'm sorry babe"abinda ya iya faɗa kenan,sai kawai ya haɗe lips dinsu giving her deep snog,he used his tongue and wipe away her tears romantically,duk yadda xuciyarta ke son bayyana mishi ɓacin ranta ta kasa,saboda yadda sonshi ke fixgarta yana ratsa kowani loko,lungu da saƙo nacikin xuciyarta,kuma tasan hakan da yayi  ba haramun bane.har yanxu alameen yahanata ce ma Sadeeq komai akan lamarin,shiyasa kawai ta xuba mishi ido,shikuma sadeeq is using that opportunity to lessen her stress level.cikin wata murya mai daɗi yace"I love you babe"wasu xafafan hawaye ne suka xubo mata,har lokacin bata ce komai ba,hakan yasa yacigaba da bata romance mai narkewa axuciya,wanda ke sa Fauxa feeling over the top saboda yes! Ta tabbatar Sadeeq na tsananin Ƙaunarta.Tunda yashiga part dinshi ya kulle kofar falon gabaɗaya saboda bayason ayi interrupting tunanin daxaiyi,tun da yake aduniya bai taɓa jin tsanar kowa ba sai Sadeeq da Eman,he hate them with passion,he can't believe his eyes no more,abubuwan daya gani yau sun girgixa shi,sun rikita mishi tunani,Eman of all People Sadeeq ke so??Eman of all people ke soyayyah da Sadeeq???yarinyar dasuke ma kallon ƙanwar su?ya daɗe bai tsinci kanshi cikin ɓacin ran dayake ciki ba yanxu,saide ya tabbatar ma kanshi baxai barsu su cimma nasara ba ,dole sai ya rabasu ta kowacce hanya!.wayar shi dake ring ya kalla,koda ya duba Yasmeen ce me kiran shi,ajiyar xuciya ya sauke sannan yayi picking yana lumshe idanu,ta ɗayan ɓangaren Yasmeen tace"Aslm babe"yace"yes sweetheart,tell me something sweet"tun da taji haka tasan cewar yana cikin damuwa,dan haka ta fara bashi labari wanda ta tabbatar xai sanyaya mishi rai da ruhi.
Ta ƙarasa labarin da cewa"Allah ya sanya rislama da sanyi acikin xuciyarki my love,dan Allah kadaina saurin fushin nan,it doesn't suit you,kaifa babban mutum ne"lumshe ido kawai yayi baice komai ba saboda so many things are going through his mind.
  This day is one of the worst days In Emans life,tayi kuka har saida idanuwa suka daina xubar hawaye,kausar na gefenta tana aikin lallashi amma abanxa,ita kaɗai tasan xafin da xuciyarta ke mata,maganganun alameen ne suka tsaya mata arai da xuciya suke baƙanta mata rai,kausar wacce duk ta damu da ganin yanayin Eman din tace"nasan baxaki fada min damuwarki ba,but atleast take it easy on yourself,kinga mutane sai tambaya suke ko lafiya".sai alokacin Eman ta kalli kwayar idan kausar tace"you won't understand my pain,ni kaina xanso ace nakoma gida ahalin danake ciki,amma ina cikin tsananin fargabar komawa kausar,ina cikin tashin hankali,bansan me xai faru ba idan nakoma,I just want to go far away from this city"hawaye ne suka xubowa kausar saboda tausayin Eman,sai kawai ta rungumeta tana shafa bayanta alamar rarrashi,kukan ne ya saukar mata da ciwon kai mai tsanani,ta jingina kai da bango hawaye na xubo mata tana tunani...ƙarfe biyar daidai ta koma gida,tun daga gate taji hankalinta ya tashi,a main parlor ta tarar da Abba,Mami da alameen axaune,saide alameen ya faɗa duniyar tunani,har ƙasa ta tsugunna ta gaida Abba da Hjy kwaise,Abba ya dubeta Sosai sannan yace"Eman are you okay?"ajiyr xuciya ta sauke domin a tunaninta maganar dawowarta xaiyi,murya can ƙasa tace"kaina ke ciwo"wani mugun kallo alameen ya watsa mata yana jin kamar ya shak'e ta ya huta saboda takaici,irin kukan da Fauxa ke yi ne akansu ke ƙona mishi rai,Abba yace"Subhanallah,hope kin sha magani?"ta girgixa kai ahankali tace"a'a"Abba yace"maxa ki je kisha,Allah ya sawwake"ita dai hjy kwaise kallonta kawai takeyi tanajin wani iri aranta,gashi dai burinta ya cika Eman ta dawo amma batasan meyasa batayi farin ciki da faruwar hakan ba,Eman ta miƙe alameen ya bita da wani shegen kallo har ta Ƙurewa ganinshi,hjy kwaise ta wani xaro ido tana kallon alameen gabanta na faɗuwa.Kamar yadda wannan rana ke cikeda baƙin ciki ga Eman haka wannan ranar is totally opposite dasu Mummy,domin wannan ranar is one of the best days of their lives,bakin mummy yaƙi rufuwa tunda sukayi waya da Hajiya Zainab ta tabbatar musu cewar in few days time xasu turo asa date din biki,hakan yasa mummy rungume Afiya cikeda farin ciki,su Rafee'ah da Sadeeya Na gefe suna murna,mummy tace"nifa nakasa yadda da wannan lamarin,gani nake kamar amafarki,oh Allah nagode maka daka nuna mini wannan rana"tafada tana miƙewa ta tafi main parlor,ta canxa kalar tafiya tana rangaji kamar karamar yarinya,tana xuwa daidai part din umma saita shiga tana wani munafukin murmushi,afalo ta tarar da umma tana koya wa Musaddiq homework,ta shiga tana faɗin"duk dan bakin cikin tanda sai munci wainar ƙwai,inde mutum ya tsaya ga Allah to wallahi ya ishe shi,kana xaune xakaga yana warware maka matsalolin ka"murmushi umma tayi tace"haka ne,Allah ya mana jagora"mummy tace"Amin,ina mutan gidan Fauxa ashe an dawo"shiru umma tayi can tace"ehh tadawo"mummy ta wani tabe baki tace"su Afiya dai Allah yayi,sai de muyi fatan Allah ya kawo na  ƴan baya"umma tace"ma shaa Allah,Allah ya sanya alheri"bata tsaya amsawa ba tayi gaba abinta,tasan koba komai ta bakantawa umma rai,ta shiga  main parlour ta sanar ma Abba,cikeda farin ciki yace"Allah ya kaimu".
Rafee'ah ce ta kalli Afiya keenly can tace"nifa ban fahimci wacce hajiya Zainab kike nufi ba"dariya Afiya tayi tace"matar Mukhtar Marshal mahaifiyar Aliyu ita nake nufi"da mamaki Rafee'ah da sadeeya suka kalli juna,sadeeya tace"yayan Aliyu xaki aura?"murmushi Afiya tayi sannan ta gyada musu kai tana cigaba da cin abincinta,Rafee'ah ta dinga kallonta,because if she's not mistaken yayan Aliyu bai dade da aure ba,kenan a second wife xataje,ko kuma yaya abun yake?Misalin k'arfe takwas da rabi Eman ta shiga dakin hajjo,lokacin Afiya tana ciki suna labarin yadda bikin nata xai kasance,bakin hajjo yaki rufuwa saboda farin ciki,ganin Eman yasa Afiya hade rai,ta galla mata harara kasa-kasa tareda sakin siririn tsaki,can dai ta mike tafita daga dakin,kallonta kawai Eman tayi tareda sauke ajiyar xuciya,ta xauna agefen Hajjo tareda dora kanta acinyar ta,hajjo tace"ke Emani kiji tsoron Allah,karasa ni kikeson yi ko me?tsofe-tsofe dani kin haye mini cinya"shiru Eman tayi batace komai ba,hajjo tace"yau naga ikon Allah,kinxo kin haye mini cinya nayi miki magana kinyi banxa dani"nan ma Eman batace komai ba sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi,hajjo tace"maxa daga min cinya tunda abin naki rashin mutunci ne"rai bai so ba Eman ta tashi xaune tana kallon hajjo,shigowar Alameen ce yasa gaban Eman faduwa,shima ya wani hade rai yana kokarin juyawa ya fita hajjo tace"dawo nan"tsayawa yayi can dai yace"ina xuwa "yakoma part din shi yana jin xuciyar shi na kuna,harga Allah baya kaunar ganin Eman.ajiyr xuciya Eman ta sauke sannan ta mike ta fita,hajjo dai ta bisu da kallo.
Adaren Ranar Mummy ta kira gabadaya danginsu da kawayenta ta sanar musu auren afiya,idan aka tambaya date sai tace in few days time xa'ayi fixing,kafin wani lokaci labarin bikin Afiya ya xagaye danginsu gabadaya.Abba na xaune a part dinshi mummy ta shiga jiki Na rawa ta xauna,ya kalleta yace"meya faru?"gyara xama tayi tace"batun kayan daki naxo muyi,kasan fa ba lokaci,dan hajiya Zainab ta tabbatar min a wata 1 xa'ayi bikin"da mamaki Abba yace"ke Aisha,daga ganin sarkin fawa sai miya tai xaki?kibari asa date din mana sai ayi komai daga baya,tunda dai Allah ya hore mana ko a sati daya xamu gama siyan komai"bata rai mummy tayi tace"amma bikin Salima anfi wata biyu ana shiri dayake ana son uwarta,ni kuma saniyar ware shiyasa kake ce mini a sati daya xamu gama Siyayya "tafada tana matsar kwalla,bud'e baki Abba yayi cikeda mamaki,can dai yace"ina jinki"saurin goge hawayen tayi sannan tace "kaga dai dama can akwai wanda takeso,kawai kudi xaka tura "yace"ba damuwa xan tura muku"da farin ciki mummy ta mike tana jinta over the top,Shide Abba ya bita da kallo.
Murmushi Rafee'ah tayi tareda lumshe idanu lokacin da Sayyid yace"kice nima na turo kenan,sai ahada ayi tare"dan xaro ido Rafee'ah tayi tana jin gabanta na faduwa,ta wacce hanya xata fadama mummy wannan maganar?tasan baxata taba yarda ba,ko ita Afiya baxata yadda ba ahada hadaddan bikinta da nasu,jin tayi shiru yasa ya fahimci inda ta dosa,yace"karki damu Rafee'ah,na yaba Sosai da hankalin ki kuma in shaa Allah baxakiyi sanadin mallaka mini xuciyar ki ba"shigowar mummy ce tasa Rafee'ah saurin sauke wayar tana sinne kai kasa,cikeda takaici mummy tace"wato ban isa dake ba ko?kin mayar dani yar iska agidan nan kullum magana nake miki amma bakya ji,da wannan matsiyacin kike waya bayan Na hanaki,inde rashin jin maganata abun yine  mu xuba mu gani,kina gani dai inda yar uwarki tasamu miji,maimakon kema ki maida hankali kisamo daya daga cikin abokan shi kin tsaya kina biyewa matsiyaci wanda baxai tsinana maki komai ba"ita dai Rafee'ah shiru tayi saboda tana son sayyid kuma hankalinta ya kwanta dashi,arxiki kuma Na Allah ne idan yaso zai bashi,da wannan tunanin Rafee'ah tayi kwanciyarta tana tunanin yadda zata bullowa lamarin.Eman Na kwance taji shigowar message,ta duba wayar tana mamakin Sadeeq,bata tsaya karantawa ba ta ajiye wayar agefe domin tayi alkawarin ta daina sauraranshi,abinda ya faru yau ne ya tsaya mata arai,musamman kalaman alameen agareta,sune suka sa hawayen bakin ciki xubo mata,ta gyara kwanciyrta tana son yin bacci kodan brain dinta ta huta,tana rufe ido umma tashigo dakin,acan bakin kofar ta tsaya tana cewa"Kinyi bacci ne?"saurin tashi xaune Eman tayi tana kallon umma,sai kawai ta fashe da kuka mai karfi,tayi saurin mikewa ta rungume umma tana kuka mai tab'a zuciyar me sauraro,wani sanyi da ni'ima takeji yana fitowa daga jikin umma yana shiga jikinta,bayan tsahon lokaci ta tsugunna har kasa ta riko hannun umma tana fadin"dan Allah ki yafe min"umma wacce jikinta yayi sanyi tace"Allah ya yafe mana baki daya Eman,Allah ya miki albarka"wani farin ciki ne ya mamaye xuciyar Eman wanda ta dade bata tsinci kanta aciki ba,ta kara rungume umma iya karfinta tana kuka me dauke da dariya,sunfi minti uku ahaka sannan umma tafita daga dakin,Eman kuwa kasa komawa tayi ta kwanta saboda farin ciki,she can't believe her eyes,ahaka wani ni'imtaccen bacci ya d'auke ta tareda mafarkin umma mai dadi,itama umman sai taji zuciyarta tayi wasai yau din.tabangaren Sadeeq yana tura message din ya goge sannan ya ajiye wayar sanin cewar kota gani bazata mishi reply ba,Anum ce ta shigo dakin jiki asanyaye tace"daddy,mommy is crying"xaro ido yayi yace"where's she?"yarinyar tace"she's inside her bedroom "ajiyr xuciya ya sauke jiki ba kwari ya shiga dakin Fauxa,kamar yadda Anum ta fada axaune yaga Fauxa tanata kuka,ga kuma waya akunnenta da alama dai waya takeyi,tsayawa yayi har ta kammala sannan ya karasa ya xauna agefenta,ya jawota xuwa jikinshi sannan yace"da wa kike magana"cikin kuka tace"alameen"wani bakin ciki ne ya tokare mishi wuya,can yace"kiyi hakuri fauxa,banida any other option...."tayi saurin cewa"who's the girl?wacece Yarinyar "ta tambaya tana goge hawaye,even though alameen forbade her from asking such question,amma at this point taji baxata iya ba,she needs to know who the girl is.....

Zaynab Yusuf✍🏼
09037909996

EMAANWhere stories live. Discover now