PAGE 79

410 9 0
                                    

EMAAN...PAGE 79

Written by Zaynabyusuf✍🏼

One month later...
Asanyaye emaan ta bud'e lumsassun idanunta,bata sauke su akan komai ba illa asaman fuskar alameen dake bacci agefenta,hannunshi na rike da nata kamar xa'a kwace mishi ita,murmushi tayi saboda kullum sabuwar shakuwa ce ke ratsa xuciyarsu,soyayyar da suke ma juna is out of this world,gefenta ta kalla inda kyakkyawan baby boy ke kwance acikin cot dinsa,yaron na sanye da kayan shi na fendi brand,bacci yake peacefully kamar yadda alameen keyi,kamar yaron daya da alameen kamar an tsaga kara,babu ta inda ya dauko kammanin emaan komai na yaron iri daya ne dana alameen,lumshe idanu tayi san d'anta na ratsa koina na jikinta,hannunta ta cire daga cikin na alameen wanda hakan ne yasa shi ya bud'e idanu yana kallonta,tayi rau-rau da fuska saide batace komai ba,murmushi alameen yayi yace"dauko mana shi"ba musu emaan ta dora yaron asaman laps dinta,yaron sai mutsu-mutsu yakeyi yana son ya bud'e ido alameen yace"wani suna ne acikin ranki?is it daddy or Abba"shiru emaan tayi kana ta girgixa kai alamar a'a,alameen ya kalleta keenly yace"fada min wani suna ne?"ruwan hawaye ne suka cika idanunta,tace"Abubakar Sadeeq "cikeda mamaki alameen yace"nice one,bansan ya akayi na manta ba"emaan tace"Alhamdulillah yau nacika alkawari "alameen yace"Allah ya raya mana Abubakar Sadeeq,ya gafarta ma namesake dinshi"emaan tace"Amin ya rabbi"adaidai lokacin Sadeeq ya bud'e idanunshi yana kallon both parents dinshi,emaan tace"lovey look murmushi yakeyi "alameen yace"what a beautiful smile"ya fada yana taba soft pink cheeks din sadeeq,adaidai lokacin fauxa da hajjo suka shigo dakin,hajjo ta tabe baki tace"kaide kaji kunyah wallahi ace Yarinya tana jego ka wani nanike mata baxaka barta ta huta ba"tayi maganar tana kyabe baki,murmushi fauxa tayi ta xauna agefen emaan tace"sannu da xuwa and congratulations,Allah ya raya mana"alameen yace"he's named after your late husband,Allah ya mishi rahama"hawayen farin ciki fauxa tayi tace"thank you both,Anum da Asad sun gode,Allah ya raya mana Sadeeq "da amin suka amsa hajjo harda guntun hawayenta itama.Farin ciki wurin su Mami da umma ba acewa komai,anty habiba dawowa tayi gidan da zama gabadaya saboda ta kula da emaan yadda yakamata,baban emaan designer clothes ya siya ma jaririn masu masifar tsada,bayan haka ya mallaka mishi kaddarori masu yawa,Abba ne ya dauki ragamar shagalin suna wanda akayi shi amadadin bikin emaan da alameen,cikin golden color komole emaan ta shirya,anyi mata nude makeup mai kyau sai glowing takeyi kamar ba itace ta haihu ba,bikin sunan ya samu halartar dignitaries and top government officials,emaan da Sadeeq sun samu gifts masu yawa fara daga cash xuwa kan kaya da toys,yadda alameen ya kashe kudi saida emaan ta tsorata sbd 2023 Land Cruiser ya siya mata amatsayin push gift,yayi mata kayan fitar suna kala bakwai kowanne da daham dinshi masu matukar kyau da tsada,umma hawayen farin ciki ne suka xubo mata ganin yadda kowa yake ma emaan kamar zai lashe ta,abun mamaki har dasu mummy da afiya saide kowa yaja baya dasu sun xama wani iri acikin dangi....misalin k'arfe goma ne na daren Friday wanda yayi daidai da kwana ashirin dai dai da haihuwar emaan,umma da habiba na xaune emaan kuma tana kwance asaman kujera Sadeeq na hannun anty habiba tana mishi rawa emaan na kallon su tana dariya,anty habiba tace"rayuwa kenan,yaushe aka haifi emaan nake mata rawa haka wai yau d'anta ne ahannuna "umma tace"rayuwa haka take dama,shiyasa ake son mutum ya xamto mai tsari da goals arayuwa"anty habiba tace"kwarai dagaske,idan mutum baida tsari sai rayuwa tayita wucewa mutum bai tsinana komai ba har lokacin mutuwa ya riske ka"haka suka cigaba da hirar emaan nata chatting da alameen yana fada mata irin missing dinta da yayi saboda ya koma London last two weeks itakuma sai tayi arbain xata koma,yanxu batada kawar data wuce wayarta saboda kullum cikin chatting da video call suke,almost every day sai fauxa ta aiko mata da mouthwatering delicacies haka baban emaan yana yawan zuwa ganin Sadeeq,dama kullum da yamma sadeeq awurin abba yake xama kowa nuna ma yaron soyayyah yakeyi,kar ma emaan taji labari,agaban kowa take nuna son sadeeq sometimes umma har kunya takeji  idan emaan tayi wani abun.Cikin black color versace outfits alameen ya shirya xaije gidan sarah kamar yadda yusuf ya gayyace shi dinner aranar,different Nigerian cuisines ta dafa sukaci suka koshi,suna cikin hira sarah tace mishi"guess what?"cikeda mamaki alameen yace "I can't guess but I'm sure akan yasmeen ne"sarah tace"yeah,an sa mata rana,nan da 2months bikinta"wata sassanyar ajiyar xuciya alameen ya sauke yace"alhamdulillah,Allah ya albarkaci union din"yusuf da Sarah suka ce amin alokaci daya.Sosai alameen yaji dadin news dinnan saboda har lokacin yana jin guilt acikin ranshi amma yanxu ranshi yayi fess burinshi daya emaan da Sadeeq su dawo su cigaba da gudanar da rayuwa cikin aminci so da kaunar juna.

*wanda sukayi joining class dina should holla me via 09037909996*

EMAANWhere stories live. Discover now