ASMAUL HUSNA 4

1.9K 86 0
                                    

ASMAUL~HUSNA 4

★★ *ASMA'UL~HUSNAH* ★★
© *MISS HAFCY*
® *NWA*

*DEDICATED TO BESTY HUSNAH*

0⃣4⃣

AJ ya juyo "Na'am Mr. Daddy yane? Ban jinka sosaii fa" Daddy cike da takaici yace " ta ina zakajini bayan ka toshe kunnuwanka kanaji wakar wani arnen banza , yaushe zakayi hankali ne? Kana ganin abokai na amma ko kazo ka gaishesu? Saima wucesu dakai kana bin wakar" AJ yayi dariyar "au sorry fa ban kula ba Mr. Daddyna" ya kalli su Abba " Abokan Mr. Daddy yane? Hope kuna lafiya? Wani bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar Daddy take ya sunkuyar da kansa cike da takaici da kuma kunya, Sukuwa su Abba suka amsa masa"lafiya lau Ammar ya gida?" Zai amsa da sauri Daddy ya daga mai hannu alamar ya tafi tabe baki yai ya maida earpiece dinsa yana cigaba da bin wakarsa.

Daddy daya sunkuyar da kansa beyi aune ba yaji siraren hawaye na fitowa daga idanuwansa da sauri ya sharesu sannan ya dago ya kallisu Abba cike da kunya " Kuyi hakuri dan Allah ka haifi d'a amma baka haifi halinsa ba, wallahi na rasa yadda zanyi da yaron nan duk da cewa tun farko sakacina ne, amma yanzu sam halayensa na damu na kullum addua nake masa amma maimakon ya gyaru sai ma kara lalacewa dayake, yanzu takai takawo ma wai ba kullum yake kwana a gida ba? Allah ya kyauta gabadaya sukace ameen Allah ya shirya mana zuri'a baki daya sai hakuri.

Malam Barau yakai Apple ya lumtsuma a bakinsa sannan yace " nikuwa shekarun Ammar nawa ne?" Daddy yace " 1st july ze cika 27 fa" Malam Barau yayi saurin cewa " Yaron ya isa aure kenan ma, to Allah ya shirya mana su baki daya, gabadaya suka amsa da Ameen bayan d'an lokaci sukai salama suka tafi Bayan Daddy ya cika su da abun arziki.

Aj ne zaune akan grass carpet na wani babban park da suka je shida yan clique dinsa ba mace kodaya dan a cewar Aj yau suje park ya gaji da zuwa club kuma be sha'awar zuwa da 'yan mata su hudu sukaje shi, Bobo Aliyu(Lee) da kuma Bash.

AJ yayi shiru kamar yana tunanin wani abu sannan ya kalli abokannsa " Guys wats todays date?" Bobo daya fi shishige masa duk cikin abokansa yace " Yau 23rd June" AJ yayi wani ihu " yay! Birthday dina 1st july, ashe kenan na fara preparation na birthday, amma ina tunanin wannan birthday din a London za'ayi shi, kodan saboda frnds dina na can" gabadaya suka washe baki amma da abin zefi kawo lyt Bobo yace " ahhh sai na samo 'yar baturiyar gfrnd mu jame, to amma kai zaka biya mana koh?" Aliyu wanda suke kira da Lee yace "kai dallah kaine matsiyaci, wakake tunanin ze biyama? Kai zaka biya da kanka if nt kayi zamanka"

AJ ya tintsire da dariya "kuyi masa azuri kukam,ina yaga kudin biya? In ba jarin atamfofin da babansa ke siyarwa ba ze dauko" Bobo ya sha kunu "ku bansan rashin m fa" AJ ya sake fashewa da dariyar mugunta sannan ya dafa kafadarshi "worry not Bobo mutumina zan biya ma ai kai na amana ne! " Bobo yayi murmushi " yanzu naji magana" Wayar AJ ce tayi kara ya duba Mr. Daddy ne ke kira sai da ta kusa tsinkewa sannan ya dauka
" hello Daddy yane?"
"Kai wai ba na hanaka cewa Yane ba, ko bakiji salamar dana ma ba? To banaso dagayau, Okay Mr. Daddy na dena"

Daddy ya sake cewa " ka bar duk abinda kake kazo gida, zamuje gaisheda Hajiya" AJ yace "nifa hutawa nake gaskiya zaa takura min, bari dai nazo" Daddy ya amsa " to ina jiranka Allah ya shiryeka Ammar, ya katse wayar.

AJ ya kalli abokansa "lemme go sai kun taho" ya karbi Key dinsa a wajen Bobo wanda dayawan lokaci Bobo ne ke tukar motar AJ ya maidashi kamar drivernsa, ya kalli Bobo yace " sai ka biyo su Lee ni na tafi" aa bari na biyoka muje" Su Lee sukai dariya " shishiginka yayi yawa Bobo inda zaka burgemu sai ka bishi har inda zasu da Mr. Daddy din" dariya Aj yayi "kun takurawa Bobo fa kubarshi ai mutumina ne" ya shiga haddadiyar benz dinshi Bobo daze tuk'a motar ya bata key suka kama hanyar gida.

**Husnah**
Husnah zaune da Mama, Khaleefa da kuma Ya Usman suna hirarsu, Husnah tace " Mama kinsan kuwa saura izu biyar muyi saukar hadda Alkur'ani ji fa nake kamar a mafarki wai nice har na haddace Alkur'ani a kaina kai Alhamdulilah!" Khaleefa yace " Su Yaya Husna an zama Hafiza" tayi dariya Mama tace " masha Allah gaskiya fa naji dadi sosaii ina alfahari dake 'yata"

Ya Usman yace "ni Mama anya ma ba zuqale tayi ba? Nifa ban yadda da saukar nan tata ba" Husnah ta tabe baki " ai dama haka zakace, amma in kana tantanma jamin ko ina kaga in na kasa sai kace zuqala ne" Ya Usman yace " tohm sai ki shirya muje zuwa"

Mama tayi dariya " kaidai Usman akwai ka da neman magana" Husnah tayi saurin cewa "no Mama barshi yaja min ai bana tantama muje zuwa" tsakiyar suratul Ma'ida yaja mata take ta k'arasa har sai daya ce ta dakata atakaice sai daya ja mata wajen ja shidda tana karasawa ba tare da gyra ba sannan yace " gaskiya ne na yadda dake Allah yasa dai anyi na tsoron Allah"
kallansa tayi ta tabe baki tai dariya " Ameen though naga alama black belly kake dan kaga kai izu goma kawai ka haddace nagaba yai gaba( ta mai gwalo) yunkurowa yai da niyyar kai mata duka na wasa da gudu ta tashi ta shige daki tana masa gwalo.

Hafcy.blogspot.com

MissHafcy at 13:38

ASMAUL~HUSNAWhere stories live. Discover now