ASMAUL HUSNAH 6

1.9K 70 0
                                    

ASMAUL HUSNA 6

★★★ *ASMA'UL~HUSNAH* ★★★
© *MISS HAFCY*
® *NWA*
*DEDICATED TO BESTY HUSNAH*

0⃣6⃣

Alhaji Barau yayi gyran murya sannan yace " tunda dai har yaro nan ya isa aure meze hana asamo nutsatsiyar yarinya me hankali da ilimi a aura masa, na tabbata zata gyrashi ya shiryu yau da gobe tafi k'arfin wasa" Daddy yaja numfashi sannan yace "ban k'i ta taka ba, amma ai samo yarinyar shine aiki" Abba dayayi shiru tun da'aka fara maganar yaja numfashi sannan yace " Lallai kam" Malam Barau da sauri yace " Ahh Alhaji Muhammad ina Husnah ta wajenka? Ko an mata mijine?" Abba yace " eh to nadai bata lokaci ta samo miji amma har yanzu shiru," Daddy da sauri yace " dan Allah ka rufa min asiri ka taimaka a hada auren nan da Husnah dan Allah" gaban Abba ya fadi, sai kuma ya tunano baya, ya tuno yadda Daddy ya mai hallaci a rayuwa wanda har yau ya kasa biya masa, ya tuno Daddy ya taka rawar sosai wajen ganin yayi arzik'i ya masa komai a rayuwa lokaci yayi da shima ze saka masa, cikin d'akilewar murya yace " tham Alhaji Jabir na amince amma a bani lokaci muyi maganar da yarinyar da kuma mahaifiyarta allah ya zaba mafi alheri" take Daddy ya washe baki farin ciki fal a zucuyarsa " nagode nagode bansan da wani baki zan gode ma ba" Abba yace "bakomai ana tare" cike da farin ciki suka tattauna abinda ya kawosu suka wuce.
☆☆☆
AJ zaune a palour shida Mummynsa suna ta shirye shiryen tafiya London, Mummy ta kalleshi "nifa Ammar so nake mu tafi da Eshale ta rage mana wasu ayyukan" AJ ya juyo da sauri had'e da tsaki " tab Allah ya kiyaye, ba inda zata je wallahi wata k'azama da ita ace sai mun tafi da ita? Ni ai sai ta bani kunya" Mummy tace " kaifa dad'in dakai kenan, waze dinga mana 'yan share sharen in munje kasan ba a hotel zamu sauka ba, a gidanmu nacan zamu sauka" AJ yace " kin manta da Ruth ne? Mai aikina tacan? In munje basai mu kirata ba" Mummy tai dariya " to shikenan, ba matsala wai kai meya hadaka da Eshalen nan? Naga alama jininku sam be had'u ba" AJ ya tabe baki " ba'a abinda tamin kawai dai kawai dai" Mummy tayi dariya "Allah ya shiryeka" .

Abba ne zaune a palour d'insa yana kallan news amma hankalinsa ba'a kan news yake ba, tunani yake a zuciyarsa in har ya amince da kud'irin Alh Jabir yayiwa yarsa ta cikinsa adalci? Hakk'insa ne ya zaba mata miji na gari me ilimi me hankali, tarbiya da kuma kammala, wanda AJ baya ko daya a ciki, a daya bangaren kuma, tunanin hallacin da Alh Jabir ya masa a rayuwa yakeyi, ya masa hallaci ba kad'an ba ya tuno Husnah zata iya zamo silar shiryiwar Ammar na har abada da wannan tunanin yayi making final decision akan ze aurawa Husnah AJ duk da yasan beyiwa yar tasa adalci ba kuma ya tabbata iyalansa bazasu yadda ba amma ba yadda iya fatansa dai Allah yasa Husnah ta zama silar shiryuwar Ammar.

Mama ce ta shigo, ganin kamar Abba na tunani tace " lafiya kuwa?" Abba yaja dogon numfashi " bakomai bakomai fa" Mama tace "okay tham" nan suka canza wata hirar zuwa wata daban.

*_London , 29 June, 7:00pm_*

Daidai lokacin jirgin Mummy, Bobo, da kuma AJ ya sauka a heathrow airport dake London, tafe suke suna jan trolley dinsu taxi ta daukesu suka wuce d'an madaidaicin gidansu da Daddy ya siya a London.

Bayan sun huta sunci abinci AJ ya shiga kiran abokansa nacan maza da mata kan karfe goma sun cika gidan sai ihu suke suna shewa, ba'a wani dade ba sukaja AJ zuwa club din da suka saba zuwa, Mummy na cikin dakin duk bata san wainar da'ake toyawa ba sai wajen k'arfe sha d'aya(11) ta fito ta tadda palour wayam, ta dau wayarta ta fara kiran wayar AJ ganin wayar akan dinning tana ringing yasa ta katse wayar tai tsaki ta shige daki.

**Husnah**
Husnah ce zaune akan kujerar mirror tana kwaliya kasancewa yau sunyi da Muhsin zezo, daidai lokacin data gama daura dankwalinta wayar ta tayi ringing ta dauka "Mi Amor ka shigo palourn yanzu Khalifa ze bude maka" yace okay my All" ta aje wayar ta dauki mayafinta tasa ta feshe jikinta da turare sannan ta fita lek'awa dakin Mama tayi tace " Mama naje Muhsin din ya iso" Mama tace "to ki gaisheshi" cike da kunya ta nufi palourn bakin.

Zaune ta taddashi a kan kujera cikin dakakiyar shadda ash da hula wadda ta karbi jikinsa ta kuma k'ara fito da kyawunsa, lokaci zuwa lokaci yana kai duba ga tsadaden agogo dake mak'ale a hannunshi, ganinta yasa ya dago ya washe baki ba k'aramin kyau ta masa ba abin da kara bashi farin ciki shine yasan duk dan shi tayi wannan kwaliyar, ya kalleta " gaskiya kinyi kyau ba kadan ba My All " tayi murmushi "kaji ka hakane kyau? Kazo lafiya?" "lafiya lau my All ya kowa da kowa ya su Mama? Ina Abba? Yau dai ya kamata na gabbatar da kaina a wajen Abba tunda ya nemi hakan" Husnah fuska d'auke da murmushi tace " gaskiya kam amma saidai bayanan amma insha Allah zuwa anjima ze dawo" yace " ba matsala sai na jira ai" nan suka shiga hirarsu ta soyayya, can dai wayar sa tayi k'ara, daga asibiti ne aka kirashi a nemanshi da gaggawa ze duba wani patient sam beso hakan ba amma ba yadda ya iya, cike da takaici sukai salama ba da san ransu ba ya tafi.

*1ST JULY*

Yau ta kama rannar birthday din AJ duk 'yan clique dinsu da sauran 'yan matansa sun hallara wanda duk a hotel suka sauka Bobo ne kawai a gidansu, tun safe suke shirye shirye, wani tangamemen cake me bala'in kyau wanda aka yishi kamar mota benz kalar black and white cake din yayi bala'in kyau ajiki ansa _HAPPY BIRTHDAY AJ_ wanda Mummy ce tasa aka masa kuma akudin mu na nan 9ja ak'la ze kai 50k, a wani shahararen club dake London suka hallara danyi celebration din AJ sanye yake cikin shiga ta alfarma kaf kayan jikinsa masu kyau ne da tsada babu na yarwa, a tare suka shigo cikin club din shida girlfrnd dinsa Pinky itama cikin shigar english wears d'amamu wanda dasu gaura babu, shigowarsu take wajen ya d'au ihu, ga kida na tashi kamar me, kwalaban giya da shisha dasu aka zagaye cake din, bayan d'an gabatarwa da Aliyu Lee yayi cikin harshen english itama pinky ta fito tai nata jawabin a matsayinta na gfrnd dinsa, baya nan ya rungumo ta suka yanka cake din wajen ya d'au tafi, sai kuma waje ya barke da rawa, bayan sun sha sun bugu rawa sukai tayi kamar ba gobe, shedancin da'akai a wajen nan ba'a magana, sai dai fatan Allah ya shirya, a takaice dai sai wajen tsakiya dare suka kamala birthday din nan suka dawo gida a bige. Mummy kuwa bata damu ba a cewar ta dan dai ranna daya yayi sha'aninsa wataran sai labari.

Washegari

Bayan giya ta saki AJ ya dawo normal, ya tuno ashefa Daddy dinsa be basa gift ba kuma ko text din birthday wishes be turo masa ba balle ya kirashi, cike da takaici ya kalli Mummy, " Mum kinsan Daddy fa be bani gift ba har yanzu? Ko dan birthday wishes babh, Me ya ke nufi baze ban ba kenan, kinsan fa ni so nake ya siyamin latest benz din nan data shigo 9ja," Mummy tayi dariya " ai ban tunanin ze siya fa, amma bari mu gani, daidai lokacin Daddy ya kira AJ, AJ ya dauka da shagwaba " Mr. Daddy nayi fushi fa, ba birthday wishes ba birthday gift, Daddy yayi murmushi " habadai Son aiki ne yamin yawa, amma ai gift din da zan baka ya wuce tunaninka, gift ne daba kowani uba ne ze iya bawa d'ansa ba" cike da zumudi AJ yace " Daddy kana nufin ka siya min Benz din?" Daddy yayi murmushi " wannan ai yafi karfin Benz, Son ka bude kunwanka kaji, cike da zumudi AJ yace "Tham am all ears"..

Hafcy.blogspot.com

MissHafcy at 13:54

ASMAUL~HUSNADonde viven las historias. Descúbrelo ahora