ASMA'UL~HUSNA
★★ *ASMA'UL~HUSNAH* ★★
© *MISS HAFCY*
® *NWA*0⃣5⃣
Daddy ne tare da iyalansa wato Mummy da AJ, tafe suke akan hanyarsu ta zuwa gidan Hajiya wato mahaifiyar Daddy kuma kaka a wajen AJ.
A hanya ne AJ ya kalli Daddy yace " Mr. Daddy birthday dina fa ya matso, ina buk'atar kudi kuma a London nake san yi kasan fa frnds dina nacan sunfi na nan yawa" Daddy ya juyo ya kalleshi " Lallai Ammar, wato yanzu kafi karfin kayi birthday a 9ja sai a London to ba London din da zaka je in bazakayi anan ba fine a hakura" Mummy tayi sauri tace " aaa kaga Alhaji ka barshi yayi wataran sai labari ,indai ace duk dukiyar daka tara danka baze ji dadinta ba to kuwa banga amfaninta ba, in bazaka biya masa ba to ni zan bada kudin duka nawa ne kudin?" Daddy yace "kwadai san yadda zakuyi amma ni bazan bada kudina ayi shed'ancin nan ba" au da duk baka san shedanci neba sai yanzu? Lallai kazo da Sabon salo" Ta kalli Ammar dake ta kumbure kumbure " Karka damu Babana zakayi birthday kaji ba London ba duk kasar dakake so zakayi acan dadinta dai mummynka nada kudi". AJ yai murmushi "thanks Mummy ur d best mum ever, i love u so much" i love you too Son, ta fad'a tana murmushi.
Tsohuwar mata ce zaune tayi zaman dirshen akan carpet tana kallo, da salama Daddy ya shigo palour ganinsu yasa ta washe baki " Ahhh kune tafe? To sannuku da zuwa sannunku da zuwa" Mummy ta amsa da yauwa Hajaju hakama Daddy , Aj kuwa zamayi akan kujera ya dau remote ya canza channel zuwa ta waka ya fara kalla, sai da suka gama gaisawa tsaf amma still ko kallan Hajiya beyi ba, Hajiya ta gaji tace " ni maigida yau ba gaisuwa ne?" Sorry fa ya kike ya hidimomi ya chilling" meye kuma chillin? Hajiya ta fada tana zaro ido " auuu na tuna fa ashe fa kece, ina wuni to?" Hajiya ta washe baki lafiya lau".
Daidai lokacin wata yar budurwa ta shigo dakin dagani bazata wuce shekara sha bakwai ba har kasa ta durkusa ta gaisheda Su Mummy sannan ta juyo ta kalli AJ da hankalinsa kacokan nakan video wakar dayake kalla " Yaya Ammar ina wuni?" Ya kare mata kallo yana tabe baki " ke kuma wacceee? Aina kika sani?" Hajiya tayi sauri tace " yar uwarka ce dai Fattun kauye" tab aikuwa sai dai kauyen kina fama yan mata" ya fada yana dariya, ita kuwa ta sunkuyar dakanta ta shige dakinta abinta, Daddy ya wurgawa AJ wani irin kallo " kai wato kowa ma baka kyale ba?, 'yar uwarka ce dai" Hajiya tace "nida ze yadda ma ai ta gida za'ayi tana gama makaranta sai a aura masa" wani wawan kallo ya wurgawa Hajiya "mtsew Allah ya kiyaye ace duk 'yan matana ace sai wannan yar kauyen zan aura karma ki soma wallahi kiji da tsofan ki malama" Hajiya tace "nima wasa nake maka d'an jikale" AJ ya tabe baki "gwanda da kikace wasan" bayan sun dan taba hira sukayi sallama suka dawo gida Aj nata kumbure- kumbure shi a dole wai am bata masa rai.
**Husnah**
Mama zaune da Husna a palour, dayake yau weekends ne Husnah na gida, Mama ta kalleta " nikuwa Husnah ya maganar da kukayi da Abbanki? Kin fito da mijin kokuwa?" Mama ai ba sai na tsaya wani fitar da mijiba Muhsin kadai nake kulawa yanzu kuma shi zan fitar a matsayin mijina," Mama tace " to yayi kyau Muhsin din dayake zuwa nan koh? Ko bashi ba?" Husnah ta tace " Mama kinada mantuwa, shine dai wannan fa Doctor din da muka hadu dashi a asibiti," Mama tace " kayya na sha'afa to Abdullahin fa?" Husnah tayi daria "dama ai ba sanshi nakeba kinsani kuma shi ya cika tsirfa yanzu gashi na samu wanda ya fishi" gaskiya ne to Allah ya sanya alheri ai dagani Muhsin din mutumin kirkine kuma ze rike ki amana, insha Allah zan fadawa Abban nasanki da kunya ba fada masa zaki iya yiba" Mama ta fada tana murmushi, Husnah tayi dariya " kamar kinsani kuwa, shiyasa uwa keda dadi Allah ya barmun ke Mamana" Mama tace " Ameen".
Khalifa ya shigo yana danna waya yana murmushi, Husnah ta kalleshi "bros sarkin Chatting wai kai k'arami dakai har wani chating kakeyi?" Yayi dariya " Yaya husna kenan, to duba kigani instagram ne" karbar wayar tayi ta duba account dinshi hotanta taga yasa yayi comment da " Ya Husna My Lovely sister" ta sha kunu "kai cire hotanan in ba hakaba muyi fada dakai, ko ni bansa hotona ba sai kai kasa" ya warce wayarsa yace " au haka zakice? to bari na cire" tayi dariya dayafi dai, shikuwa yasha kunu zaki san rashin Mutuncin danma kinsamu nasa pic d'inki " sannan ya shiga d'akinsa yana gunguni.
*Bayan kwana biyu*
Daddy ne zauna a makeken office dinsa ga tulun files a gabanshi amma ya kasa tabuka komai sai uban tagumi daya zabga, a hankali Malam Barau da Abba suka turo kofar office dinsu dan suzo suyi maganar akan wata kwangila da zasuyi, salama biyu sukai sai ata ukun ya amsa suka samu waje suka zauna, Malam Barau yace " Alhaji Jabir lafiyarka lau kuwa? Wannan tagumi daka zabga haka?" Daddy yaja dogon numfashi sannan yace " inada damuwa ne kuma duk akan wannan Yaron Ammar abin nasa na k'ara zama worst na rasa yadda zanmasa wallahi" Malam Barau yaja dogon numfashi " to in bazaka damu ba ga wata shawara" cike da zumudi Daddy ya matso " ina jinka Malam Barau!"
Www.hafcy.blogspot.comMissHafcy at 13:40
YOU ARE READING
ASMAUL~HUSNA
General Fiction#5 in general fiction 15/oct/2017 # 3 in destiny 6 sept 2018 Labari ne akan wata nutsatsiyar budurwa me ilim da tarbiya me suna Asmaul Husnah wadda ta tsinci kanta da auran wani takadirin matashi mara tarbiya wanda ya maida shashaye da sauran mugaye...