16_17

1.2K 46 0
                                    

☆☆ *ASMAUL_HUSNAH*☆☆
© *MISS_HAFCY*
*** Last post na manta bansa number din page din ba an sorry 14-15 ne***
1⃣6⃣_1⃣7⃣

10:30PM

Tana palour tana kallon photo album na bikinsu da'aka kawo d'azu, taji anyi knocking kofar a zaune tace "waye?" Muryar mace taji da sauri ta tashi ta bud'e, tsayawa tai tana kallon yar matashiyar budurwa wadda fuskarta har wani yellow take saboda tsbar bleaching, dake tsaye a bakin kofa sai wani cika take tana batsewa, bangajeta tayi ta shiga cikin palourn, Husnah ta juyo a fusace "baiwar Allah waceceke da zaki shigo cikin gidana ki bangajeni ki wuce? Ko salama babu?" ta juyo ta kalleta ta bushe da daria tana nuna Husnah tace " ke baki isa nai da ke ba wallahi kinyi kadan! Wajen mijinki nazo ba wajenki ba, Sakarya kawai!" Husnah na k'ok'arin magana AJ ya fito da sauri dan daga cikin d'aki yana juyo hayaniyar su.

A fusace yace " ke Pinky meya kawoki gidana?" Juyowar da zatai suka hada ido na tsawon minti biyu(2) tuni yaji duk ya sauya nan da nan ya wayance " my Pinky yaushe kika zo?" Husnah ta saki baki tana kallansu, pinky ta karasa wajensa cikin shwagba tace" ba wannan sakaran matar taka ce ta tsaya tana zagina ba," a fusace yace " ke meyasa zaki zageta? Ko bakisan matsayinta a guna bane?" Husnah data rik'e baki saboda mamaki tace "bansani ba, kuma dan na tambeyata shine ze zama abin zagi? Ya zaayi ta shigo min gida hadda bangajeni danna tambayeta daga inda ta fito ace zagine? Nidai sanina dakai baka da wata kanwa balle kuma wata matar bayan ni, to wannan d'in wacecce??" A fusace ya daga hannu ze wanka mata mari da sauri pinky ta dakatar dashi "Ahh no karka taba ta" " ai da kin barni na mareta in yaso seta gane wacece ke, to wannan da kike gani tafi min ke sau dubu, ko kin manta ni ba sanki nake ba? Hadani aure akai dake" tuni hawaye suka shiga kwanrayowa daga fuskar Husnah ta rasa bakin magana jin abin take kamar almara.

Pinky tai wata shu'umar dariya sannan tace " kaga my dear kar wannan kucakar ta bata ma rai cool down kaji nawan, kaga ni yanzu bacci nakeji wani d'aki ka tanadar min?" ya murmusa sannan yace " zab'i duk dakin daya miki kije ki kwanta my pinky dear" tai turo baki " ummm lemmi see waccan (ta nuna dakin dake kusa dana Husnah,) yai dariya " yauwa to muje ya dau jakarta d ya kai mata d'akin ta kalli dakin yai mata kyau " to ni bari na kwanat G. Nyt saura kuma kaje wajen waccar kucakar" ni na isa? Ya fada yana nuna kansa, tai dariya hade da cire dan yololon mayafin dake kanta, Sweet dreams dear ta fada tana murmushi "same" ya fada tare da ficewa daga dakin.

Husnah na tsaye kuka kawai take kamar me ya fito ya sameta ya daka mata " ke kukan me kike yi ne? Me aka miki?" Ta share hawayenta tace "Bakomai" to zaki wuce ne ko saina makeki tukun ba shiri ta wuce d'akinta tana kuka, a rannar dakayr tai bacci gashi ta kasa ko daga waya ta fadawa wani damuwarta ganin kukan ba inda ze kaita ta tashi tai alwala ta shiga jero salloli tana addua ahaka har bacci barowa ya saceta..

Washegari da safe bayan Pinky ta tashi tai wanka ta fito ita taje ta tashi AJ daga bacci da kyar ya tashi dan bacci ssai yake tiolet shima ya shiga ya watsa ruwa ya sa kaya ya fito palour, har a lokacin Husnah bata fito ba tun asuba ta tashi tana ta muraji'ar alkuani, Pinky ta kalli Aj " dear nifa yunwa nakeji dama haka take barin ka da yunwa har yanzu bata hada maba breakfast bafa?" Da sauri ya tashi " bari na tasota"

Da karfi ya tura kofar wanda yasa ta tsurata ainun, kan tai magana yace " ke me kikeyi da bazaki zo ki hada mana breakfast ba?" Ta juyo ta da mamaki ta kalleshi " ka manta bani nake girki ba daga gidanku ake kawowa?" Tsaki ya buga " to ni yau ke nakeso ki hada maza tashi" aje Al kur'anin tai a gefe ta tashi ta nufi kitchen jiki a sanyaye.

A falo ta tadda Pinky ta barraje akan kujera romote a hannunta tana canza channel " ke Babu manya a gidanku ne? Baki iya gausuwa ba?" Husnah ta kare nata kallo tabbas zata girmeta a shekaru amma dai sam bata da wani kwarjini da kima da ya kamata a agaisheta! amma gudun tashin hankali ta kalleta tace " an tashi lfy?' Da ban tashi lafiya ba zaki ganni anan bace min dagani karki batan rai! .

A daidai lokacin Eshale ta buga kofa da sauri Husnah ta bude har kasa Eshale ta gaisheda Husnah sannan ta wuce wajen dinning kafar pinky dake kan carpert ta taka tana sauri bata lura ba dan ita bata kawo da mutum a wajenba, wani k'ara Pinky ta saki dayasa AJ fitowa ba shiri " My Pinky meya faru? Ba karamin mamaki Eshale tai ba ganin wata mace bayan Husnah a gidan har AJ na kiranta da My, fuskarta karara ta nuna tai mamaki tana shirin bata hakuri Pinky ta dago ta maketa s ta bugu da Bango tuni jini yafara ambulowa ta bakinta harda hanci, Eshale ta fasa wani k'ara Shikuwa kallan Pinky yai "kin min daidai dama ni na tsani yarinyar sam bata da kunya" Husnah da sauri ta yo wajen Eshale ta tallofa tana mata sannu, da sauri ta dauko tissue ta shiga goge mata bakin tana mata sannu Eshale tana kuka ta tashi ta gyra hijab dinta ta na kokarin tafiya Husna ta dakatar da ita " ki tsaya mana a akai ki asibiti!" Kallanta yai ya watsa mata harara kana yace " waze kaita asibitin? zaki barta ta tafi ko kema sai na miki irin tatan?" Husnah ta saketa tana mata sannu har se data fita tana rusa kuka abinta...

Har gudu take taje gida ta sanarwa Mummy ,ita ba buguwar ne ya dameta ba ala aka take taje ta sanarwar Mummy labarin matar nan data gani har ta ji mata ciwo , tana isa ta rushe da kuka sosaii Mummy ta rikece tana mata tambayoyi ajere a jere "waya fasa miki baki? Ince dai ba Babbana bane?" Bashi bane Mummy dama Ya Ammar matansa biyu?" Mummy tace kamar yaya? Tuni Eshale ta labarta mata komai Mummy bata san sanda ta yarda spoon din dake hannunta ba a razane tace " WHAT???!!!!
KU biyoni
《Hafcici》

ASMAUL~HUSNAWhere stories live. Discover now