ASMA'UL HUSNA 8

2K 76 4
                                    

☆☆ *ASMA'UL_HUSNAH* ☆☆
       © *MISS_HAFCY*
        ® *NWA*
                    0⃣8⃣
     *I dedicate this page to Zarah Bukar and Sweet Surry thanks for d love and care ILYSM❤*

    Cikin mamaki tace "wannan wacca magana ce da tafi karfin ayita a waya? Eh? Jin shiru yayi yawa yasa ta sako da wayar daga kan kunne ta sai a lokacin ta lura da ya dade da kashe wayar, wani dogon tsaki taja cike da takaici, nan ta shiga kwalawa Ammar kira amma shiru hakan yasa tayi dailing numbersa danji inda yake, bugu biyu ya d'auka kan yayi magana tace " dadyna kana ina ne?" Kai tsaye ya amsa mata " mun fita dasu Bobo ya akai?" Cikin nutsuwa tace "to kayi saurin ka dawo kana jina? Gobe insha Allah zamu koma gida" kan yayi magana ta katse wayar a zuciyatarta tace "inaga fa maganar auren Ammar zemin oho dai indai kan maganar ne to nidai ban bada goyon bayana ba yasan yada ya karke shi daya" da haka ta tabe baki ta shiga daki.

     "Nifa Abba wannan hukuncin daka yanke sam bemin ba, be kamata ace kamar kai kayiwa yarka auren dole ba" Mama ce ke wannan maganar idanta nakan Abba dake ta karanta newspaper hankalinsa kwance, ya nade newspaper din ya aje akan center table din dake gabansa sannan ya kalli Mama yace " abinda nakesan ki fahimta shine wannan hukuncin dana yanke bawai kai tsaye na yanke shi ba sai danai tunani, kuma abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala baze hango ba, dan haka dan Allah ina rokonki daki aje wannan maganar gefe kisawa auren nan albarka mudai a koda yaushe alheri muke nema kuma ina ji a jikina wannan auren alheri ne, mu cigaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi alheri" Mama tayi jim na d'an lokaci sannan tace "na fahimceka Allah ya zaba mafi alheri"  cike da jindadi Abba yace Ameen sannan suka cigaba da hira.

      A washegari  jirgin su Mama ya diro Nijeria, bayan sun huta da daddare Daddy ya tari Mama da zancen auren Ammar kai tsaye ta nuna rashin amincewarta shikuwa ya jadada mata cewa ya riga ya yanke hukunci babu gudu babu ja da baya, ba yadda batai ba amma Daddy yak'i ji hakan yasa itama ta sauko har ta amince mussaman jin da Husnah zaa had'a d'an nata  ita dai a sanin data mata yarinya ce me hankali da nutsuwa kuma Husnah ns burgeta matsalar dai daya Ammar shine tasan ze kawo matsala amma taci alwashin zatai dabara ta shawo kansa har shima ya amince ya fara santa, fatan ta dai Allah yasa ta zamo silar shiryuwarsa, shikuwa Ammar duk besan wainar da'ake toyawa ba dan shi a zatansa duk wasa Daddy yake masa yama manta da zancen harkar gabansa kawai yake.

    Bayan 1weeek da dawowarsu daga London aka yi komai aka sa rannar auren Ammar da Husnah wata biyu masu zuwa, duk ba da sanin Ammar ba, itakam Mummy ta saki jikinta ta kuma bada goyon baya d'ari bisa d'ari dan yanzu ganin take tafi kowa matsuwa ayi auren.

     Husnah na zaune duk abin duniya ya isheta damuwarta d'aya yadda zata fadawa Muhsin cewa Abba ya riga ya  zaba mata miji har ankai ga sa rannar biki, tana cikin wannan tunanin ne wayarta tai ringing da mamakinta Muhsin ne, sai da wayar ta kusan tsinkewa sannan ta dauka, muryar Muhsin taji yana cewa yana kofar gida gabanta ya fadi tasan wannan ce rannar da zata fada masa cewa ansa rannar bikinta wannan ce rannar data dade tana addu'ar kar tazo wato rannar rabuwarta da Muhsin, wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo a kyakyawar fuskarta, ta goge fuskarta ta dan yi light makeup sannan tasa hijab ko Mama bata fadawa ba ta fita.

   Motarsa ta hango a gefe gidansu a hankali ta k'arasa ta kwankwasa ya bude  ta shiga, kallo daya ya mata yasan akwai abinda ke damunta ya kalleta na 'yan sec sannan yace "are u alright?" Yes im fine" noo ki fada min gaskiya meke damunki?" Ta kalleshi sai kuma ta fashe da kuka, sosaii hankalinsa ya tashi ganin tana kuka har haka shi dai tun dayake da ita be taba ganin tana kuka har haka ba, yasan kuwa ba karamin abu ne ya faru ba" cike da tashin hankali yake tambayarta meke faruwa" dakayr ta saita kanta sannan tace " im sorry niban san ma ta inda zan fara ba, duk yadda zanyi naga cewa Abba ya fahimce ni nayi buh still ban samu nasara baAbba yamin miji har ansa rannar aurena nan da wata biyu!"

       Tamkar saukar aradu haka yaji maganar a zuciyarsa "innalalahi kawai yake maimaita " kina nufin yanzu na rasaki, kina nufin yanzu bazan aureki ba? dis cant be possible!   lets be serious da gaske kike ko wasa?" " wallahi da gaske nake,!" Innalahi waina ilaihi rajun! Ya fada hade da dafe kansa yayi shiru na d'an lokaci sannan yace "nikuma kaddarata kenan? Husnah bake ce farau ba, ba akanki aka fara min haka ba hakan tasha faruwa dani,  i dunno why inaga nikuma k'addara ta kenan haka Allah ya tsara min, dole na yadda da hukunci ubangiji doleh na yadda da k'addara a matsyina na musulimi  Husnah kije kibi zabin iyayenki kada ko kadan ki yadda rudin shedan yaja ki har kice zaki bijirewa maganar iyayenki a ganina zabin iyaye shine daidai, domin da hankalinsu bazasu zaba miki wanda suka san ze cuce kiba, Husnah mu musulmai ne dole mu yadda da k'addara, inaso kiyi hakuri kije Allah ya baku zaman lafiya, ni kuma ina rokon ki dan Allah ki tayani da addu'a Allah ya cire min sanki a zuciyata ya kuma bani mace irinki sak bazance wadda tafiki domin a wajena kinfi ko wacca komai a wajena...

    Ya sauke ajiyar zuciya muryarsa na rawa sannan ya cigaba, har ina murna na samu mace ta gari wadda na dade ina addu'ar samu ashe Allah be kaddara zaki zamo tawa ta har abada, ina baki shawara da kiyiwa mijinki biyayya karko kadan sona yasa kiki mai biyaya in kikai hakan zan iya cewa kinci amanata! Allah ya baku zaman lafiya, ya karasa maganar hade da share hawayen dake fuskarsa, Husnah dake ta kuka kamar me ta dago jajayen idanunta ta kalleshi " yanzu shikenan mun rabu kenan...???" Mun rabu kenan Husnah!" Hawayen dake kokarin fitowa yayi sauri ya share sannan ya tada key din motarsa hakan yasa ta bude murfin motar a hankali ta fita tana kuka dan tama kasa magana, shikuwa yaja motarsa yayi gaba ta tsaya tana ta kurawa motar ido har sai data dena hango motar  sannan ta juya da gudu tana kuka ta shige gida.
       Rabuwa da masoyi...................
      Hafcy.blogspot.com

ASMAUL~HUSNADonde viven las historias. Descúbrelo ahora