*ASMAUL_HUSNAH*
*©MISS_HAFCY*
*NWA*
*DEDICATED TO BESTY HOUSNER*2⃣0⃣_2⃣5⃣
"Nima nasan da hakan Buhari, nagode sosaii" Bobo yace " babu komai ana tare yanzu dai mu tayashi da addu'a nima rannar fa daga na tambyeshi ya Husnah ya fara balbaleni da masifa abin nasa ya fara ban tsoro" Mummy tace " nikaina Allah de kawo karshen abun,ya raba shi da wannan tsinaniyar yarinyar amma dole nai abu akan wannan abu bazan tsaya na zuba musu ido ba! Bobo yace "Ameen Mummy ai abin se addu'a, gaskiya kam ya kamata ai abu akai". Nan suka cigaba da hira akan maganar daga baya yace ze tafi Mummy ta ciro kudi ta mika masa " Gashi nan Buhari amma dan Allah kayi amfani dashi ta hanya me kyau! Kar kaje ka sai kayan maye dasu badan haka na baka ba" Insha Allah Mummy nagode sosaii ya fada yana sosa keya.
Washegari.
Husnah a dakin da'a sauketa zaune tana karanta Alkur'ani bayan ta idar ta rufe ta aje gefe ta kunna Tv din dake makale abango d'akin takai Sunnah TV, Sheik Dr. Isah Ali Fantami ne ke wa'azi ta zauna tana saurare tana jin dad'in wa'azin bayan ya gama ne aka masa tambaya akan yadda za'a warware sihiri da ayar Allah ba tare da wani boka ko malam ba, daidai lokacin dq Mummy ta shigo dakin kenan dan ta kirata suzo su gaisa da Daddy ya dawo, taji, itama zama tai tana jin ya fara da cewa
" Na farko dai
1) A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a nika a zuba cikin ruwan.2) Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan.
3) Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).
4) Sai a karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.
5) Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.
6) Suratul Kafirun kafa daya
7) Falaki da Nasi kafa uku- uku.
8) Sai a karanta wannan addu'a
"Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi wa antash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakaman" kafa uku.9) Sannan za'a iya karawa da wannan addu'a "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika" kafa uku
Insha Allahu ta'ala idan aka karanta wadannan, kuma Mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi. Basai mutum yaje wajen boka an danfare shi ba. Sannan kuma basai an maka/ miki sihiri ba, mutum zai iya yi domin tsima jikin sa daga shairin masharranta. Wahlahu a'alam".
Mummy tace " kai amma Allah ya sakawa malam da alheri, kinga sai muyi amfani da wannan hanyar kai amma naji dadi" Husnah tai murmushi " Ameen gashi dama nai recording" Mummy tace " to kinga hakuri zakiyi ki koma gidan dan ke zakiyi dibara ki dinga bashi ruwan maganin yana sha bari na aika a sisiyo abubuwa" Husnah tace " bakomai Mummy anjima sai na koma" Mummy tace "yauwa Allah ya shi miki albarka ya ta gari, gaskiya iyayenki sunyi dace, na dade banga 'ya me halayya irin taki ba, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya" tai murmushi "Ameen mumy".
Da kanta ta hada maganin, ta zuba gayen magaryar ta tofa duk ayoyin da sauran addu'oi kamaar yadda Malam yace sannan ta aje gorar ruwa a gefe.
Bayan Magrib Husnah ta koma gidan da gorar maganin gidan duk yai kaca-kaca da taimakom Eshale da Mummy ta hadata da ita ta tayata aiki suka samu suka gyra gidan tsaf sannan sukaci abincin da suka taho dashi Eshale ta koma.
Sai wajen Bayan isha Ammar ya dawo amma shikadai ya dawo ba tare da Pinky ba hakan yasa Husnah tai zatan ko ta tafi dan taje ta duba dakunan babu akwatinta watakila ta gaji ta tafi kuma, Yana kallan Husnah ta watsa mata harara " ke wai wacca irin jarababiya ce? Waya dawo dake kuma? Ai na zata kin tafi kenan" murmushi tayi " Ai nan ne yafi dacewa dani na zauna domin nane gidan aurena kuma kar ka manta har yanzu da igiyar aurenka a kaina taya kuma zanje wani waje na zauna bayan ga gidan mijina?" wani tsaki yaja sannan yace " kedai kika sani, ni wallahi an cuceni kawai an hadani da wata wadda bana santa, bana kaunarta, ya zama dole na auri Pinky kwanan dan itace ta dace dani ba wannan kucakar ba!" Yana gama fadin hakan ya shige dakinsa, Husnah tai murmushi takaici a daidai lokacin datake share siraren hawayen da suka zubo mata a fuska, duk laifin Abba ne daya barta ta auri wanda takeso tun farko da bata shiga cikin wannan halin ba!" Abinda ta fada keman a zuciyarta sannan ta dau Goron ruwan maganin ta dauka tasa fridge.
Daga daki ta jiyo muryar Ammar yana kwala mata kira ba shiri ta shiga " Gani Ya Ammar" ya watsa mata wani kalo " oya jeki hadamin ruwan wanka naga babu a ruwan zafi a heater ki tafasa min a kettle ki kawo min sannan ki kawo min ruwa nasha," Jiki a sanyaye ta je kitchen ta dora masa ruwan sannan ta zuba masa ruwa a cup sai data bude fridge ta tuna da maganin aikuwa ta zuba masa shi ta kai masa be lura ba saboda da alama kishi yakeji nan da nan ya kwankwade ya aje glass cup din a gefe. A ruwan wankan ma sai data sa masa maganin ta kuma yayafa a dakin da koina na gidan bayan ya shiga wanka sannan ta dawo dakinta tana addu'a.
Washegari da safe ma haka tayi shi tasa masa a ruwan wanka ta kuma sa mai a ruwan sha data kawo masa, yai wanka ya fice bayan ya cika cikinsa.
Da yamma kuwa su Mama sukazo unexpected ba karamin dadi Husnah taji ba hadda su Nana aka zo Mama tace ina fatan dai ba wata matsala naga kamar kin rame fa" Husnah tai murmushi " babu mama kawai dai missing dinku ne yasani rama" Mama tai murmushi " zaki saba ne ai, ki dena sa wannan a rai kinji?" husnah tace to Mamana", sun dan jima dagabaya suka tafi bayan Mama tayiwa Husnah nasiha sosai akan aure, da sunzo su jira Ammar amma daga baya suka tafi, Husnah tasha kuka da zasu tafi dakyar ta samu ta dena kuka.
Haka rayuwa ta cigaba wasa-wasa har anyi sati, wani sain Pinky ta kwana a gidan wani sain ta kwana a wani waje.
A gabaanta suke soyewa abinsu duk da ta lura soyayya suke basa kusantar junansu amma wasu abubuwan da suke sam be dace ba be kamata ba tunda ba aurenta yake ba, wani sain agabanta zasu dinga ba juna abinci a baki suna wasa da dariya abinsu tun tana damuwa har ta dena, ta koma kamar wata me aiki sai dai ta gyra gida ta dafa ta sauke su ci wani sa in suka fita sai tsakiyar dare su dawo. Bobo kuwa tunda ya mai magana akan Pinky ya hau gaba dashi zagi da gori ba irin wanda Bobo besha sha ba ganin abin yafi karfinsa yasa yaja gefe.Wata rana Husnah na k'okarin shigowa palour suka ci karo da Pinky a fusace pinky ta dago zata wanka mata Husnah ta rike hannunta " kar ki sake ki mareni! Shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ne, sakarya wawiya kawai" Pinky bata ce mata komai ba taje ta sanar da Ammar tana kukan munafinci, yazo ya balbale Husna da masifa, tasha zagi da gori kala-kala dagabaya yace ta tattara ta bar mai gida, tana kuka bata san inda zata nufa ba har ta yanke shawarar komawa gida kuma se ta fasa domin sam batasan hankalin Mama ya tashi tasanta da hawan jini ga kuma sa abu a rai, shiyasa duk abinda yake faruwa bata sanar da ita ba bata kuma sanar da kowa daga danginta ba, dan bata san abun yai tsamari tunda ta riga ta aureshi komai ya wuce zata juri duk wani k'alubale da zata fuskanta tasani Allah yana tare da ita kuma komai yai farko zeyi k'arshe ta tabbata akwai rannar da itama zata sami kwanciyar hankali da mijinta a gidan mijinta, dagabayane ta yanke shawara ta tafi gidan Mummy dayake ba nisa sosai nan da nan ta isa ta mata bayanin komai, Mummy sam bata ji dad'i ba itama abun ya fara damunta daga karshe dai ta ta bata hakuri sosai ta kuma ji dadi da bataje gidansu ba tazo nan wajenta.
Haka Husnah ta zauna gidan Mummy har na tsawon kwanana Biyu babu Ammar babu dalilinsa babu waya balle sak'o sam Husnah bata wani damu ba illa addu'a datake tayi kulllum.
Suna zaune itada Mummy sukaji shigowar Ammar kamar a mahafrki sunyi mamaki sosaii Mummy tai karaf tace " Yau kuma kaine a gidan?" " Nine Mummyna" ya fad"a yana sosaa k'eya, sosaii Mummy taji d'adi ta tabbata addu'arsu kuma abinda sukai yayi aiki cikin ikon Allah domin kuwa dagani asirin Pinky ya bar jikin Ammar. Ya k'araso ya zauna ya dukar da kai " Mummy dan Allah ki yafe min duk abinda na miki na baya har zuwa yanzu" " Mummy tayi Jim ba komai d'ana nima ai da laifina kuma na gane kuskurena, amma ina ka baro Pinkyn taka? (ta fada dan bugar cikinsa) wani tsaki yaja " Mummy Pinky shedaniya ce wallahi duk abinda nake yi a kwanakin duk sa hannunta ne da kunne naji tana waya tana fad'a har tana ikirarin zata iya kasheni a duk sanda ta nuna buk'atar ta ta kudi na hanata ta kwashe kudi wai taga alamu akwai kud"i a gidan tun dana ji wannan jikina yai sanyi na dawo hayyacina karshe dai da 'yan sanda na hadata na musu bayyanin komai nakuma ce su tsare ta har sai ta shiga taitayinta, yanzu bani ba ita kuma bazan taba yafe mata ba! " Mummy tace tirkashi! Allah mun gode maka Allah ya k'ara kiyaye gaba, nagodewa Allah daya kawo min wannan lokaci Alhamdulilah" Amin yace kansa a kasa sannan yace " Mummy dan Allah ki tayani neman gafara wajen Dady kan ya dawo da kuma ita" Mummy tace ita wa" Husnah" ya fada yana kalan Mummy tace " au ai gaka gata sai ka nema da kanka bari ma na tashi na baku wuri" take ta tashi ta nufi dakinta.
Sai dayayi shiru na 'yan Mintina sannan ya kalleta yace " Husnah nasani na miki laifi tun kafin aurenmu har zuwa yanzu dan Allah ina neman yafiyarki," Husnah tai murmushi " bakomai zan yafe maka amma sai da sharadi daya" Name nene? nikuma indai befi kargina na zan miki shi!
《Hafsisi》
Www.wattpad/Miss_Hapsy.com
YOU ARE READING
ASMAUL~HUSNA
General Fiction#5 in general fiction 15/oct/2017 # 3 in destiny 6 sept 2018 Labari ne akan wata nutsatsiyar budurwa me ilim da tarbiya me suna Asmaul Husnah wadda ta tsinci kanta da auran wani takadirin matashi mara tarbiya wanda ya maida shashaye da sauran mugaye...