7

2.1K 73 2
                                    

★★ *ASMA'UL~HUSNAH*★★
© *MISS HAFCY*
© *NWA*

*DEDICATED TO BESTY HUSNAH*

0⃣7⃣

Daddy yace " to mata na maka!" Da sauri kamar yana kallansa ya zaro ido " Wat??! Mata kuma?, which kind mata? Yayi dariya irinta kokontan nan" Daddy ya sha kunu kamar AJ na kallansa sannan yace " Ina maka wasa ne? Koni sa'an kane? I mean what i say na maka mata ko kanaso ko ba baka so kuma sai ka aureta" kit ya kashe wayar ya bar AJ da dafe kai, juyowa yayi ya kalli Mummy da itama mamaki ya hanata magana dan dagajin yadda AJ yace what cike da razana tasan akwai matsala ta kalleshi sannan tace" me yake fad'a maka ne? Ina fatan dai lafiya" AJ yace " kiji wai yamin Mata, wayace masa aure nakeso, kamar ni din nan har sai an wani zaba min mata, Lallai za'ayi ruwa da kankara dan wallahi bazan yadda ba," Mummy tayi tsaki " kaga kar ka tada hankalinka ka barni dashi, wannan ai ba mai yiwuwa bane, tukuna ma wacca mata yayi maka??"oho masa nidai koma waccece bazan yadda ba cuz ban shirya yin aure yanzu ba kuma koma na shirya sai na zab'i wadda nakeso tukuna, tun wuri ma ki fadamasa dan ni in na fada ba maganata zeji ba yanzu". Mummy ta jinjina kai sannan tace "kaga ka dena maganar nan ma please, raina b'aci yake, dan Allah ka dena damuwa karma kasa wannan a ranka kasan dai bazan taba bari a aura ma matar dabaka so ba, dan haka kar ka wasu damu Son ka manta da maganar ma" cike da rashin gamsuwa ya amsa da "toh" haka Mummy ta zauna tayi ta kwantar masa da hankali har ya manta da zancen ya shiga harkokin gabansa shida shedanin abokin nasa Bobo.

☆☆☆☆
Abba ne zaune yana karatun news can kamar ya tuno wani abu ya kwalawa Khalifa kira, dayake yana kusa nan da nan ya amsa yazo ya rusuna a gaban Abba, Abba ya kalleshi " jeka kirawo min yayarka maza" Khalifa yace to sannan ya tashi ya nufi d'akin Husnah.

Husnah na zaune tana karatu Khalifa ya shigo, beyi wata-wata ba ya isar da sak'on Abbah jin hakan yasa Husnah ta had'e kan textbooks din waje daya ta dauko mayafin abayar dake jikinta ta nufi palourn Abba.

Zaune ta tadda shi har k'asa ta tsuguna sannan tace "Abba gani" yayi gyran murya bayan 'yan mintuna yace " Husnah ina so na ki bani hankalinki wajen daya domin wannan maganar da zan fada miki tana bukatar nutsuwarki dan magana ce me muhimaci" Husnah tace " ina jinka Abba", Husnah inaso na sanar dake cewa na miki miji! (Dum! Gaban Husnah ya fad'i) Abba ya cigaba " kuma ba kowa bane illa Ammar dan gidan Alhaji Jabir na tabbata kinsan shi" Da sauri Husnah ta d'ago ta kalli Abba cikin muryar inda inda tace " Ab...bbaa to Muhsin fa? Shine fa wanda nakeso" Abba ya sake gyran murya " ni na riga na zartar da hukunci Husnah, dan haka ni bansan wani Muhsin ba, Ammar na zaba miki matsayin miji kuma a matsayina na mahaifinki doleh ne kimin biyaya ko kuma ki halaka ke kanki kinsan illolin sab'awa iyaye no need na sake fada miki".

Kuka ne kubce mata a daidai lokacin datake k'ok'arin yin magana hakan yasa muryarta ta sarke tama kasa magana, Ya Usman dake kokarin shigowa palour yajiyo kukan Husnah da sauri ya shigo ganin dan ganewa idansa abinda yasa k'anwar tasa kuka, abin ya d'aure masa kai ganin agaban Abba take kukan kuma be dau wani ya mataki ba da sauri ya k'araso ya zauna a kujera me kallan ta Abba, mamaki fal a cikinsa dan alamu sun nuna k'arara a fuskarsa a hankali ya kalli Abba yace " Abba barka da dare, ya kai dubansa ga Husnah dake kan carpert tana sharar kuka yace " Husy meya faru? Bakida lafiya ne? Abba me aka mata" ya jefa tamboyin a tare.

Husnah ta kasa magana sai kuka take abinta, Abba kuwa ya kalleshi yayi d'an murmushi irin na manya sannan yace " kagamin ita daga na fada mata cewa na bada aurenta ga Ammar dan gidan Alhaji Jabir shine take ta kuka, kamar wadda nace zan aurawa dodo" Ya Usman ya zaro ido sannan yace " Abba Ammar fa kace? AJ yaron dako abota bazan so k'ulawa dashi saboda munanan halayensa shi kake k'okarin aurawa yarka kuma k'anwata? Lallai Abba bakasan waye AJ ba, ai doleh tayi kuka dan gaskiya abinda kake kokarin yin ba adalci sam a ciki, kuma Abba tanada wanda takeso Muhsin yaro me mutunci da kamala, kusan sau uku yana zuwa ganinka kuna sab'ani dashi dan yanaso ya gabatar da kansa a wajenka, kuma kasani dan ina yawan ma zancensa, Abba dan Allah ka aje maganar wani AJ a gefe ka aurawa yarinyar nan Muhsin dan shine wanda takeso yake santa" Abba ya kalleshi a fusace " kai waya saka a cikin wannan maganar? banasan zancen banza, shi Muhsin din dakake magana tabbas ka tab'a min maganar shi nasani, amma yaron is nt serious inda har ya dau zancen da muhimanci kuma yana san aurenta ai da tuni yayi yadda yayi dan ganin ya gabatar da kansa wajena, amma ya kasa, yayi sake dan ni na riga na zab'a mata mijin dazata aura, kuma abinda babba ya hango yaro ko ya hau kan dutsen Dala baze hango ba, mu mun san dalilin daya sa muke san had'a auren nan, mun riga munyi maganar da Alh. Jabir kuma a matsayina na babban mutum wanda yake ganin girmana nake ganin nasa bazanso nayi magana sannan na canzata ba, aure kam sai anyishi da yardar Allah ku tashi kuban wuri" simi- simi Ya Usman ya tashi yabar falon yana gunguni, da sauri itama Husnah ta tashi tabi bayansa tana kuka bata zame koina ba sai d'akin Mama.

Mama na zaune tana sa gogagun kayanta a cikin wardrobe taji shigowar Husnah tana sheshek'ar kuka hakan yasa hankalinta ya dungunzuma ya tashi ta tashi da sauri ta talafo ta " Husnah meya faru? Bakida lafiya ne?" Shiru Husnah batai magana sai daga baya tace " Abba ne waii.." wai me ? Me yafaru ne wai? Mama ta tambaya cike da k'aguwa, Ya Usman ne ya shigo yana gunguni ya kalli Mama " yanzu dan Allah fisabililah Abba yayiwa Husnah adalci? Mama kisa baki mana" Mama cikin rashin fahimta tace " kai ni kun sani a duhu wai meya faru ne? " Ya Usman ya had'e yace " wai abba ne ze aurawa Husnah AJ Ammar dan gidan Baba Jabir wai harma sun gama maganar da Baba Jabir din, kuma shi wai baze canza magana ba na fada masa cewa tanada wanda takeso, kuma AJ ba mutumin kirki bane buh still yak'i yadda " Mama ta juyo da sauri ta kalli Ya Usman "Usman to ya zanyi? Jiya nan muka gama zancen dashi na nuna masa rashin goyon bayana k'arara amma sam yak'i yadda sai ma jadada min dayake shi ya gama magana aure sai anyi shi, karkaso kaga yadda nai ta shawo kansa amma yaki, yanzu sai dai muyita addu'a Allah ya zab'a mafi alheri inaga itace kadai mafita" Ya Usman yayi shiru kamar yana tunanin wani abu sanan yace " Mama to ki fadawa Kawu Yusuf(yayan Abba) yayiwa Abba magana na tabbata zeji zancensa" Mama ta d'an jinjina kai sannan tace " ka kawo shawara kuwa zan masa magana insha Allah" ta kalli Husnah " kinga Husnah ki kwanatar da hankalinki ki dena kuka, zan same shi na masa maganar da yardar Allah baza'a hada auren nan ba kiyi shiru ki dena damuwa kinji" Husnah ta d'an share hawayenta ta amsa da toh da kyar Mama ta lalashe ta har ta dena kuka, tashi tayi tai alwala tai sallah daga nan bacci me nauyi ya kwasheta.

☆☆ AJ ☆☆
AJ ne zaune da Mummy a palour suna hira, AJ yace " Mummy nifa kinsan me? Har yanzu hankalina ya kasa kwanciya da abinda Mr. Daddy yace kinsan shi fa maybe fa da gaske yake" Mummy tayi wata daria " Son wai bana ce ka dena zancen nan ba in da gske yake meyasa ni be tareni da zancen ba? Kuma kai kanka kasan indai ina raye bazan bari hakan ta faru ba, ka dena damuwa kaji," Daidai lokacin wayarta tai k'ara ta duba Daddy ne, shikuwa AJ ya fice daga palourn, cike da isa ta dauki wayar ta kara a kunne tare dacewa "hello" Daddy ya amsa sannan yace " wai yaushe zaku dawo ne?" Mummy ta dan tab'e baki kamar yana kallanta sannan tace "next week meyasa kake tambaya? " Abba yace " saboda matsayinki matata, kuma kin ketare iya kwanakin dana baki, bayan kince min befi kuyi 4days ba sai gashi har kunyi 1week kunasan kara wani, tsakani da Allah kin yiwa kanki adalci? To ina umartarki duk abinda kuke ku bari na baku gobe zuwa jibi ku dawo kinaji na? Kuma akwai wata muhimiyar magana dana kesan yi dake" Mummy tai sauri tace " to naji Allah ya kaimu, zamu dawo , amma wacca irin magana ce wannan data fi karfin ayita a waya?"
Hafcy.blogspot.com

******
Am sorry kunjini kwana 2 shiru hakan ya faru ne saboda rashin lafiya danayi amma yanzu Alhamdulilah naji sauki sosai, ina godia da kularwaku da addu'oinku i really appreciate Allah ya bar zumunci , and inason baku hakuri ba kullum zakuna jina ba saboda skul yanzu ba kullum nake samun enough tym da zanyi typing ba, ina fatan zaku cigaba da bibiyar littafin, i love you all❤.

ASMAUL~HUSNAWhere stories live. Discover now