18_19

1.2K 46 0
                                    

☆☆ *ASMAUL_HUSNAH* ☆☆
© *MISS_HAFCY*
*NWA*
1⃣8⃣- 1⃣9⃣

Eshale tace "Wallahi Mummy da dagaske nake" Mummy da ta gama rikicewa ta kalli Eshale " Dank'ari! To kinga maza turo min driver ya kaiki chemist ni kuma ya kaini gidan naga meke faruwa. Daki ta shiga ta dauko mayafinta ta fito palour dan Daddy da sassafe ya fita wata tafiya data sameshi da gaggawa bale ta fad'a masa.

A kofa ta tsaya jin muryar AJ data pinky sunata yiwa Husnah bala'i duk da bataji meta musu ba, tura kofar tai ta shigo a fusace Husna naganinta ta fashe da wani kuka taje wajenta " Mummy dan Allah ki maidani gidanmu bazan iya ba banzan iya ba wallahi" Mummy ta kalli Pinky sama da kasa tace " ke kuma wacecce da zaki shigo gidan yarinya ki nemi ki ci mata mutunci? " wata shu'umar dariya Pinky tai sannan tace " ke kuma wacecce ke? Da har kike da ikon Nunani da hannu" AJ kam ya kasa cewa komai sai kallan Mummy dayake yana mata alama da tai shiru, Mummy a fusace tace " Uwaki ce! Nace uwaki ce mara kunyar yarinya kawai, Dadyna wannan d'in wacecce? Meye matsayinta a wajenka? ina ka samo wannan yar barikin?" Pinky ta dakawa Mummy tsawa " ke dattijuwa ki rike girmanki in ba so kike nida d'an naki mu ci miki mutunci yanzu nan ba" Mummy a fusace ta d'aga hannu da wankawa Pinky mari sai data ga taurari.


Pinky ta fashe da kuka ta nuna AJ "kana kana kallo ta mareni koh?" Mummy tace "an mareki! "Sai a lokacin AJ yace Mummy dan Allah kiyi h'akuri kije ki tafi please, Mummy ta saki baki ta kasa magana " ni kake cewa na tafi? Anya kana cikin hayacinka kuwa?" Shiru yai kamar wani sakarai yana kallanta.

Mummy ta shiga wani yanayi in banda gumi ba abinda takeyi duk da sanyin Ac na palourn ta kalli Husnah daketa kuka tace " jeki hado kayanki mu tafo gida, dan hankalina baze tab'a kwanciya ba nabarki a gidanan, in ya dawo hayacinsa na tabbata da kansa zezo ya nemeki".

Cikin hanzari ta shiga ta dauko akwatinta data jida kayanta dan dama ba'a lawo lefenta ba su ta hada wanda zasu isheta tasa kan a kawo lefe ta fito Mummya tja hannunta suka fice a fusace.

Husnah se kuka take har suka shiga mota Mummy bata hanata ba dan ita kanta ji take kamar ta fashe da kuka duk nadama tabi ta isheta
" Laifi nane daban tsaya na yiwa yaran nan tarbiya ingantaciya ba, laifina ne daban dora shi akan turba me kyau ba, Laifina ne dan kasa gyra masa laifufunka tun kan ya kai haka, gashi nan yanzu dalilin haka rayuwarsa tana cikin hatsari, nida aganina shwagwaba yaro shine gata ashe wannan ba gata bace, bawa yaro tarbiya ingantaciya itace babbar gata, Allah na tuba Allah ka shirya Ammar" duk wannan maganganun a zuciyarta take fuskarar d'auke da damuwa, haka har suka iso gidan.

Bayan sun isa gida, Mummy takai Husnah wani d'an maidaidaicin daki da tiolet a ciki inda zata sauka, ta aje akwatunta jiki a sanyaye ta zauna a gefen gadon Mummy ta kalleta cike da tausayawa tace " yi hak'uri 'yata kinji insha Allah komai ze dawo daidai ki dena damuwa kinji? Ki saki jikin ki, yanzu nikaina almarin Ammar yafi karfina amma ai befi karfin Allah muyi ta masa addua insha Allah kome ze daidaita" Husnah ta share hawayenta "to Mummy insha Allah" " bari naje, in kin kintsa ki fito muci abinci "Mummy ta fada a daidai lokacin data ke k'okarin fita.

Bayan 2hours.

Mummy na zaune duk abin duniya ya isheta, tama kasa tuna waccece Pinky da matsyinta a wajen Ammar, kamar taso taji sunan a wajensa amma sam ta manta had'insu, wayarta ta dauko ta shiga laluban number Bobo taci sa'a kuwa ta ganta, cukin hanzari ta kira layin, bugu daya aka dauko "Mummy ina kwana?" Bobo ya fad'a da muryar girmamawa " "Lafiya lau, dan Allah inaso kazo gida yanzu akwai wasu tambayoyi danakesan maka" Gaban Bobo ya fad'i " Mummy hope dai lafiya?" Lafiya ba lafiya ba, ina jiranka dai" Bobo yace "to no wahala gani nan zuwa" .

Sai bayan 30mint Bobo ya iso, ya gaishe da Mummy sannan tace " Ni wai ya sunanka na gaskiyane? Bansan kiran wannan sunan naka wai Bobo?" Ya dan sosa keya yai murmushi " Mummy sunana na gaskiya Buhari" tai dariya " suna me d'adi suke ce maka wani Bobo? Yanzu ba wannan ba dama tambayraka zanyi wacecce PINKY? Bobo yace " Pinkyn Aj?" Mummy tace " Eh ita fa," Bobo yaja ajiyar zuciya sannan yace

"Sunanta na asali Surraya amma ana kiranta da Pinky yar asalin garin Bauchi ce amma ta gudo Kano dalilin cikin shege datayi ta kama daki a wani gidan karuwai dake nan, Sun hadu da AJ ne a club shekara 2 da suka wuce, inda ta nuna tana sanshi ya kuma fad'a mata bashida ra'ayi, dakyar da siyasa ta samu taja hankalinsa ya fara santa har suka fara soyayya" Mummy tace "dankari! Nan ta labartawa Bobo labarin duk abinda ya faru a tsakanin jiya da yau, shi kansa ya firgita, yana jinjina kai yace " tabbas zata aikata! dan bazan manta abinda tace ana sati daya bikin AJ tazo har inda muke zaune ta kuma gagayya masa magana inda tace se yayi nadamar yaudarata da yayi, na tabbata tayi amfani da malamai da bokayen datake bi, nasan AJ ciki da bai, nasan abinda ze aikata nasan wanda baze aikata ba, na tabbata AJ da hankalinsa baze tab'a aikata hakan ba!.....

*** Kuyi hakuri na rashin jina kwana2 abubuwa sunyi yawa amma insha Allah yanzu zaku dinga jina akai-akai. Gaisuwa da fatan alheri gareku masoya littafinan a duk inda kuke❤***
《Hafsisi》

ASMAUL~HUSNAWhere stories live. Discover now