2

2.6K 100 2
                                    


ASMAUL HUSNA 2

★★★ *ASMA'UL ~HUSNA* ★★
© *MISS HAFCY*
® *NWA*

*DEDICATED TO BESTY HUSNAH*

0⃣2⃣

A hankali ta furta salama cikin d'addar muryarta", daya bangaren aka amsa "my All ina kika shige ne inata kiranki amma shiru" "am sorry Mi Amor yau lecture mukai ba intervals dayawa sai yanzu dana dawo gida na d'au wayar" "okay My All to bari na barki ki dan hutu zan kira anjima" murmushi tayi sosaii sannan tace " to shikenan take care" yace " i will My All" sannan ta kashe ta shiga bandaki dan watsa ruwa.

Bayan 'yan mintuna ta fito cikin doguwar riga light purple ta amshi jikinta, kai tsaye wajen dinning tayi, dan kawar da yunwar dake damunta, ta fara bude warmers din dake kai, na farko fried rice ce taji kayan had'i dayan kuma farfesun kayan cikine sai kamshi yake ga jug na Mango juices, ta lashe baki "yummy!" Ta fara zubuwa a hankali, sannan ta faraci tana yaba dad'in abincin, Abba ne ya shigo rik'e da jaka ya dawo daga office da sauri ta tashi tana murna ta karbi jakar "Abba sannu da zuwa" yauwa Husna, ya school?" Alhamdulilah Abba, to madalah Abba ya fada yana murmushi, "ina Mamantaki?" Tana ciki" ta amsa, okay bari na shiga, tabishi da jakar ta aje a palour dinsa sannan ta dawo ta cigaba da cin abincin

★★
A b'angaren AJ kuwa be tashi ba sai wajen bayan la'asar, a hankali ya bude idanuwansa ya ture blanket din ya tashi cikin hanzari ya d'au towel ya shige tiolet dake hade da dakinsa, be wani dade ba ya fito, drower dinsa ya bude ya dauko wata armless riga white me adan black yasa three quater din wandonsa shima white me adan black ya feshe jikinsa da turare ya taje kansa da za'a iya kitse shi saboda tsabar yawan gashin danma gashin kamar na larabawa kuma dagani ana kashe kud'i wajen gyrashi.

Jero salolin da'ake binsa ya fara yi tundaga magrib na jiya har zuwa la'asar din yau sharp sharp yayi ya gama ko addu'ar kirki beyi ba yasaka earpiece dinsa wakar Lil Wayne yasa yana kada kai yana bin wak'ar kamar shi ya rera a haka ya fito daga dakin.

Kai tsaye kitchen ya nufa, a gaban sink ya tadda me aikinsu( Aisha wadda suke kira ESHALE) tana wanke wanke " ke!" Ya daka mata tsawa, a kid'ime ta amsa sannan ya cigaba " ina breakfast dina?" Cikin inda- inda tace " breakfast kuma? Kode abincin rana? Yanzu fa an kira la'asar" cakumo ta yayi yafara dala mata mari to ko'ina "keni sa'anki ne kike musu dani? An fad'a miki bansan an kira la'asar din ba?" Wani k'ara ta saki wanda yayi sanadiyar tasowar Hajiya da sauri dan ta juyo tun daga falo " mene ne?" Ganin AJ tayi tsaye yana huci " Mummy kibarni na mata duka, saboda ta rainani ina tambayarta breakfast tana min maganar lunch," cool down my son muje yanzu za'a kawo maka worry not" ta kalli Eshale dake ta kuka tace " kema kinsan halin shi akan me zaki tab'oshi? Son me kake son ci?" Chips da scramble egg" ya fada a takaice, Mummy tayi murmushi " kwantar da hankali bada 10 min yanzu za'a ma consider it done" kada kai yayi ya fice daga kitchen yana huci.

Mummy ta kalli Eshale tana tab'e baki cikin rashin damuwa tace " yi hakuri kema da jan magana ai kekikaja, yanzu dai dauko farayayen chips din nan dana siyo dazu ki soya mai ki masa scramble egg, kiyi sauri na baki minti sha biyar(15)) Eshale ta share hawayenta ta fara abinda aka sata, cikin 'yan mintuna ta gama ta jera masa a dinning ta kawo masa flask din ruwan zafi already dama akwai kayan tea akan dinning, harara ya dala mata bako nagode ya fara ci yana gunguni.

Yana cikin ci ne wayarsa ta ringing sai data kusa tsinkewa ya dauka " Hlo kai kar ka takura min pls wetin happen?" Dayan bangaren akace " kai Baabaa kana ina ne? Yau akwai birthday din Teemoh baby till down zamuyi yau a club kaifa ake jira kazo afara organizing abin nan" tabe baki yayi " kasan ni ban zuwa wajen kolancin nan, Teemoh baby har yaushe ta waye da zanje birthday dinta? Da village girl ni ba inda zani " " haba AJ pls kazo kasan in kaje wajen zefi armashi kuma tana can tana expectin zaka zo, tun saura 1month fa take ma zancen" " mtsw shishigin yarinyan yayi yawa dan taga irin kudin dana kashe a birthday din Pinky, shine take expectn zan mata?, to kace mata bazan zo ba," ya katse wayar yana tabe baki" Mummy dake kalansa tun sanda ya fara wayar ta juyo da sauri " kai da waye?"

"No need kisani cuz be shafeki ba!, ya fada ba tareda wata damuwa ba, " nidai yanzu please ina bukatar 100k aljihuna empty please ki temaka" tayi murmushi " me zakiyi da 100k? canake kan Dad dinka yayi tafiya sai daya baka makudan kudi?" "Sun kare" ya fada a takaice" to ni banda kudi, kuma ko in inadashi ma bazan baka ba! Marairacewa yayi sannan yace " ina magana ace ni dan gatane amma in nace aban kudi aki bin, just 100k shine zaa ce baza'a aban ba, to shikenan ai nasan inda zanje na samu" tayi sauri dakatar dashi " kar ka kuskura kaje wajen nan, ka bari zan baka, but kafin nan promise me bazaka k'ara tambayata ba" cike da zumudi yace " i promise" Mummy tace " yauwa bari naje na dauko ma" murmushi yayi sannan yace " Dats my mum i luv soo much muah, nagode" tayi murmushi " love u too son" sannan ta tashi ta shiga d"akin...
Hafcy.blogspot.com

ASMAUL~HUSNADonde viven las historias. Descúbrelo ahora