🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY👄**January 2017*
3⃣Cikin gda yakoma yana huci yace "wannan wace irin masifa ce? Salman Ashe har yanada bakin cimun mutunci ya badawa idonsa kura basani ba sabo kamar batare mukayi kuruciyaba?"
Kwanciya yayi akan kujerar zaman mutum biyu ya zabga uban tagumi babu abunda yake dawoma kwakwalwarsa sai yadda son NASREEN ya mamaye ilahirin birnin zuciyanshi yadda bazai iya rabuwa da itaba.Sadi yasan NASREEN tun tana yar karama kasance wanshi abokin yayanta, Wanda amintarsu ta wuce gaban wasa babu inda baya kutsawa acikin gidansu, gashi iyayen Salman sun kasance masu k'aunar Sadi saboda ladabi da biyayyarsa da ganin girman manya,
Al'amarin yafarune lokacin da NASREEN tadawo hutun dogon zango daga *Delight secondary school* dake cikin garin kano a k'aramar hukumar Kumbotso dak'e Panshekara, makaranta ce wacce yaran manya ne kadai ke iya zuwa makarantar duk da bawani girma gareta ba amma har daga kasashen k'etare ana kawo dalibai don samun ilimi ingantacce.Sadi ne jingine da motarsa dayayi packing a farfajiyar gidansu Salman, Wanda ke cikeda ni'ima ta bishiyu da shuke shuke dake kad'awa gashi Daman lokacin hunturu ne, Sadi sanye yakeda jeans da Riga mai wuya(tortul neck) sannan sai jacket (rigar sanyi), Wanda duk Wanda yayi masa kallon tsaf yasan shigar kota meye.
Sadi jiyayi ajikinsa kaman dakwai wani koh wata halitta dake kallonsa, dagowan da zaiyi yayi ido hudu da Nasreen ta taga daga saman bene tana kallonsa lokaci guda ta boye tareda jin kunya.Tundaga Ranan nasreen take masifan Jin kunya Sadi koda yashigo cikin gidansu, saidai ta boye kanta a daki koda kuwa ya bukaci tazo su gaisa sai tace ace tana bacci, hakan bai dameshi ba saboda yasan akwai tsantsar yarinta a tartare da ita,
wata safiyar Asabar ne Salman ya bukaci Sadi dayazo su maida Nasreen makaranta alokacin Hutu ya kare, ba musu Sadi yashirya cikin manyan kaya Wanda duk namijin daya ganshi saiya fadi irin shigar dayayi wacce ake kira Muhammadu Buhari style.Lamarin bai k'ara ta'azzara ba sai lokacin da Nasreen tashiga cikin mota a gidan baya ta zauna amma ba'a gefe ba tsakiya ta zauna yadda zata dinga hada ido da Sadi ta glass, Wanda yatafi da imaninta harda baseerarta gami da zuciyanta, Sun kama hanya amma gaba daya Sadi a tak'ure yak'e har Salman yaso yagano hakan,
Amma saiya wayance duk inya kalli madubi saiya hada ido da ita Wanda hakan ba karamin dad'ad'a mata zuciya yakeba.
Allah Allah sadi yayi su isa makarantar su sauketa ya huta da mayattacen kallon datake mai.Tunda suka sauketa sukayi Sallama suka juyo, Sadi yake fargaba acikin zuciyanshi, Adu'a yakeyi kada Allah yasa abunda yake hassashe ya zama gaskiya, Allah bai karbi adu'arsa ba saboda tabbas shima zuciyansa ta harbu da son baiwar Allah Nasreen.
Bayan wata daya da tafiyar Nasreen, Sadi yana zaune acikin office dinshi yana hada wasu takaddu Wanda za'a tura kasar new York city don siyo karafunan mota, kwankwasa kofa yaji kamar daga sama yace
"Yes come in"
Abokin aikinsa yagani Adil tsaye Murmushi Sadi yayi yace "Mutumina lafya daganka da sanyin safe a office dina? Allah yasa lafya"?
Adil yace
"Inafa lafya yar' mutane ta mutu a sonka",
Lokaci guda zuciyar Sadi tafara bugawa fargaba fal acikin ranshi karfin hali yayi yace
"Aboki ban gane inda maganarka ta dosaba"?.
Envelope Adil yafito dashi daga aljihunsa ya nikawa Sadi, hannu na rawa ya amsa "Abokina Nasreen ce tayo aike tace gashi abaka sannan tanada bukatar reply nanda kwana biyu"..Adil yana gama magana ya nemi guri ya zauna saboda baisan meye aciki ba, Sadi yafara bude wasikar a hankali kamar ancemai bomb ne aciki, Adil yace
"Mutumina kudine"?
Sadi yace
"wasikace kawai kuma zan karanta amma bayanzu ba".
Adil tashi yayi yayiwa Sadi Sallama, bayan fitansa ne sadi ya tashi ya kulle kofa saboda bayason Wani disturbance (Damuwa).Sadi bai bata wani dogon lokaci ba yafara karanta wasikar,
_SADI_
_Dafatan wannan wasikar ba zata k'ona rank'a ba, haka nan kuma bazata zama katsalandan ga rayuwarka ba, nake budeta da tambayar lafiyanka da ainihin aikinka, Gaban sadi faduwa kawai yakeyi, Mai yuwuwa wasikar ta baka haushi da takaici yayinda kake karantowa sannan yayinda kaji daga hannun wacce yafito. Haka nan mai yuwuwa kayi Shankar abunda na rubuta a cikinta koma kaga kamar nayi maka rashin kunya, amma inaso ka daure ka karanta koda bazan samu amincewarka ba.__Nidai tsawon lokaci, a gida koh a makaranta ina samun karancin Bacci sannan da karancin tunani duk dominka, nayu kokarin ganin na jure amma nakasa jurewa in boye nakasa boyewa nadade ina tunaninka sannan zuciyata ta Dade tana tafarfasa dominka Wanda hakan kesamun k'unci da Rashin kwanciyan hankali._
*©ZAZZAU*😘
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.