NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani) Babi Na Takwas

160 5 0
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄

*January 2017*
8⃣

 
     "Amin"
Gyara xama tak'ara yi magana yak'eyi ciki ciki, nidai banjin komai sai umm da ah ah hirar yan mata kenan idan aka kule kuryar gado, sallama sukayi cikin amincewa da juna, tabbas bagudu ba jada baya NASREEN da SADI soyayya sai abunda ya turewa buzu nadi,
Don babu dare ba rana waya har kawayenta sun fara gane yanayinda kawarsu take ciki na LOVE.

Salman kuwa, abun duniya ya isheshi, zaune yake a bakin gate, Sai muzurai yakeyi wani mutum ne ya iso kofar gidan cikin wata Range Rover mai launin Kore, Shidai Salman binsa yakeda kallo don ko a hanya baitaba coming  Acrossing din wannan fuskarba,
Fitowa yayi daganinshi Dan gayene amma kallo guda zakayi mai kasan cewa bakaramin mutum bane, Ashekaru zai iya kaiwa shekara 40.

Bai nufi koh inaba sai, wajen Salman sallama yayimai gamida mikamai hannu, barka dai Salam yace
"Bawan Allah wani kake nema ne?"
Cikin sauri yace
"ah ah Amma dakwai wata yarinya da nake nema kuma ina kyautata zaton kamar nan gidan naga tashiga doguwa ce".

"Salman yace, Kwarai nan gidanne kanwata cema sunanta NASREEN, koh lafya?".

"Eh a gaskiya naji dadin ganinka, kwarai saboda a magana ta gaskiya inason k'anwarka sona hak'ik'a kuma agaskiya banaso abun yadau wani dogon lokaci amma bansan ya ita k'anwar taka zata dauk'a maganarba, kila koh dakwai wani Wanda takeson ta aura koh take soyyaya dashi".

Salman ya gyra tsayuwa yace,
"ai tazo gidan sauk'i Abu guda zakayi yanzu zan baka lambarta, inaso kayi duk yadda zakayi ta soka kadasa soyayyarka acikin ranta, amma kafin haka kazo zuwa jibi mai gidan zai dawo sai kazo ka  gabatar da kanka, koda wani Nasan bai rigada ya gabatar da kanshi ba nabaka dama".

Yayi godiya, Sosai yakumaji dadii har wasu yan canji ya mikawa Salman  nidai tsaye nayi na rike baki, hannu na kyarma Salman ya amshe kudin saikace Wanda ke yunwansu, Wanda tsayawa gayawa mai karatu arzikin mahaifinsu batawa ne, kuma babu abunda yake nema wajen mahaifinsa ya rasa amma inyana maula wasu har zundenshi sukeyi, wasu su bige da zagin mahaifinsa.

Sallama sukayi, cikin gida yashiga, ya samu, NASREEN zaune daga ita sai three quarter, dawata yar karamar Riga wacce koh cibiya batakaiba, gashi tayi packing gashinta da ribbons sunkai takwas sauda yawa wasu kance tayi acuci maxa amma hakan baya damunta.

Cikin murmushi, yace
"kanwata wai har yanzu fushi kike dani? Haba yar k'anwata k'usada ita ya matso kiyi hak'uri, tashi tayi tace,
"dakata yaya bak'ada abunda zak'ace mun, saboda karigada ka rusamun budget" tak'aitaccen labarin ziyarar data kaiwa SADI tafara bashi, da maganar da sukayi.

Shima tsaye ya mik'e "me kike nufi kenan? Ba zaki rabu dashi ba?" Ta girgiza kai.
Bawai bazan rabu dashi bane, yaya ya nemi Dana bashi dama, yace indai akan halayyansa ne zamu rabu yayi mun alkawarin ya daina duk abunda yake yi,".

"Jinan rukayya" inji Salman, "Sadi bazai taba daina halinsa ba, ki saurari maganata sosai, Najima ina tareda Sadi abokinane kut da kut, Nasan shi fiyeda yadda wani koh wata yake tunanin Nasan shi, kiyi hakuri har Allah ya kawo miki Wanda zai dace da rayuwarki".

"Gaskiya bazan iya rabuwa da SADI ba yaya".

Wannan maganarce ta sanyawa Salman wakafi, "Bazaki iya rabuwa dashi ba?"
Sunkuyar dakai NASREEN tayi tace "Ka gafarce ni yaya Gaskiya inason sadi bazan iya rabuwa dashi ba".

"In baki rufemun bak'iba, yanzu zan lallasa ki sakarya Mara wayo, ga mutanen arziki suna sonki Amma ke kin nacema ma wannan sakaran tasono dashi, wallahi ki kiyaye ni inba hakaba saina bata miki rai,  banda kin raina mun wayo"?
Yaya Dan Allah meye na rainin wayo acikin maganata gaskiya ne kuma dole infada zan cuci kainane inyi shuru? Kaga yaya ka barni naso Wanda zuciyana take muradi" tas saukan mari taji ai a guje ta fece don bazata tabayin sake yakara yimata dukan jiyaba.


*©ZAZZAU*😘

NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)Where stories live. Discover now