🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January 2017*
1⃣6⃣Sadi baikara cewa komai ba, illah tashi dayayi yace
"Idan ta kammala tasameni a waje".
Koh kallonsa hajiya batayiba, taja tsaki tace
"Duk kagama aure babu fashi kuma zama daram",
Amla dake Jan trolley dinta cikin natsuwa ta tsugunna gaban hajiya uwar Nana "Hajiya kiyafemun idan na bata miki rai nizan tafi sai gani na biyu"
Washe baki hajiya tayi tace,
"mikomun waccan jakar kudi ta dauko Wanda batasan iyakansu ba ta mik'awa AMLA" amma kemadagas taki amsa saida tayi dagaske, yaran cikin gidan kowa sai bank'wana yake mata kowa da kyautar daya bata, tasa Jakarta da tsarabarta a bayan boot
Shigarta keda wuya sunfara tafiya ta, juya abun mamaki Sadi tagani sanye da Three quarter da Riga yar shara, zare ido tayi cikeda mamaki shiko Sadi kallonta yake ta wutsiyan ido."Wannan wane irin wulak'ancine, Dan Allah wannan wace irin shigace irinta yahudawa? Ahaka zaka gaida surukai, oh my God this is Disgusting" tasa hannunta a gashin kanta tana yamutsawa,
"Gaskiya inharda wannan kayan zaka kaini gida saidai ka ajiyeni anan Dan bazan iya wannan rashin kunyanba, suruki da Bacci Gadon matar dansa".Sadi juyowa yayi cikin wata shegiyar murmushi
"Gaskiya wannan shine karo na farko dakika taba burgeni,
Dakika iya namijin kok'arin cewa in ajeki a dok'ar dajinnan"
wata irin dariya yayi yaja wani mugun birk'i yace,
"inaso kiyi gaggawan fita daga cikin motan nan idanko kikak'i saina kaimu indan zamu hala".Shiru tayi tana tunani
"Toh yanzu iya sauk'eni inaxan samu mota gashi mun baro gari, idan nace mutafi ahaka dawani ido jama'a zasu kallemu?"
Nidai Humairah nace sha'awara yarage ma mai shiga ruwa.........
Juyowa tayi tadan kalleshi saitaga bama ita yake kallo ba, cikin tsawa yace
"Jiranki nak'e kifita intafi inda nafi wayo"
Marairaicewa AMLA tayi tace "Dan Allah my blood kayi hakuri mutafi amma gaskiya iya kanka, kofar gida basaika shiga cikin gidaba".Wani irin k'allon rainin wayo ya watsa mata, "Meye amfanin cewa inkaiki gida inhar bazan shiga ingaida suruk'aina ba? Look koh kiyi shuru kizubawa sarautan Allah ido kokuma inyi flushing dinki waje".
Ai AMLA koh motsi takasa yi har suka isa cikin garin jigawa har kofan gida ya ajiyeta ya fito ya bude bayan boot yaciro mata kayanta daduk wani tsaraba nata."Kallonsa takeyi taga iya ruwan gudunta,
"Kina iya dauko kayan mushiga" gaba yayi yabarta tsaye ai dagudu tasha gabansa tace "Dan Allah my life karka shiga dawayannan kayan! Badan niba"
Bangajeta yayi yashiga cikin gidan har cikin falon gidan ya shiga yana sallama, umman AMLA ce tafito ganin Sadi yasa ta wadata murmushinta,
"Mutan dutse mutan kano dafatan kunzo lafya? Ina ita Amlan koh ba tare kukeba".Tsugunna wa yayi tukunna yafara gaidata cikin ladabi da biyayya,
"Tare muke da ita gatanan shigowa nizan wuce umma idan Abban yadawo a gaidashi".
Tsam ya tashi yafice umman AMLA koh mamaki ne duk yabi yadameta,
"Wannan wane irin shigane koh ba komai zakazo gidan surukai kasa kayan mutunci Allah ya karemun yata Donni wannan auren basonshi nakeba idai ladabine da Sanin girman mutane Sadi badaga nan ba".Sadi na gabda fita yaci karo da ita sai tare tare takeda kaya, kallonta yayi yace
"Allah raka taki gona, daman duk saboda ke hajiya ta dameni masifan yau daban na gobe daban"
Dariya AMLA tayi tace abun dariya yaro ya tsinci hakori, banda abunka kwana nawane zamu dawo tsintsiya madaurinki daya kaga hajiya saitayita yankan tsokanka tana miya dashi" mtwzzz wani dogon tsaki taja,
Binta kawai yakeda kallo.*KANO*
An shirya komai a dining table, NASREEN koh ta gaiyaci Kawarta Afnan tazo ta tayata tarban bak'i,
Gunjin motoci taji ai Tuni Afnan ta tashi ta leka ta window
"Waw k'awata kinyi dace Kwarai baki ba wahala daman bakiyi gadon shi ba,
Kinga motoci kuwa
Daganin wannan shine Angon wannan kuwa wan angone kayansu iri daya, kawata Dan Allah kitaso kigansu nasan dole kiyi alfahari dasu".Juyowan da Afnan zatayi, taga Nasreen kwance sai rusa uban kuka takeyi lokaci guda afnan ta bata rai, tace
"A gaskiya MUSNAS kina ban mamaki har yanzu bazaki cire Sadi daga cikin ranki ba? Look maxa kitashi ki wanke fuskanki ki shirya, NASREEN tace "Afnan yazanyi da soyayyar danake yiwa Sadi bazan iya rabuwa dashiba, kuma yau nasan za'a samun rana da musty, nashiga kuka cikin kuka ta kwabe fuska Afnan itadai lallashinta kawai take don tasan yadda kawarta takeji akan Sadi amma yaxama dole Nasreen tabi umurnin mahaifinta don gamawa da duniya lafya.Tashi NASREEN tayi tak'ara wani wanka tashirya cikin wata Atamphanta Super Aura wacce taji Stone work, Riga da skirt ne sun amsheta, zama tayi gaban mudubi Afnan tayi mata makeup, ta daura mata dankwali duk Wanda yaga Nasreen saiyaji kamar ya saceta, sarka tad'auko ta gwal ta laka a wuyanta, ga zobbai sai sheki suke.
Ammi ce tashigo cikin murmushi tace, "waw you are looking beautiful my Princess"
lokaci guda Nasreen taji wani irin haushi inama ace Sadi tayiwa wannan k'walliyan, tasan da saiya kai dare yana kare mata kallo,
Takalmi tasa high hill ta dauki gyalenta KUMAR Wanda ake yayi, To Match tayi.
Afnan ke taka mata baya itakoh NASREEN jitake kaman ta fadi saboda bakin ciki har cikin falon baki suka samesu, zama sukayi akan kujerar mutun biyu, wani irin murya NASREEN takeji kaman na Abba amma takasa tantance waye musty acikinsu dayake ta sunkuyar dakanta kasa.*©ZAZZAU*😍😘
*For comments and correction the door is open*👍🏻
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.