🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January 2017*
1⃣4⃣"Tashi kifita"
cikin tsawa daddy yake magana, NASREEN tashi tayi tafita jikinta dukya mace zuciyarta tana zargin su Ammi da Abba, me Ammi take son fade Wanda Abba ya hanata fade?.
"Karki sake ki fadawa NASREEN cewa bamune iyayenta na ainihi ba, idan kikayi haka kin karya Alkawarin damuka daukarwa kanmu nacewa babu wani mahaluki daxai sani har duniya ta nade".Shuru Ammi tayi tace
"Amma a gaskiya yakamata kajikan Nasreen kabarta ta auri muradin ranta, koh ka manta gwagwar mayar da'aka Sha kafin muyi aure koh ba haka ummata ta Tsaya kaida fata wajen ganin na aureka ba?"
"Dakata karki sake kiyimun katsalandan cikin al'amurana, bazan taba ba Dan iska yata ba"."Ammi da ranta ya gama baci tace inbaka ba Dan iskaba, zaka bata Wanda bazai taba damuwa da itaba, Wanda aikinsane a gabansa ba mataba, Wanda bazai iya cika hakkok'in auren dasuka rataya akansa ba kaga daganan idan takasa jurewa saita fada wani hali Wanda bashi muke fataba,
Wallahi kasani iyaye maza kuke jefa yayanku cikin halin k'ak'anik'ayi saboda auren dole, indan kudinsa kakeso NASREEN ta aureshi wane irin darene jemage baigani ba? Sai Daren da uwarsa ta haifeshi".Rai abace abban su NASREEN yafice tabarta zaune, a kofar kitchen yaga NASREEN yace
"Kiyi maza ki gama girke girken saboda sunakan hanyarsu na zuwa, sannan saura inji wani Abu ba daidaiba".Cikin bacin rai Nasreen ta fada kitchen din kafan Laure tasa kanta tana kuka,
"Dan Allah baba Laure kitaima keni wallahi banason Wanda Abba zai auramun, Sadi nak'eso kuma shi nakeso in aura" itadai Laure shuru tayi don tasan irin ciwon da NASREEN takeji saboda itama tataba shiga irin wannan rayuwan,
"Nasreen share hawayenki kiji"
Cikin sauri ta dago tace mezakimum baba Laure?
"Kinsan inasonki koh? Inason abunda kikeso? Toh ki dinga tashi kina sallan dare, kina kaiwa Allah kukanki kina Neman zabi toh koda An taru za'a daura aure da musty sai an fasa, an daura da SADI".Wani irin ihu NASREEN tayi tace, "Baba Laure dagaske kike? Naji dadi Kwarai tabbas kincika uwata gari Ammi itama tana iya kokarinta amma abun yaci tura Allah yasak'a muku da gidan Aljanna"
"Amin"
Ammi ce tsaye ganin yarta cikin farinciki yasa ta matso tace "wani albishir ne yasamu tilon yata?
"Ammi adu'arku kawai nakeso naji dadin sha'awaran baba Laure tabani".*Tabbas burin kowacce uwa ganin yarta ta auri abunda ranta yak'eso, sannan burinta taga yarta cikin farin ciki yawancin auren dole daga iyaye maza yake bullowa kuma sunfi kowa dana sani*.
*Dutse*
Tunda suka gama wayada NASREEN yake tunani masu yimusu hidima ne suka shigoda kayan Karin kumallo aka kawo musu, waya yadauka yakira Adil "mutumina kayi harama kazo ka karya ka koma bakin aiki kasanar dasu halinda nake ciki, Donni inajin dawowa na jigawa ajalinane yayi".
Bayan sun gama breakfast ne Adil ya kimtsa Yakama hanya shiko, Sadi cikin gida yadawo yanata nazarin abunda ke shirin faruwa dashi,
Karo yacida wata yarinya babu shakka AMLA ce saboda bazai manta kamanninta ba, tea dinda ya watse masa ajiki yake kallo ba itaba saboda babu wata ya mace dayake kara son gani inba Nasreen ba,
Cikin karamar murya tace
"Dan Allah yaya kayi hakuri bansan cewa mutum na tahowa ba, pls am sorry I don't mean to hurt you".
"Dakata maza kibacemun daga View banza Mara hankali, kawai kuna tafe kuna Dan iskan chatting daman yaushe zakisan da mutum Dakin konani dasaina miki aibu".Haushinta kawa yaji yakeji, Allah shi kyau ta in aureki wannan ai saidai inji ciwo ba inji dadii ba, kada kansa yayi yashiga daki kwanciya yayi yana tunanin Rayuwa, ji yayi Anata ihu oyoyo Baba! oyoyo baba!!!!?!
Wani dadi yaji aransa, yasan mahaifinsa baxai taba yimasa abunda bayaso ba.
Saidaya tabbata mahaifin nashi ya huta yashiga bangarensa, yayi sallama abun bakin ciki uban nashi koh kallonsa baiyiba.
Karin bakin ciki*©ZAZZAU*😍😘
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.