🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January 2017*
🔟Inta kaitawa mai karatu iyayen sadi hamshakan masu kudine a garin Dutse dake m gawa, makaranta ce takawoshi kano harya hadu da Salman, bayan sun gamane yasamu aiki a wani kamfani dake chalawa.
Da sanyin safe Sadi yanufi wani babban asibiti inda za'a diba lafiyarsa, dakyau sannan asan wace irin cutace dashi.Bayan yasamu nasaran ganin likita ne yafara yimishi, bayanin abunda ke damunsa, kallonsa likita yayi yace
"Bawon Allah bawata cuta bace ke damunka illah Cutar damuwa, Wanda inbaka rageba kana gab da kamuwa da cutannan datayi ramped agari Wato *Hawan jini* inhar tayi kamari toh kana iya kamuwa da ciwon *Zuciya* idan bakayi wasa ba harsai takaiga sai anyima *DASHEN ZUCIYA*"
(littafina biyu mai zuwa cikin wannan shekaran.Shidai sadi kallon kawai yakeyi,
"Likita meye mafita sannan inaso ka daurani a maganin dazai kusarmun daduk wata damuwa saboda inacikin matsala" yana cikin maganane yaji karar wayarsa dakai dubinsa ga wayan yaga *MOM* yayi appearing ajikin tank'amemen Screen dinsa, dauka yayi jiki ba kwari yace "Allah ya taimaki hajiya uwar Nana Dafatan kun wuni lafya"."Dakata Sadi Bana bukatar gaisiwarka, daman ashararancin dakake kenan a Kano? Neman mata da shan giya toh Alhamdulillah Allah ya Toni asirinka Shiyasa koda yaushe innayi maka maganan Aure saikace ba yanzu ba Wato sai matan banza sun kare zakayi aure toh baka isaba wallahi, maza ina umurtanka daka shigo jigawa komin dare inason ganinka".
Bata jira yace wani abuba, karaf ta kashe wayarta dafe kai sadi yayi yana huci idanunsa sunyi jajir kamar garwashi yace "likita indai irin wayannan abubuwan na faruwa dani, Toh bazata gaiga anyimun Dashen zuciya ba, zata tarwatse".
"Meyasa ka fadi irin wannan maganan? Kasan cewa komai yayi zafi maganinshi Allah sai kace ba musulmi ba? Kamanta da Hadisin dayace, Idan kana cikin bacin rai ka yawaita cewa
(Inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun)? Inaka aje wannan hadisin kanasawa kanka damuwa tun kana Dan karami?"."Likita kenan, bani magani nagode daduk wata sha'awara taka, zanyi amfani da ita da yardan Allah".
Tashi yayi yafita amma yarasa ina zai dosa, dawace kama zai nufi Dutse?
Cikin Motarsa yashiga amma gaba daya hankalinsa da tunaninsa baya jikinsa, Atakaice zan iya cewa Allah ne yakaishi gida lafya.Kwace yake Kwatsam saiga abokinsa Adil "Mutumina lafya naga duk kabi ka rame kwana biyu shuru gayamun meye ke damunka?
"Adil ni meyema baya damuma? NASREEN ta juyamun baya, Salman ya tasata gaba, gashi Mom itama ta huro nata wutan! Yazanyi abokina inaso ka taima keni kakaini Dutse inyaso kadawo da motar ni acan zan Tsaya inji Neman da akemun".Shuru Adil yayi yace
"Toh abokina tashi ka shirya mutafi kasan hanyan jigawan nan sai a hankali in dare yayi"
Haka suka tashi sai cikin Garin Dutse.*DUTSE*
Wani layi suka shiga dagani, masu k'umban Susa ne ke zaune a unguwan koda naji GRA nagani A rubuce,
Sai shuke shuke tundaga farkon layin har karshe, sai haushin karnuka kawai kakeji.
Wani katafaren gida suka tura hancin motarsu, Adil sai murna yakeyi saboda baitaba manta wani zuwa dasukayiba, yaci abinchi harsaida ya fara Gudun bayi.
Shiko Sadi rannan a turbune gabansa sai fadi yakeyi, horn sukeyi chan saiga mai gadi saboda tsabar tsaro harsaida ya leko yaga wake horn kafin ya bude musu suka shiga.Tirkashi
*Gidan su Salman ne koh Sadi?*
Mai karatu tunda Nike inajin ana cewa akwai Aljannan duniya amma bantaba coming across din irin wannan tsarin gidanba, don yafi gidansu NASREEN tsaruwa dagani Wanda ya zana gidan badan Nigeria bane.*©ZAZZAU*😍
*Zaku gafarceni👏🏻Saboda makaranta Dana koma, I will be a little bit busy😫, my love for you will never dies😍😘*.
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.