🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January 2017*
4⃣_Da nayi niyyan in barma zuciyana amma sai kawayena suka sha'warceni da in sanar dakai in nunama abunda ke zuciyata, intayi ruwa rijiya in batayi ba Shadda._
_Saidai ina wannan muradin nawa bai samu shiga ba, bazan damu sosai ba kona damu zanyi iya bakin kokarina ganin na tankwasa zuciyana, na tursasawa zuciyana ganin na hakurewa raina abisa dole, koda yake inhar bukatar bata amsu ba ban rasaka ba muna tare tunda kai abokin yayana ne Wanda a hakan nasan matsayina nanan da kanwarka._
_Amincewarka ce burina, hada jini dakai shine cikar fatana ina sonka ina kaunarka_.*Daga k'anwarka mai fatan zama matarka NASREEN (SADNAS) A Abdullahi*.
Jiyayi zuciyansa na Duka da sauri, ya Mirza takaddar, yaji babu shakka takaddar ce a hannunsa,
Wannan shine tayinda NASREEN tayi Wanda ya kasa tsallakewa, Ba shakka Nasreen ba irin matan da zasu yiwa mutum tayin Kansu bane na iya tsallakewa ba.Domin kuwa ta halittu ga kyawun hali, A dalilin haka Sadi ya kamu, yau shekara Kusan biyu da rabi kenan amma babu Wanda yasan halinda suke ciki.
Abu d'aya da Sadi yayi Wanda ya jefashi a tarkon shine k'in yiwa Salman bayani, inda salman yasani tun a farko kafin yakamu dason Nasreen toh duk da sauk'i, don an nemi a rabasu duk ba zaiji zafin rabuwarsu ba, amma kuwa tabbas in aka rabasu yasan shikenan natsuwarsa da tunaninsa duk zasu gushe.Tun kulla halakarsu, yarage wasu mugayen halayyansa, yawon dare duk ya daina, Neman mata kuwa duk ya daina saboda alkawarin daya daukarwa NASREEN, koda yake yanada Wata budurwa mai suna BETI yar Southern Kaduna ce Wanda aiki yakaita garin Kano, don acikin gidansa ta tare cinta da Shanta duk a wuyansa yake, sannan in dare yayi su aikata Abunda Allah bayaso Wato (Zina), Sadi yarasa yadda zaiyi ya banbareta, saboda tariga tasaba dashi, shi kadai yake iya gamsar da ita indai a fagen kwanciya ne.
Zaune, Sadi yake yace "Yazama dole in rabuda NASREEN tun wuri tun kafin sonta yamun illah acikin zuciyana, Hannu yasa aka maiyasa tun farko na yarda da bukatar Nasreen abunda nasan banda niyyan yin aure yanzu, meyasa na daukan mata Alkawari gashi inaso in karya Alkawarin, inasonki Nasreen ina sonki yazanyi gashi Salman ya kudiri aniyar ruguza halakata dake, dole muhakura da juna badon munaso ba".
Karar wayarsa yaji, Assalamu alaikum yaji ance lokaci guda yaji zuciyarsa ta buga, Nasreen ce baka ganeni ba? Tace cikin yauki da yanga,
Lokaci guda Sadi ya kashe wayar baki daya.*******
Salman yayi packing motarsa a fusace yafito yashiga cikin gida, Dakin shakatawarsa ne waje na farko da mutum zai iya isa kafin shiga cikin gidan,
Nasreen yagani zaune akan doguwar kujera ta harde kafarta, tana kallon film din India a cikin wani katon talabijin mai launi,
Nasreen dai doguwa ce Dirarriya a mike kamar ingarman doki, mijinta kalar mak'uba, tanada matsakaiciyar fuska, mai kunshe da manyan fararen idanu, hancinta a mike kamar biro, Labbanta kamar an tsaga da reza, ga shafaffan kundukuki.Tana sanye da wani Wata doguwar Riga mai launin ja wacce taji ado da duwatsu, kanta sanye da gyale baki,
Salman yace
"Ke maxa kisameni a Daki, inason magana dake, bai jira abunda zatace ba ya wuce, Binsa tayi da kallo tarasa abunda ke damun Dan uwanta nata cikin yan kwana kinnan.Gashi, Babu Sadi babu labarin sa kodai sun samu matsalane dashi, gashi nakirashi ya amsa ya kashe wayan koh lafya? Itada zuciyarta take wannan zancen,
Tashi tayi tabi bayansa, dakinsa ta shiga kai tsaye, a tsaye ta ganshi ya rike k'ugu.*©ZAZZAU*😘
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.