🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January 2017*
9⃣Dakin Ammi ta nufa tana zuwa tafada kan jikinta, kuka take kamar wata jaririya, abundai babu kyan gani sai Wani shagwaba takeyi wai ita ala dole auta, nikam nace autar banza dai da haka iyaye ke bata yayansu, dazaran kikace ma yaro auta Toh duk wata tabara ta tabbata akansa Daman shi yaro kadan yake jira.
Ammi tace
"ke Dallah yi mana shuru har yanzu kinki ki girma kwanan nan fah zaki fara higher institution, wannan shagwabar yace ace kin barta haka gashi har na samu siriki".Juyowa NASREEN tayi tace "Nidai gaskiya Ammi kiyiwa yaya magana Kullun bashida wata magana saina in rabuda SADI Ammi nidai gaskiya shinake so babu Wanda nake kulawa kingama yanzu marina yayi wai saina rabuda sadi".
"Kwarai saikin rabuda shi saboda ba kalanki bane, gwamma tun wuri kinsan inda zakiyi shuka tayi yabonya, inba hakaba Saina ballaki inga ubanda zai kwashe ki a balle".
Ammi tace
" Inyehhh!!!!! Lallai ne Salman wuyanka yayi kauri, ba kunya ba tsoron sarkin gari? Neema'a Wah Nushuuf (maji ma gani) inkai ka haifeta dazaka rabata da abunda takeso, bari kaji indai ina Raye babu Wanda zaima tilon yata dole babu".
Ammi na lura duk ke kike daure mata gindin yin duk abunda takeso, yaza'ayi Dan Allah kamanni ace bazan ba Nasreen sha'awara ta daukaba, nagaya mata sadi mashayin giyane manemin matane amma takiji.Kuka yasaka, ya fice daga Dakin, NASREEN tace "Ammi karki yarda da abunda Salman yake cewa wallahi sharri yakewa Sadi saboda sun samu wata matsala Dan Allah Ammi ki taimakeni in auri Sadi Ammi Dan Allah",
Meye na kuka ai kamar anyi an gama tashi maza kije kiyi sallah ki kwantar da hankalinki jibi Alhaji zai dawo za'ayita ta kare".Cikin murna NASREEN ta mike tanata tsalle Ammi binta kawai takeda kallo tace,
"waiyo yata ta kamu da So, kamar ba haka nima aka sha gwarama kafin in auri Alhaji ba, nayi kuka nayi kuka gashi yanzu nikejin dadii".NASREEN zabin Allah kawai Nike nema miki, inhar Sadine mijinki babu makawa saikin aureshi.
NASREEN ce zaune tana game a cikin na'ura mai kwakwalwa Wato(Computer).
Karajin wayarta taji tashi guda takai duba ga lambar datake kiranta,
A zuciyanta tace waye me wannan lambar lokaci guda ta daga lokacin tana gan da katsewa, "Hello"
tace kamar yadda tasaba wata murya taji Wanda dadinta ya zarce Wakan Ala,
Lokaci guda bugun zuciyanta yakara hauhawa,
"Dafatan kina Lafya Gimbiya sarautan mata, Dan Allah kice wani Abu kozanji dadi"
cikin shagwaba yake magana gaba daya taji jikinta ya mace gaba daya, gyra zama tayi tace
"Lafya lau nake amma zanso insan dawa Nike magana?"."Nasan cewa ni bakone a wajenki, amma zanso kibani zuwa wani lokaci koda zakisan koni waye, amma the most important shine Sanin sunana,
Dafarko dai sunana
ABBA MUSTAPHA
Dafatan kin gamsu"
Shuru tayi don ina iya cewa har bacci tafara saboda dadin maganarsa,
"Hello are you dere?"
Da sauri NASREEN tace
"yes inadan nazarine"
"Ba matsala yaushe kikeso inkara kiran ki don muryarki dadi takemum, kaman sarewa"?NASREEN tarasa meke mata dadii,
"Duk lokacin daka kira ina maraba da kiranka".Wani ihu yayi yace,
"Tnx alot my Princess you deserve to be honoured zakiji dadin kasancewa taredani, saina nuna miki *Pure Love* Wanda da wuya wani mahaluki yayi miki irinshi, lets call it a day".
Baijira abunda zatace ba kawai ya katse wayar, abun mamaki lokaci guda naga Nasreen tana murmushi gamida kallon fuskan wayarta, can nakara ganin ta juya muryarsa kawai take tariyo wa, magana take a zuciya amma har saida tafito Abba mustapha Nyc name.BAYAN
KWANA BIYUMahaifin su Salman ya dawo, bayan yahuta ya natsane,
Salman ya nufi falonsa farawa yayi da gaidashi daga bisani yafara,
Sanar dashi abunda ke faruwa tsakanin NASREEN da SADI
"Abba, wallahi sadi bai dace da Nasreen ba nayi nayi ta fahimceni amma ina abun yaci tura Abba ba mutumin arziki bane karshenta ayi auren taje ta dawo, Abba ninasan halin Sadi koda nake abota dashi Nasan takuna, abun haushi Abba harda sha giya, ga mutanen arziki amma taki basu dama su turo".Ran Abba ya baci, yace
"Baba karami tabbas koh bayan baraina Nasan cewa kai mutumin K'warai ne, zaka rik'e NASREEN cikin aminchi, Kuma zan kirata zan sanarda ita mahimmancin auren mutum nagari".Salman yaji Wani dadi gar cikin ransa, tashi yayi yafita,
Dukda fadawa son Musty datayi bai hanata ganin girman matsayin Sadi ba, don Babu gudu Baja dabaya.*LARABA*
Akace tabawa rabar samu,
A Ranan akayi sallama cewa ana sallama da Abban su salman,
Sakkowa yayi falon baki yace, ayimishi iso da bakon ace yashigo, Abba koh kyau sai Wanda yagani dukda bawani shekaru Abban su salman ya bashiba amma har kasa ya durkusa ya gaidashi kalmashe kafa yayi ya zauna a kasa, suka farada gaisuwa Abba yace
"Tashi ka hau kujera haba Yazaka zauna a kasa"
Amma atafau yaki zama, Sunkuyar dakansa kasa yayi yace,
"daman Alhaji nazo Neman irine acikin gidannan, Shiyasa naga bai kamata inyi Abu dakaba, shiyasa nazo nace insameka inji koh anyi mata mijine?"Abba ya gyara zama, yace "gaskiya wannan shine tsarin da addini ya tanada, idan kaga yarinya kanaso gidan su zakazo kasamu iyayenta kafin ka fara ganin yarinya koh zuwa zance,
Toh Alhamdulillah naji dadii indai NASREEN ce batada wani miji tsayayye a yanzu sannan kuma zaka iya zuwa wajenta a koda yaushe".Bakaramin dadii Abba yajiba,
"yace nagode kwarai Allah yasa ayidamu"
Amin.
Nan aka kawo mishi kayan motsa baki Wanda shi awajenshi basu Dada shi da kasaba, saboda shi yafison komai natural.BAYAN SATI DAYA
Sadi yarasa abunda yakemai dadi, baya samun wata kulawa daga wajen NASREEN ka yawan fushi da take dashi,
Wata safiyar juma'a ne sadi ya tashi da matsanancin ciwon kai Wanda baya rasa nasaba da damuwa dayasa kansa aciki.Kubiyoni donjin
Shin NASREEN zata aminche da soyayyan Musty?
Shin Yazatayi da Sadi?
Shin Sadi zai hakura da Nasreen?
Meye Asalin labarin su Sadi da Salman?*©ZAZZAU*😘😍
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.