🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔*NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄*January2017*
1⃣2⃣*Dutse*
Mikewa Sadi yayi yana salati yana sanarda ubangiji, saboda wani mummunan mafark'i, daya tashi dashi
"Daga hannu yayi sama yana rokon Allah, Allah yasa mafarkinsa karya zama gaskiya don rabuwa da nasreen baxai iyaba, dafe kai yayi lok'acin da Adil yafito daga cikin toilet, shima ya dauro alwala suka fita zuwa masallaci Al'adar gidansu ne dazaran an dawo masallaci sai anbi koh ina cikin gidan an gaida kowa dayake katone amma Kuma ginin zamani.
Dakin hajiya Nana shine Daki na karshe da suka shiga, zaune take tana Jan chalbi, zama sukayi akan Carpet kamar masu karbar gafara.Hjya tagama Adu'oin ta, juyowan dazatayi kawai sai cewa tayi,
"yau naji munafukan yara Saiku wani zauna a kasa salon wancan ifiritin tace ninace kuzauna akasa"
Tashi sukayi tsam suka tsugunnan sukace "barka da safiya Hajiya Dafatan kin wayi gari cikin koshin lafya?
"Lahhh!!!!! Kai wayannan yara akwaiku da kini bibi daban tashi cikin koshin lafya ba zaku ganni zaune anan? Daba a gadon asibiti zaku ganni ba?""Shidai Adil yak'asa cewa komai, tashi yayi yace mutumina saika fito, zandanje inzagaya koh Allah yasa adace"
Fitansa keda wuya Hajiya ta juyo kan sadi tace,
"Dalilin dayasa na kiraka shine, kaki aure yanzu Sadi a shekarunka? Gasu musa duk sunyi aure da yayansu, kabarni cikin gidannan da abun fade?"
Kuka hajiya ta fashe dashi shikam sadi hankalinsa yayi kololuwar tashi "Hajiya kinsan hawayenki azabane kike karamun a wajen Allah hajiya wallahi duk abunda aka gaya miki karyane wallahi karyane so kawai ake a hadani dake, Hjy nayi Rayuwa mai muni ada amma a yanzu nazama abun kwatance saboda NASREEN itace silar komai Kuma ita nakeda burin in aura".Zare ido hajiya tayi tace, "kul kul Sadi nayi maka mata tunkafin kak'ai haka don hak'a nibansan wata nasara ba komi ma kace sunanta, Toh AMLA itace matar Dana zaba maka wacce zata zama uwar jikokina".
Cikin tsananin razana Sadi yace "Hajiya zanyi miki komai amma banda auren Amla, yaza'ayi in auri wacce nayiwa tsarki nagama ganin duk wata suran jikinta? Haba hajiya impossible, this can happen hajiya ki canza shawara".Hajiya tace sannu, toh baka isaba Kuma tuni magana takaiga manya, koh mahaifinka baice Ah ah ba bare kai yarinya mai mutunci da kima mai Sanin girman manya, Sadi zakayi Alfahari da AMLA cikin yardan Allah, dakake cewa ka gama ganin suranta ai tuntana karamane, yanzu kuwa ai igiyar rakumi tayi nesa Dana kaxa,
Sannan ba sha'awara nake baka ba Umurni ne sannan yaxama wajibi kayi biyayya".Waiyo Allah na nikaina saida Sadi yabani tausayi, kamar zanyi mishi kuka, shiru yayi yace Hajiya AMLA itace zabinki amma kisani zabita itace NASREEN, banida wacce nakeso nake muradin zama da ita sai Nasreen,
Sannan Daidai da yini guda bantaba jin ina son Amla ba
Kuma duk abunda yaje ya dawo kekika jawo".Fuuuuu yatashi harya isa bakin kofa hajiya tace
"Karka sake ka taka k'afarka ka koma Kano saboda babu dangin iya babu na baba, babu abunda katsinta sai ashararanci da".
Fit yafice Dak'i yashiga ya kulle kansa zuciyanshi kaman zai fashe saboda ruri datakeyi, wayarsa ya dauka lokaci guda ya kira lambar NASREEN, Wanda rabonsa da ita tun ranan da Sukayi fada da Salman."Hello" yafadi, cikin muryar ajalina yazo
NASREEN zan iya mutuwa daga yanzu zuwa gobe Dan Allah ki yafemun Darling I love you Kuma zan mutu da ciwon sonki banso na mutu ban ji dumin jikinki ba, Ashe burinmu bazai cikaba Nurul-Qlby"
Daga dayan bangaren, hawaye kawai Nasreen take don wannan shine Abu mafi muni data tabaji a rayuwanta, Wanda yakusa dode mata kunnuwa,
"Sadi ina sonka karka mutu kabarni meyasa kaddara take bibiyanmu haka Sadi zan iya rasa rayuwana nima matukar baka numfashi"............*©ZAZZAU*😍😘
YOU ARE READING
NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)
General FictionLabarin wasu Abokai dasuka taso tun yarinta Amma daga bisani, suka samu matsala abotar ta wargaje saboda SADI yace yana son NASREEN kanwar SALMAN.