NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani) Babi na sha Bakwai

409 15 0
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄

*January 2017*
1⃣7⃣

     Musty ne yace "yakamata amaryar tamu ta kwanan nan, ta bude idanunta muga juna kada wata rana Mu wuce juna ba tareda mun shaida juna ba, yaya ai kaga ai da anyi abun kunya"
Dam taji karjinta ya buga, tabbas wannan shine Abba cikin rada Afnan tace
"Dan Allah Kawata ki bude fuskanki"
Cikin yanga ta dago lokaci guda suka hada ido dashi taji wani kwarjinin sa ya ziyar ceta.

"Yauwa kokefa,
Gaisawa sukayi amma gaba daya NASREEN ta daburce "wannan shine Abba Wato shine yaki gayamun ainihin sunansa?".
Sunyi hira sosai amma nasreen taki sakin jiki dashi, don daganinsa tasan bai dace da irin mijin datake burin zama dashi ba,
Na daya miskili ne, sannan ga shegen sarauta kamar Kansu farau, daganin shi bazai ba matarsa cikakken kulawa ba.

Bayan sun gama hira, musty yace
"ina fatan ranar wata gudan da'aka samana baiyi nisa ba?"
Lokaci guda idon NASREEN yaciko da kwalla,
"Ke nake saurare idan baiyi ba koyayi yawa kifada sai asan yadda za'ayi?"
Nasreen tace
"Ai ni babu abunda zance duk abunda aka zartar shikenan fatana shine Allah yayi mana zabi mafi Alkhairi".

Musty baice, komai ba amma yasan tunda Nasreen ta fadi wannan maganan toh dawalakin goro a miya, dayan biyo ko dakwai Wanda takeso koh kuma dole akayimata akaina?.
Tashi sukayi
Muzamu wuce Dan Allah idan mun bata muku rai kuyafe mana ai Tuni Afnan ta chabe tace,
"Lah mukam Baku mana komai ba, mungode kwarai sannan inafatan zaka rikemum Kawata bisa yarda da Amana, itakadai gareni,".

Murmushi musty yayi yace,
"Karkiji komai Afnan yanzu haka ina Gina wani kata faren Plaza Wanda da sunan NASREEN nake ginawa zanyi mata komai ganin nasata farinciki".
Fitowa sukayi farfajiyan gidansu, wani katon boot aka bude Nidai Humairah nakasa gane koh kayan Meye acikin boot din, mai gadinsu aka kira ya dinga sauke kayan itako Nasreen koh kadan basu burgeta ba, tunda ba sadinta bane yayi mata kyauta.
Saida aka gama sauke komai Musty ya fito da wani katon envelope ya mikawa NASREEN amma taki amsa Afnan Tuni ta zura hannu tace
"Inajin kunyanka takeji bari ni nabata dakaina".

Wani irin haushi Afnan takeba NASREEN, amma itako koh a jikinta cewa take yaushe zan bari abun ungu ya wuceni daga baya in bige da cizon yatsa?.
Nimadai Afnan dinnan haushi take bani akwaita da katsalandan nikam nace anya bazata ba NASREEN  matsala ba kuwa anan gaba?? Muje zuwa wai mahaukaci yahau kura.

Bayan tafiyan sune, Nasreen tace
"Gaskiya Afnan kin batamun rai bariki ji ingaya miki har yanzu Sadi nakeso kuma shi nake kauna don haka kinga wayannan komatsan kidauka ki tafi dasu don naga jikinki sai wani rawa yakeyi lashe money kawai
Kodai wansa zakiso tunda ni kanin kesona kinga ai dukkansu arziki garesu",
Afnan taji zafin kalaman NASREEN tashi guda tace
"Kawata meyayi zafi shiba wutaba, maida wukan kube bani nakai zomon ba ratayan ma ba'a baniba".

Kudin ta shige dasu ciki Ammi ta mikawa tace,
"Ammi nizan koma dare yasoma yi" kudin mota Ammi tabata masu tsoka,
Ficewa tayi don koh tsayawa bitakan Nasreen batayiba.

Nasreen taja dogon tsaki ta shige ciki,
Ammi tasamu zaune
"Gaskiya Ammi Afnan ta gizgani yau bakiga wani rubbish datake ba wannan ai saisuce kwada yayyune mu don nayi mata magana shine taji haushi ta tafi toh tafi ruwa gudu shiyasa nifa in banda su ikram dasu Nana don suna cousin dinane su shiyasa nake sake jiki dasu amma irinsu afnan Ammi saisuyi embarrassing din Mutum in public wallahi".
Ammi binta takeda kallo tace
"Ina gaya miki wannan tunba yauba trust no one but your self saboda human being are wicked they can hurt you in many ways, shiyasa for the first place na nuna banason k'wancenki da Afnan amma kika nuna ke ina toh gashinan idan zaki kiyaye ta dayafi miki".

BAYAN SATI BIYU

Abubuwa da dama sun auku, ciki harda arresting din Salman da akayi sanadiyyan giya dayasha yayi tatil ya bige wata mata har yakaiga ya kasheta har lahira, shiko musty Tuni yayi revealing kansa awajen Nasreen yana iya kokarinsa wajen ganin ya faranta mata amma ina Kullun bata bashi full concentration dinta,
Biki sai karantowa yake anfara shirye shirye gadan gadan yan gidansu musty saboda sonda sukema Nasreen musamman suke kwaso zuga don azo aganta, uwar mijinta kuwa waya akai akai abun kara daurewa Nasreen kai yake "Wane irin laifi nayima Sadi da Kullun sai munyi waya saina gayamai halinda nake ciki amma bashi babu alamansa?".
Itakadai take wannan tunanin.

Abbansu Nasreen kuwa, yayi mata kaya nagani na fade, a Afnan furnitures dake cikin garin kano akaje aka siyo mata kaya,
abun farin ciki shine yadda Abba yake ririta Nasreen saboda tana shirin amincewa kudirinsa,
Bashi da wata magana saita Nasreen komai ya siya Nasreen,  itakoh sai rama takeyi dukta fita hayyacinta, Kullun saita kaiwa Allah kukanta amma ina kwanaki kara karatowa suke.

*Nida masu karatu bamusan wa Nasreen zata auran ba,*
*Sadi ne koh ko musty? Gashi Abu sai matsowa yakeyi*.

*©ZAZZAU*😍😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 31, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)Where stories live. Discover now