NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani) Babi na biyar

204 7 1
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY👄*

*January 2017*
5⃣

Cikin sanyanyar murya, tace
"yaya gani"
juyowa yayi a fusace cikin karaji yace
"NASREEN
meye halakarki da SADI?"
Shuru tayi kafin ta tattara natsuwarta waje daya,
"Saurayina ne mana wani abune yafaru dashi koh koh mene ne?"
Salman ya dafe kai yakoma gefen gado ya zauna, yana salati yana sanar da ubangiji.
          "Har tsawon wani lok'aci kuka dauk'a kuna soyayya daban sani ba sai yanzu?"
"Nifa yaya ban ganeba sai wani damuwa kake shin meye aibun sa? Tsawon inajin shekara uku kenan muna soyayya dashi".

Dafe kai yayi yace "Nasreen Kinsan cewa ina sonki bazan so abunda xai cutar dake ba koh, Kinsan cewa banida wata kanwa data wuce ke?
Toh inaso inbaki sha'awara a matsayina na dan'uwanki kuma maison cigaban rayuwanki, dafatan zaki bani hadin kai?"
Shuru tayi nadan lokaci tace, daga bisani tace
"ina saurarenka matukar bai sabawa shari'ar Allah ba".
Salman ya matso kusada Nasreen yace inaso ki rabuda SADI saboda bai dace dake ba be chanchanci zama wani bangare a rayuwarki ba".

Cikin rashin fahimta NASREEN take kallon Yayanta, cikin tashin hankali da rashin Sanin madafa,
"Haba yaya meyasa zak'ace na rabuda abunda na fara so a fark'on rayuwana? Meye aibun Sadi bayan yana sona meye dalilinka na rabani da masoyina inada buk'atar kwakkwaran hujja?"
Nasreen tsaye tayi ga AC a Dakin amma zufa kawai tak'eyi, jikinta sai tsuma yak'eyi, shiko Salman yarasa ta inda zai fara fahimtar da Nasreen.

"Nasreen Sadi mashayin giyane, sannan mayaudari ne bashida wani buri illah ya lalata rayuwar yarinya yayi dumping dinta, manemin matane na karshe sannan Rabin darensa a Club yakeyi, kanwata meye abunso acikin irin wannan mutumin? Wanda bashida qualities dinda mace takeso take burin samu, don haka kiyi gaggawan rabuwa dashi".

Nasreen tace
"gaskiya yaya ban yarda ba, sadi bai taba nunamun irin wayannan abubuwan daka lissafo mun ba, saboda tun haduwana dashi yamun Alkawarin daina duk wani Abu dukda bai sanar dani ko meye ba, sannan koda wasa Sadi bai taba rikemun hannuna ba, bare kuma Mu hada kafad'a, Sadi bai taba yimun maganar banzaba, bantaba ganinshi koh jinshi cikin maye ba, yaya taya kak'eso na yarda da kalamank'a akan Sadi?"

Tana gama magana ta ruga aguje tashiga Daki, ta kulle kuka kawai tak'eyi,
"Dan Allah wane irin abune wannan, tabbas a shirye nak'e inhar halin Sadi kenan saina canzashi zuwa mutumin Kwarai saboda bazan iya rabuwa dashiba, amma kuma wani hanzari ba gudu ba, dafarko Dana bukaci in sanarda yaya akan soyayya Mu Sadi cewa yayi kar'in kuskura in fadamai, Dana bukaci insan dalili sai cemun yayi kunyarsa yakeji".

Cikin Daren Nasreen tunani kawai, tak'eyi gashi takira sadi kusan sau Goma amma baya dauk'an wayanta, mahaifiyarsu ce tazo wucewa, taji kaman motsi k'utsa kai tayi cikin Dakin taga Nasreen zaune ta zabga uban tagumi.
  "NASREEN lafiya bakiyi bacci ba, har Kusan karfe biyu na dare"?
"Ummi Wallahi dayake nayi bacci da rana Shiyasa na nemi baccin narasa amma yanzu nake shirin kwanciya",
Ummi dai kallonta tak'eyi amma tasan cewa tanada damuwa fal acikin ranta, "Maza ki kwanta saboda yanzu zakiji ankira sallan asuba" Toh tace.

Fitanta keda wuya, bacci mai nauyi ya dauketa bata farkaba sai wajen karfe Tara na safe saboda makara koh sallar Asuba batayiba, cikin hanzari tayi Alwala tayi sallah tana idarwa ta fada toilet tayi wanka, ta Sanya bakar jallabiya, Laure ce tashigo tace "uwar dakina kifito inji Ummi kuyi breakfast!!".

   Ya mutsa fuska tayi tace
"Laure kice mata fita zanyi inna dawo zanyi".      bata jira abunda Laure zatace ba, ta dauki Jakarta da,mukullin mota tafice..
Bata zarce koh inaba sai wajen Aikin Sadi dake Chalawa Wanda awa daya tayi kafinta isa saboda traffic da ake yawan samu acikin garin kano.

Garin kano dai yakasance cibiyar kasuwanci ta daya a arewa inda dubban mutane daga kasashen da muke makota ka dasu kamar nijar, kamaru da chadi, suke shigowa don siya da siyarwa, a arewa dai birnin kano shine babban birni Wanda yakeda kananan hukumomi 44 sannan garine Wanda yafi kowani gari yawan mutane a arewa.

Tana isa tayi packing motarta, a waje inda tafito wani tagani dagani shima ma'aikacine a wajen,
"Salamu alaikum"
Cikin sauri ya waigo tareda amsa mata sallamar,
"Dan Allah sadi nakeso kataimaka ka kiramum, kace yayi bakuwa a waje".
Ba musu ya nufi inda ogan nasa yake aiki musabaha sukayi yace
"Yallaboi kayi bakuwa tana waje".

Sadi ya mike yace ni koh Adil?
Ah ah oga kaitace, Toh k'ace inadan wani aiki amma ganinan zuwa, Adil ne yashigo da sauri yace
"mutumina k'abar Aikin nan zan k'arasa Gimbiyace a waje" jiyayi gabansa ya fadi fitowa yayi a hankali kamar wani Wanda akace EFCC tazo tafiya dashi, waige yake amma baiga Nasreen ba, tabayansa tafito tace "gani sai wani mik'a wuya kak'e".

Dariya sukayi gaba daya, Sadi yace
"Nasreen inadai fatan lafya yadda naga baki taba zuwa wajen aikina ba yaukuma saigaki?"
Shuru tayi tace    "Eh a gaskiya lafya ba lafya ba mezai hana musamu waje Mu zauna?"
"Muje office koh?
Da sauri tace ah ah badadewa zanyiba gashi ma na katseka kana cikin tsaka da aiki, bakomai wata yar inuwa suka samu suka zauna suna kallon juna.

Nasreen tafara magana, tace
"Rabin jiki meyasa kake kin daukan wayata? Saikace nayi maka laifi koda yake laifin wani yakan shafi na wani Toh inhar takasance haka bakayimun Adalci ba,
Sannan naxo maka dawasu maganganu Wanda bansan yaxaka daukesu ba,"
Sadi yace ina saurare.

"Yayana jiya yake gayamun wasu abubuwa Wanda bantaba ji koh gani daga gareka ba, inaso kafitar dani daga  rudanin Dana tsinci kaina daga jiya zuwa yau, yace mun kai mashayin giyane, manemin mata mayaudari inaso inji gaskiyar magana daga bakinka karka boyemun kayi tunanin zan rabu dakai nidakai mutu ka raba takalmin kaza".

*Shin Sadi zai gayamata gaskiya kohkoh zai boye mata? Inya fadi mata meye makomar saoyayyansu?*

*©ZAZZAU😘*

NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)Where stories live. Discover now