Babi na d'aya

4.1K 198 13
                                    

Ma'anar sunan littafin;- Kwaiseh na nufin kyakkyawa da harshen shuwa. Maryamah kuma suna ne kaman yanda kowa ya san ana kiran Maryam da Maryaamah.

💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
Rigar jikinta ta ja ta goge dan guntun hawayen da ya sauk'o mata sannan ta ci gaba da wasa da k'afafunta da ke cikin kogin, can ta ga kifi yana gibtawa dan k'arami da shi, har tasa hannu ta cabko shi ko me ta tuna ta sake maidashi cikin ruwan, ta waiga dama ta waiga hagu bata ga kowa ba, kuma ga rana rau a kanta, ya zata yi ta d'aura ruwa a kan jaki ita d'aya?

ga shi bata koma gida da wuri ba, yau kam ta tabbata sai Amty Babbe ta kusa sumar da ita. Ta fidda k'afafunta daga cikin ruwan ta fara kokuwa da k'aton kwano, tana yi tana tsoron kada ya fad'o yayi lamba ta shiga uku, sai ta fara dagawa sai ya yi santsi ya koma k'asa.

Yarinya ce 'yar kimanin shekara takwas, in ba ka kula da d'an kunne da ke kunnenta ba bazaka tab'a d'auka mace ba ce kallon d'a namiji zaka yi mata, duk da ko d'ankwali bata da shi.

Dalili kuwa shine toliya hud'u ne a jere a tsakiyan kanta, gefen duk an aske shi tankwal da gani sabon aski aka mata, haka zalika an raba kowane toliya an aske, sai ya zama daga toliya na farko sai aka aske na biyu sai toliya na uku an aske na hudu, a takaice dai gashin kanta kaman kitson kalaba guda hudu ne masu shegen tsayi, kuma hakan yana daga cikin Al'adun shuwa arab, ana ce masa gudd'iye.

Chab a ka d'auke kwanon ruwan ana mata dariya, aka ajiye gefe sannan aka d'aga ta chak aka d'aurata kan jakin, bata tsorata ba dan ta san ko wanene.

"Saleh tun dazu nake jiranka"
Ta nuna masa ranan da ke samansu.

"Ammi Jidda ya sani tafiya da shanunsa, gudowa na yi dan in rakaki bayan gari sai in koma".

Bata sake masa magana ba shima bai mata magana ba har suka fara tafiya, yana jan jakin yana tafiya ita da kwanonta a saman jakin, ta rungume kwanon wai kada ya fad'i, idonta rau-rau tana juye-juye, ko me take nema oho, sai da ya iso inda suka saba tsayawa sannan ta umarcesa da tsayawa a wurin.

Bai yi musu ba ya tsaya, ya d'aure kwanon da igiya da kyau a jikin jakin sannan ya sauk'o da ita.

"Matsoraciya, babu wanda zai ganmu"
Murmushi ta yi, cikin rashin sanin abunda zata ce masa.

Har ya juya ya tafi bata bar wurin ba tana kallonsa, hawaye ke zuba a kuncinta, duk da karancin shekarunta ta san me sonta kuma ta san me kinta. Ta tabbata Saleh yana daga cikin masu sonta a cikin dajin nan.

D'an k'aranin daji ne da mutane 'yan kad'an, ba za su wuce hamsin ba, yawanci wadan da suka manyanta ne mazauna garin, yawancin samari da matansu suna yawatawa a fadin duniya dan samun wurin ciyar da dabbobinsu, wasu har abada basu dawowa gida wasu kuma suna dawowa jifa jifa sannan su koma, gari ne dan karami da suka sa masa suna Godil, suna da rafi madaidaici sannan kuma akwai 'ya'yan itatuwa da ciyayi, abinda ya basu kwarin gwiwan zama a wurin kenan dan basu rasa ciyawa dan k'ananan dabbobinsu.

Dafata aka yi ta baya, firgigit ta juyo ta ga k'awarta ce Khajije, sa'anni suke, ita ma da gudd'iyenta ba d'ankwali, murmushi ta k'ak'alo wanda bai kai zuciya ba.

"Baki koma gida ba har yanzu?"

Ta janyo bakin riganta tana goge wa Maryamerh hawayen fuskanta, sannan ta janyo hannunta har suka isa k'ofan gidansu Maryamah.

"Ki shiga, tunda kullum ba a rabaki da kuka ke kam. Ba zan iya shiga ba dan amty in ta ganni zata koreni".

Maryamah gyada kai ta yi ta janyo jakinta ta shiga cikin gidan zuciyarta a cunkushe ko sallama babu.

Kwaiseh MaryaamahHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin