CHAPTER ELEVEN

473 24 0
                                    


        Aliyu a daren yaje yata kiran number ta baya shiga, daga baya yayi deciding ya buga musu kofa. Bayan ya buga kofa Faruq ya bud'e mishi kofan, bayan sun gaisa Aliyu yace
   "Ummm sunana Aliyu, brother Fido"
  "Ohh Allah sarki, ya gida?"
    "Alhamdulillah lafiya kalau, Fido nake nema kuma I tried calling her but her number was switch off kuma munyi da ita akan zanzo na d'auke ta"
   "Ohhh ayyah kasan daman ba wanda zai kwana a gidan and d'azu naji kamar Eesha tana cewa zaka zo ka d'auke ta. Lemme talk to her"
   "Ohk Nagode"

      Faruq ya shiga ciki sai kusan bayan minti biyu ya fito tareda Eesha, Eesha tana ganin sa tayi murmushi tace
   "Ango kasha k'amshi, baka had'u da amaryar kaba?"
Aliyu ya d'an sosa kansa yace
  "Wallahi kuma munyi zanzo na d'auke ta"
   "Kuma wallahi haka ta fad'a mini har tace bara ta fita da wuri dan bakasan actual gidan nan ba, ka kirata?"
   "Yeah na kirata but her number a kashe"
  "Ya Salaam! Ohk give me some seconds let me call my sis koh ta koma gidan mu, mushiga daga ciki"
  "Aiit nagode"
 
   Bayan sun shiga ciki suka zauna a parlour.

    Shiga d'aki tayi ta d'au wayarta tafito parlor, number Anty Halima tayi dialing, bayan ya shiga ta saka a loudspeaker
  "Hello amarya lafiya kuwa?"
  "Anty Halima ina Fido? Tana gida neh?"
  "A'a Fido fa bata nan, tace mun Yayan ta zaizo ya d'auke ta a gidan ki, mesa kika tambaya?"
  "Wlhy Yayan tane yazo kuma batanan and number ta akashe"
  "Ikon Allah, toh ina tashiga? Allah sa lafiya"
"Ameen Anty Halima"
"Ki kira wasu koh Allah zaisa kiji labari"
  "Ohk toh nagode, bye" ta katse wayan.

    Eesha ta kalla Aliyu tace
  "Kaji bata wajen, but bara nakira Anty Rif"
   A take tayi dialing number Anty Rif itama yayar Eesha ce, tana d'aga wa tace
  "Amarya lafiya kika kirani hope baki manta komai a gida ba?"
   "Lafiya kalau wallahi, amm daman Fido nakeson na tambaye ki koh kin ganta da zaki bar gida nah"

  "Ohh Fido, da zan wuce na ganta tsaye da Issam abokin Faruq. Har naji yana maganan zai kaita gida"
  "Ohk toh Nagode" ta katse wayan.

    Zuciyan Aliyu neh yake bugawa, tabbas ya ganeh Issam dan da akayi posting pictures nasu a Facebook yaga an saka sunan sa. Take yace ki kiramun number Issam d'in.
  Take Eesha tayi dailing amma shima switch off. Tace
"Yaya Aliyu number sa akashe, inaga ya kaita gida neh. Tabbas ba inda Fido zata wuce gida ya kaita"
  Faruq yace
  "I trust my friend ba inda zai kaita sai gida, kaje gida In Shaa Allah tana gida"

    Aliyu duk yadda yaso ya b'oye b'acin ransa amma sanda suka gane. Yayi murmushin dole yace
  "Ba komai nagode"

     Tafiya yake a cikin motar sa amma zuciyan sa yana me bugawa, tsananin kishi ya rufe masa Ido, buga siterin motan yayi yace "Auren mu saura one week amma tana kula wani, wallahi Allah sai ta ganeh kurenta"

   A haka har ya isa gida, yana shiga cikin gidan wani irin parking yayi ya fito a motar da sauri, direct b'angaren Inna ya wuce. Yana shiga ya ganta da Shamcy suna kallo a parlour. Inna tace
  "Aliyu lafiyan ka kuwa? Har yanxu baka wuce gidan ka ba?"

   Bai bata amsa ba yace
     "Inna ina Fido?"
   "Kaji ja'irin yaro, toh Fido bata gidan nan gidan auren k'awarta zata kwana"
  "Inna kina nufin Fido bata dawo gidan nan ba?"
  "Toh karya zan maka neh?"

  "Kee Shamcy ina Yayar ki?"
   "Yaya Aliyu bata dawo gida bafa, ka manta yau ana auren k'awar ta Eesha? Sai gobe zata dawo"
"Bata dawo gida bafa kukace?"
Inna ta harare sa tace
  "Ka fara zautuwa neh? Sau nawa zamu fad'a maka bata gidan nan tana gidan aure"
  "Inna bata wajen auren dan daga can nake, ance wai an ganta tareda wani"
  "Kaga Aliyu bana son shirme, toh Fiddausi d'in binshi zatayi gidan sa sabida an gansu tare? Maza ka tashi ka tafi gidan ka dare yayi"
  "Inna baki yadda dani ba kenan?"
  "Ban yadda ba, kuma idan ka k'ara cewa Fido ta fita da wani toh ban yafe ba duniya da lahira, kai Allah ya isa ma"

HAYAATEEY (Completed✔)Where stories live. Discover now