CHAPTER TWENTY THREE

408 28 1
                                    


    Mutuwar zaune tayi data karanta, zuciyanta na mai wani irin bugawa, ba wannan baneh mutuwar auren ta na farko amma wannan yafi mata tashin hankali fiyeda tashin hankalin daya sameta gidan Yaya Aliyu. Take ta fisga motar ta tana wani irin gudu akan titi har takai gidan ta, wani irin horn takeyi amma shuru, sauk'a tayi a cikin motar ta ringa buga gate nan ma shuru gate d'in ma a rufe da k'aton padlock. Zama tayi dirshan a bakin gate d'in ta rushe da sabon kuka, yi take har sanda muryan ta ya dashe hawayen ta suka tsaya. Ga wani irin ciwon kai da jiran dake d'eban ta. Ganin mota tayi anyi parking nashi dai-dai inda take, Mummy da Yaya Khaleal da Shamcy neh suka fito a cikin motar. Mummy ta sunkuya kusa da ita tace
   "Habibty baya cikin gidan neh?"
  Tana kuka tayi hugging nata tace "Mummy gidan rufe, bansan ina Issam yake ba, bansan a wani irin hali yake ciki ba, gashi ya sake ni Mummy na shiga uku"
Bubbuga bayanta take a hankali tace
  "Shhhh! Baki shiga uku ba Habibty, In Shaa Allah everything will gonna be alright yanzu ki tashi mu tafi gida kusan k'arfe biyu fa"
  "Mummy ni bazanje ni gida ba sai naga Issam, Mummy wallah...."
  "Shhhh kiyi shuru Fido a daren nan ina zaki samu Issam? Kibari da asuba sai mufita neman sa kinji dan yanzu ba inda zaki same sa"
  Da k'yar ta lallashe ta suka sakata a mota sai gida, a gidan ma kuka take sosai koh wani minti biyu sai ta duba agogo taga koh k'arfe hud'u yayi. A haka batayi bacci ba anyi-anyi da ita ta kwanta amma sam taki kwanciya har k'arfe hud'u yayi. Tana ganin k'arfe hud'u ta tashi tace ita sam asuba yayi zata fita, haka Mummy da Inna sukata bata hak'uri ta bari k'arfe biyar yayi, da k'yar ta iya jira zuwa k'arfe biyar, k'arfe biyar nayi tace zata tafi, Inna ta rufo k'ofa tace sam sai taci abinci, da k'yar ta yadda ta iya shan Tea kad'an tace ya isheta, had'ata da Yaya Khaleal akayi ya kaita duk inda takeso. Suna cikin mota Yaya Khaleal yace
  "Fido yanzu gidan ki zan kaiki koh ina?
  Fido da tayi zuru zuru daga jiya zuwa yau har ta wani rama idonta ya fito murya a dashe tace
  " Gidan Eesha zan fara zuwa"
  Direct gidan Eesha yayi da ita, da d'an gudu-gudu tashiga gidan tana kwad'a sallama, da sauri Eesha ta fito a d'akin ta tace
   "Fido lafiya? Ina kiranki jiya da daddare bakya picking calls nace da safe zanzo na duba ki"
  "Ina Issam?"
Ajiyar zuciya Eesha tayi tace
  "Da asuba suka bar asibiti jirgin shi zai d'aga Abuja 7:00am"
Take ta d'aga idonta dan ganin agogon dake mak'ale jikin bango taga 6:59 "Ohhh shit!" Ta furta a hankali tafita a gidan da gudu tashige motar tana haki tace
  "Yaya Khaleal muje airport and please drive fast idan bazaka iya gudu ba ka sauk'a kaban waje naja"
  Fisga motar yayi yana wani irin gudu akan titi, duk gudun da yakeyi gani take kamar baya tafiya, 7:12 dai-dai suka shigo cikin airport. Da gudu tashiga wajen ta tambaya akace mata yanzu yanzun nan jirgin ya d'aga. Fita tayi a guje ta same Yaya Ahmad tace
  "Can you drive me to Abuja?"
  "What! Abuja kuma? Bakida hankali neh?"
  "Dan Allah kayi hak'uri idan bazaka iyaba ka sauk'a kawai zan iya driving da kaina wallahi Allah"
  Tausaya mata yayi sosai yace
  "Toh shikenan barana kira gida"
  D'aukan wayar sa yayi ya kira Mami ya sanar da ita, ta musu Allah kiyaye hanya kuma yace ta fad'awa Mummy da Inna. Bayan sun gama wayan ya fisga motar sai hanyan Abuja, gudu yake sosai akan titi Fido gani take kamar ma baya tafiya taja dogon tsaki tace
  "Dan Allah ka sauk'a naja motar nan"
  Wani uban speed ya k'ara yana tafiya at 100, ni kaina sanda na tsorata a irin gudun da sukeyi, wata motace babbar Daf take zuwa ta gaban su kan su matsa gefe suka shige daji, yayi×2 ya danna brake amma ina is too late suka buga wata bishiya sai ga motar tayi kaca-kaca.....

_After Eight Hours (Bayan awa takwas)_

     A hankali take bud'e idonta ga wani irin ciwon kai dake addabar ta harta bud'e idonta gaba d'aya. Tunani take meya faru da ita har aka kawo ta asibiti dan da ganin cikin d'akin asibiti neh ga drip dake mak'ale a hannun ta. Sallamar da Doctor tayi shineh ya dawo da ita daga dogon tunanin data fad'a, Murmushi Doctor ta mata tace
  "Ya jiki k'awata"
Da k'yar ta iya furta "Da sauki"
  "Meke damun ki yanzu, any pain?"
  "Kaina neh ke ciwo ga jiki nah ba k'arfi"
  "Karki damu zaki samu lafiya In Shaa Allah"
  "Dr please meya faru dani? Wannan wani asibiti neh?"
  "Don't stress yourself karki damu kinji"
  "I need to know neh, ina 'yan uwana?"
  "Gaskia kam you really need to know, accident kukayi a hanya shineh aka kawoku National Hospital, nan Abuja ne, had it been namijin da kuke tare dashi ya farka da ban fad'a miki ba, nida mijina a idon mu accident d'in yafaru shineh muka d'auke ku muka kawo ku asibiti Allah yaso ma ina aiki anan. But karki damu mun d'au wayar ku munga last dialed number suna Mami kuma munyi calling nasu yanzu suna hanya ma"
  Yanzu neh abun ya dawo mata kai, wani sabon tashin hankali ya taso mata
  "Dr ya jikin shi yake?"
Murmushi tayi tace "Karki damu zai samu sauki In Shaa Allah don't worry. Yanzu nurse zata shigo da abinci idan kinci zata baki magani kisha"
  "Ohk Thank you"
  "Zan wuce sai da safe"
  "Yanzu k'arfe nawa neh?"
"8:20pm, karki damu na kira mutanen gida kan nashigo d'akin nan ma sukace already suna cikin abuja so any moment from now zasuzo"
  "Ok nagode sosai Allah saka da alkhairi sai da safe"
  "Ameen! Goodnight"

     Dr tana fita a d'akin Fido ta damke idota tacire drip da aka mak'ala mata a hannu. Da k'yar ta iya tasowa dan ta bugu akanta sosai gashi goshin ta duk bandage, neman hijabin ta tayi dan ta rufe kanta amma bata gani ba, a k'arshe purse nata tagani a kan kujera ta d'auka tafita a d'akin ba d'ankwali duk suman kanta a waje. D'akin gefen ta tashiga tayi sallama taga wata yarinya mai kimamin shekaru goma sha bakwai a d'akin ga mata kuma kwance kan gado. Bayan sun gaisa Fido tacewa yarinyan
  "Sister dan Allah zan samu hijabi nayi sallah?"
  Murmushi yarinyan tayi tace
  "Mai zai hana na baki, gashi da gani kina jin jiki sannu Allah k'ara sauki". Hijabin gefenta ta d'auka ta mik'a mata, murmushi Fido tayi tace
  "Nagode sosai, d'aki nah shine next to you idan nagama zan aiko miki"
  "A'a karki sha wahala zanzo na karb'a da kaina"
  "Nagode"

    Fido saka hijabin tayi ta kama hanyan fita a asibitin, da k'yar ta samu k'ofan fita ta fice. Tana fita ta tsaida taxi tace masa Maitama. A daidai k'ofan gidan su Issam ta sauk'a ta biyasa kud'in.
Danna bell na gate d'in tayi sai ga mai gadi ya bud'e mata k'ofa. Bayan sun gaisa yace
  "Ikon Allah Hajiya sai yau d'azu naji labarin mai gidan ki ya dawo gida amma bamu had'u ba sabida naje sadakan uku an mana rasuwa kanna dawo akace mini ya koma amma. Hajiya duk yadda akayi ba lafiya ba naganki haka duk ciwo a jikin ki"
  Murmushi tayi tace "Lafiya kalau wallahi, Hajiya tana ciki?"
  "A'a fa bata ciki, Issam yana dawowa gida tace a fad'a mini zasuyi tafiya amma zasu dawo kwanan nan"
Zuciyan tane yayi mugun tsinkewa "yanzu kana nufin ba kowa a gidan?"
  "Wallahi ba kowa inaga suma ba lafiya ba dan tafiyar gaggawa sukayi"
   Wani jiri neh ke damun ta ji take kamar zata fad'i k'asa, kama kanta tayi ta rufe idonta dan Allah kad'ai yasan yadda takeji. Take mai gadi ya shiga gidan ya kira matarsa suka fito tare a lokacin har Fido ta fad'i k'asa
Yace "Haule taimaka ki shigar da ita cikin gidan ba Hajiya  tabaki mak'ulli kina shiga kina share gidan ba?"
  "Eh tabani". Da k'yar ta iya taso da ita suka shiga ciki ta bud'e mata cikin gidan tace
  " Duk d'akunan a rufe suke amma inaga d'akin mijin ki a bud'e yake"
  "Yana da d'aki neh anan side d'in?"
  Murmushi Haule tayi tace
  "Yana dashi, ai baison kwana acan sai anan sanda kukayi aure yake kwana a b'angaren sa"
  "Ina d'akin yake?"
Nuna mata tayi tace "Gashi can"
  "Nagode"
  "Ba komai barana kawo miki abinci da maganin ciwon kai"

  Fita tayi a parlour'n Fido kuma ta kwanta flat akan dogon cushion, cikin ten minutes saiga Haule tashigo da kwanuka da maltina tace
  "Hajiya ki tashi kici abinci bakida lafiya ga kuma maganin ciwon kai"
  Da k'yar ta iya ta tashi, wainan kwai neh da d'anwaken fulawa tace
  "Hajiya Allah sa zaki iyacin irin abincin mu"
  Murmushi Fido tayi tace "Shine favourite d'ina ma"
  Nan tafara ci a hankali tana shan maltinan, Haule tace
  "Hajiya na tambaye ki mana dan Allah"
  "Ina jinki"
  "Meya sameki haka naga goshin ki duk bandagi"
  "Hatsari nayi a hanyan zuwa na nan"
  "Allah sarki Allah baki lafiya"
  "Ameen"
"Ni zan wuce sai da safe"
"Allah kaimu"

   Bayan ta d'an ci kad'an ta wanke hannun ta tasha maganin da Haule takawo mata ba tareda ta duba sunan maganin ba, da k'yar ta iya tashiwa ta shiga d'akin da aka nuna mata na Issam. A hankali ta bud'e k'ofan k'amshin turaren sane ya dake hancin ta, ji take kamar yana cikin d'akin. Mutuwar tsaye tayi dataga pictures nata a duk jikin bango. Wasu tana restaurant, wasu tana coffeehouse, wasu tana tafiya, wasu tana cikin class, a ko wani hoto ya rubuta HAYATEEY boldly.. Bin pictures d'in take d'aya bayan d'aya tana shafawa tana hawaye!!!!!

   Many suna tambayana ina labarin Issam???? Please don't panic zakuji labarin sa next page In Shaa Allah

VOTE AND SHARE!!!

HAYAATEEY (Completed✔)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora