CHAPTER EIGHTEEN

373 23 0
                                    

[
       Tufa masa miyau'n bakin ta tayi tana hawaye tace
   "Bazan tab'a yafe maka ba k'azami kawai"
   Murmushi yayi yace
     "Mss Contour ai kece babbar k'azamiya tunda kika tufa mini miyau a jiki nah"
   Wani dogon tsaki taja tace
   "Aww daman so kake na had'iye wannan kayan k'azantan"
   Dole kuwa ki had'iya, zuwa yayi daf kusa da ita zata kurma ihu ya had'a bakin sa tareda nata had'e da damk'o hannun ta, sanda yayi kissing nata iya son ransa ya sake ta, wani irin bak'in ciki neh ya cikata nan take ta fashe da wani irin kuka, rungumo ta yayi sosai ya matso ta ajikin sa yace
  "Don't cry Hayateey, I really don't wanna see you cry"
  Da k'yar da iya furta
    "You're hurting me!"
  "Oshhh! Sorry" ya raba jikin sa da nata, har yanxu hawaye take, zuwa yayi daf kusa da ita tana ganin haka ta damke bakin ta tarufe shi gam ita duk a tunanin ta kissing nata zaiyi tareda rufo idonta, murmushi yayi yafara lashi hawayen da suke sauk'o wa a kuncin ta, nan take ta bud'e ido zatayi magana yace
   "Idan kika kuskura kika bud'e bakin ki kinsan mai zai biyo baya"
   Jin haka yasa tayi tsit bata k'ara cewa komai ba har sanda ya lashe hawayen tas yace
   "Karki k'ara kuka kinji Hayateey?"
   D'aga masa kai kawai tayi yayi murmushi yace
   "Yawwa ga abinci na kawo miki kinji, banson zaman ki da yunwa" nan ma d'aga masa kai kawai tayi yace
  "Ni zan fita anjima kad'an zan dawo"
  "Ohk" ta amsa masa da k'yar, yana fita a d'akin take tabi bayan sa tace
   "K'azamin namiji kawai, wallahi ban yafe maka ba!"
Tana ganin ya juyo nan take ta rufe kofan tasaka lock, zama tayi dirshan a k'asa ta fashe da wani irin kuka, yi take har sanda tagaji dan kanta tashige toilet ta ringa goge jikinta da soso, bakin tama yafi sau hamsin tana saka toothpaste tana brush....

   Bayan ta fito ta d'aga dogon kayan daya yaga, har aranta taji haushi dan kayan ya mata kyau sosai, zama tayi akan dressing mirror tashafa cream, bayan nan ta nema wani doguwar riga armless tasaka ta zuro hijabi tayi sallah Asr, bayan ta idar ta bud'e ledojin da Issam yashigo dasu, fried rice ne,  sai chips da kwai, shawarma, icecream, da coke. Cin fried rice d'in take tana shan icecream da already yayi melting. Bayan ta cika cikinta ta bud'e data ta tashiga email ta turawa class-reps akan su shirya gobe zatayi lecture, tayi fixing na 'yan part two zatayi 9:00am, part four kuma zata shiga 11:00am. Daga nan ta kashe data ta dan batason damuwa, latsa number'n Shamcy tayi yana fara ringing tasaka wayar a loudspeaker, Shamcy tana picking call d'in tace
   "Adda Fido gaskia nayi fushi, ina kiranki baki picking kuma you dnt bother to call back"
  Ajiyar zuciya Fido tayi tace
   "So sorry Swthrt! Guess what?"
   "What?"
  "Ina KT!"
Ihu Shamcy tayi tace
   "Are you serious?"
  "Mtssw kinga nayi kama da wacce zata miki k'arya"
"Kai dad'i na dake Adda Fido yawan tsaki, please ki daina babu kyau"
   "Zakizo ne koh kuwa?"
  "Dole nazo Adda Fido"
  "Ohk toh bara na tura miki address d'in"
   "Karki damu nasan gidan"
   "Yaushe kika san gidan?"
  "Kedai nasani"
"Ohk toh" ta katse wayan.

Kwanciya tayi akan gado tana tuna irin wulak'ancin da Issam ya mata, wani shu'umin murmushi tayi tace "Wallahi Allah sai kayi dana sanin had'uwan ka dani"
   Laptop nata ta kunna tafara duba lectures da zatayi wa students nata gobe, cikin thirty minutes sai ga Shamcy tashigo d'akin, wani tsalle tayi ta rungume Fido tace
  "Gaskia Adda Fido nayi farin ciki da kikazo ki KT dan nayi missing naki sosai"
   "Mtswww sati d'aya shine har kinyi missing na? Kinga ni banson munafurci fad'a mini taya ki kasan gidan nan?"
  "Ai Adda Fido tunda kuka tafi muke zuwa gidan da Mami dubawa, kayan akwatinan kima mu muka kai miki"
  "Shineh dan wulak'anci kikayi pretending kamar bakisan da zuwa na ba?"
  "Ya wuce Adda Fido"
   "Karki k'ara kirana da Adda I told you times without number"
  "Sorry Yar! Yawwa me acikin ledojin nan?"
  "Duba ki gani"

   Bud'e su tayi tana ganin chips tace "Yawwa Alhamdulillah kamar kinsan abunda nake son ci kenan"
   Tana sakawa a baki ta yamutse fuska Fido tace
   "Ke lafia kuwa?"
  "Kinsan bana cin Chips da sanyi"
   "So? Akwai wanda yasaki dole ne?"
   "Nan ta ajiye Chips d'in ta d'au shawarma da coke, tace "Adda Fido ai da sai ki saka icecream d'in a fridge tunda yayi melting"
  "Tunda kinzo ba sai ki saka ba, ni tunda nazo gidan ma banga fridge ba"
  Dariya Shamcy tayi tace
    "Anyi 'yar kauye, bakiga fridge a parlour'n kiba?"
  "Ban lura ba toh Malama"
    "Bara na lek'a kitchen ina zuwa"
   D'aga mata kai kawai Fido tayi Shamcy tabar d'akin. Can kusan after twenty minutes taji gidan ya d'auka da k'amshi, nan ta tashi tace "Bara naje na duba mai yarinyan nan takeyi haka"
  Bata sha wahalan neman kitchen d'in ba dashike tana jin k'aran kwanuka, shiganta ta tsaya tana k'arewa kitchen d'in kallo, babban kitchen neh wanda yasha furnitures masu kyaun gaske tsaya describing na kitchen d'in b'ata lokaci neh, Shamcy tace
  "Adda Fido ya kin tsaya kina kallon kitchen d'in haka? Ya had'u koh?"
   Yamutse fuskan ta tayi tace
  "Ni banga had'uwar sa ba, what are you cooking haka inajin k'amshi?"
  Murmushi Shamcy tayi tace
   "Liver sauce, perper chicken, coconut rice"
"Ohk idan kin gama kisame ni, already magrib tayi ma"
  "Ohk toh"

HAYAATEEY (Completed✔)Onde histórias criam vida. Descubra agora