CHAPTER SIXTEEN

473 22 0
                                    

     Kwance yake akan kujera a parlour, ji yake zuciyan sa kamar an d'aura dutse mai nauyin gaske, duniyan ya masa zafi sai wasu zazzafan hawayen da suke sauk'a akan kuncin sa. Meena ce tayi sallama tashigo, dan tsaban bak'in ciki ya k'asa d'aga ido ya kalle ta, zama tayi a d'ayan kujeran da yake facing nasa tace
   "Moon of my life inata jira kazo ka d'auke ni shuru, nata kiranka a waya baka d'auka wa what happen?"
   Ji yake kamar ya tashe ya rufeta da duka dan bak'in ciki, ganin baida niyar amsa mata tace
  "Moon of my life dakai fa nake"
   Bud'e idanuwan sa yayi yana kallon ta, sai can da k'yar ya iya furta
    "Ki koma daga inda kika fito"
   "What! Me kake nufi?"
Wani tsawa ya daka mata yace
   "Nace ki koma daga inda kike, kije na SAKE KI SAKI D'AYA"

    Hankalin ta tashe hawaye yana sauk'a kan kuncin ta tace
"Yaya Aliyu mena maka? Mena maka da zaka d'auka wannan d'anyan hukunci?" Ta fashe da wani irin kuka.
   Tasowa yayi ya d'auke ta daga ita har jakarta ya fitar da ita a gidan sa, ya nuna ta da yatsa yace
   "Yanxu ba asara bibbiyu kikayi ba uku-uku kikayi. Na farkon shineh dalilin muguntarki 'yarki ta mutu, na biyu shineh mahaifanta kalau yake har koma tayi wani auren, na uku kuma shine mutuwar auren ki"
  Meena fashewa tayi da wani irin kuka ta durk'usa ta kama kafan sa tace
  "Dan Allah Yaya Aliyu ka taimaka mini, ka cece ni, kaine farin ciki nah, kaine jin dad'i nah, nasan na afka babban kuskure amma ka yafe mini wallahi zan gyara hali nah, wallahi ina k'aunar ka, ina masifan sonka, sonka neh sanadin abunda nayi, ka yafe mini dan Allah"
  "Bazan tab'a yafe miki ba Meena, bazan tab'a yafe miki ba. Kin kashe mini 'yata, kin rabani da masoyiyata, kin rabani da farin ciki nah, kin rabani da Fiddausi wanda a yanxu ta mini nisa sabida haka bazan tab'a yafe miki ba"

   Juyawa yayi ya shiga cikin gidan sa yaja door d'in. Kwanciya yayi a k'asan tiles yana mai wani irin nishi zuciyan sa kamar an zuba wuta. Tunanin irin wulakancin daya ringa mata yake, wasu zazzafan hawaye neh suke sauk'o wa yace
   "Ki yafe mini Fido, wallahi ina sonki, ina matuk'ar sonki, koda da rana d'aya ban tab'a tsanan ki ba kawai maganar baki neh, gashi yanxu kin mini nesa".



    S.A yace "Kin tabbata Fido, promise me you'll come back to me"
   Fido tace "I promise In Shaa Allah"
   Murmushi yayi yace "Nagode sosai Beauty, idan akwai abunda ya shige miki gaba just give me a call kinji? Ni bana k'auna ki zauna da wannan beast d'in"
   "Karka damu beast d'in bazai mini komai ba, bakaga koh a film d'in Beauty and the Beast ba?"
  "That's just a movie"
Fido tayi murmushi tace
   "I know just kidding you, but karka damu In Shaa Allah bazai mini komai ba"
   "Ohk zan tafi, take care"
   "Aiit Thank you! Bye"

      Fita yayi a d'akin, yana fita tayi ajiyan zuciya ta zauna ta bud'e kunun madaran da Dije ta kawo mata ta fara sha tana lumshe ido. Bayan ta gama sha tayi brush da alwala tayi sallah daga nan tabi lafiyar gado....

     Washegari da safe bayan tayi sallah ta shirya cikin riga da skirt atamfa super mai kyaun gaske ta yafa mayafin ta, ba k'aramin kyau tayi ba. Mum ce tayi sallama tashigo d'akin tana murmushi tace
   "Wow kinyi kyau"
Fido rufe fuskan ta tayi da tafin hannun ta tana murmushin k'arya. Mum ta kama hannun ta suka zauna bakin gado Mum tace
   "Kinsan mai yafaru jiya?"
Girgiza kanta tayi, Mum tace
   "Ina fad'a wa Issam an aura masa ke nan take ya farka, Fiddausi Issam yana sonki sosai dan haka ina rok'an ki dan Allah don't ever betray him cox it will break him into million piece of broken glass please"
   "In Shaa Allah Mum"
Rungumeta Mum tayi tace
  "Nagode 'yata, Allah miki albarka"

   Daga nan driver ya kaita asibitin, tana shiga d'akin ta gansa kwance yayi uban rama kamar ba Issam ba, zuwa tayi kusa dashi tana mai k'are masa kallo
   "Tun jiya na k'asa samun nutsuwa, ina cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, I can't really tell you how happy I am" tareda bud'e idon shi k'yar a kanta wanda tayi mugun tsorata dan ta d'auka yana barci, yace
   "Don't move back Hayaateey! Come closer to me"
   Tsayawa tayi cak a inda take, da k'yar ta iya bud'e baki tace
   "How do you know nashiga d'akin kuma nice?"
   Kirjin sa ya nuna mata yace
  "Zuciyata, my heart! A duk ranar da zan had'u dake sai zuciyana ya fad'a mini, kinsan dalili?"
   Girgiza kanta tayi, murmushi yayi yace
   "Because you are my HAYAT! Kece RAYUWATA"

HAYAATEEY (Completed✔)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant