CHAPTER TWENTY SEVEN

653 29 0
                                    


   Tun lokacin da Issam suka rabu da Fido a Lagos basu k'ara had'uwa. Tunda suka kuma gida Abuja ya daina magana sai "eh" koh "a'a". Har yafi Issam nashi na da miskili yanzu yafi abunda ake kira da miskili, ba yadda Mummy batayi ba akan ya fad'a mata abunda ke damunsa amma yace ba komai. Wata d'aya da dawowan su Salala ta haife kyakkayawar 'yarta, Issam ba tareda yayi shawara da kowa ba ya rad'a wa yarinyan suna FIDDAUSI amma yana kiran ta da Jannah. Abun ba k'aramin sosa masu rai yayi ba Mummy tayi masifa tayi fushi amma duk a banza baima san tanayi ba. Salala kam kullum sai ta sha kuka dan tun daga ranar da ya rabu da Fido a Lagos ya daina shiga harkar ta. Idan tana kuka sai ya zauna yata kallon ta yace "Kiyi hak'uri bayin kaina baneh na k'asa cire Hayateey a raina neh". Idan zai kira sunan ta sai ya kirata da Fido, idan ta nema hakkin ta suna raya sunna ba sunan da yake fitowa a bakin sa sai Hayateey~Fido, abun sosai yake cin ranta, a kullum sai taje wajen Mummy tana kuka tace "MUMMY GANGAR JIKINSA NA AURA, Mummy kisa ya sake ni dan bazan iya zama dashi ba". Haka kullum Mummy ta ringa bata hak'uri, ta kira Issam ta masa fad'a amma sai abunda yayi nesa.
  A haka har akayi shekaru biyu, kullum yakan shiga d'akin sa na cikin part na Mummy wanda akwai pictures na Fido yata kallo yana nunawa 'yarsa Jannah wanda a yanzu ta girma tana magana, kullum suna shiga d'akin suta kallon ta suna hira. Idan yana zaune ma Jannah takan ce " Daddy bazamu je wajen Hayateey ba?" Toh fa nan duk abunda yake zai tashi su shiga d'akin suta kallon pictures nata suna hira, baida abokin hira a gidan sai 'yarsa Jannah...
   Rana d'aya sun shiga d'akin da Jannah kawai yaga wayam ba pictures, ransa yayi mugun b'aciwa ya same Mummy da Salala suna d'aki suna hira, zama yayi shima yace
  "Mummy waya cire pictures na Fido"
A tsawace tace "Nice"
  "Mesa?". Ba k'aramin mamaki tayi ba da yake tambayan ta mesa, tace
" Awww duk abunda ta maka baka gani ba"
Salala ta fashe da kuka tace
  "Nidai Mummy ya sake ni wallahi nagaji da zama dashi idan bazaki sa ya sake ni ba zan tafi Yemen na kai k'ara wallahi nagaji"
  "Ki barni dashi nace bazai sake ki ba shida Fiddausi kuma sai a lahira duk abunda ta masa bai gani ba"
  Issam gathering confidence yayi yace
  "Mother ba abunda Fido ta mun, asalima ni na mata laifi. Kinsan me na mata kuwa? A ranar da b'arayi suka shiga gidan su Fido toh harda ni aciki"
  Mummy bud'e baki tayi tana kallon sa yacigaba
  "Tun ranar da naji labarin baban ta shi ya kashe mini Abba na d'au alkawarin sai naga bayan sa, banyi niyan kashe shi ba amma nayi alkawarin rabasa da duk properties nashi, na samu wasu gangs na b'arayi suka mini jagora na shiga gidan dan na karb'a duk k'addarorin sa nazo nasa a kashe yaron sa Ahmad wanda akafi sani da GONER, bayan mun shiga gidan na karb'a duk wasu takardun nasa yayi signing not knowing bakin su d'aya da Ahmad yasa su kashe ni, bayan mun fita naji tausayin su sosai nayi alkawarin zan maida musu da duk wani abunda na karb'a sai b'arayin da mukazo dasu suka harb'e ni a hannu suka karb'a takardun sukace Ahmad neh ya saka su, haka na sa ake mun bincike Ahmad shineh dalilin zuwa nah UK, tun acan na gano ba Dad nata baneh yasa a kashe Abba shineh suka had'a baki da governor akan zai biyasa, ita kuma ashe ranar dana shiga gidan su ta ganeh ni tayi alkawarin d'aukan fansa, shine dalilin da yasa tamun haka"
  Wasu kyawawan mari guda uku Mummy ta wanke sa dashi, ranta idan yayi dubu ya b'aci, hawaye take tace
  "Issam yaushe ka zama haka? Har zaka iya shiga cikin gidan su mutaneh da tsakar dare da suna sata? Ka bani mamaki, kaci amanar yadda dana makaa. Kaci amanar mahaifin ka, dukda munje court amma bamuyi nasaraba lokacin bai kamata ka d'au d'anyan hukunci ba, bai kamata sam kayi haka ba, ka bani mamaki, ka bani mamaki Issam. Sam ni yanzu banga laifin Fido ba dan hali d'aya kuke, duk kuka k'asa hak'ura Allah ya musu hisabi ranar gobe ku a dole sai kun d'au FANSA, yanzu suwaye suke shan wahala idan ba ku ba? kuma haka zaku dawwama cikin wahala dan bazan tab'a bari ka aure taba, tunba yau ba Salala take kawo mun k'ara akan gangar jikin ka ta aura ba ruhin kaba, yanzu inaso ka sake ta dan ba amfanin zama da mutum irin ka, baka dace da mace irin Salala ba sam"
  Zuwa gaban Mummy yayi yana hawaye yace
  "Mummy ki yafe mini, nasan nayi kuskure amma dan Allah ki yafe min, kuma bazan iya sakan Salala ba".
"Bazaka iya sakan taba?"
  "Eh bazan iya ba" ya fad'a hankalin sa a tashe, Salala ce ta taso tazo gaban sa tace
  "Zaka iya min rabin son da kake yiwa Fido? Karka min k'arya Issam if you lie to me i'll never forgive you for that"
  Girgiza kansa yayi yace "Kiyi hak'uri Matata amma bazan iya miki rabin son da nake yiwa Fido ba, but I promise with time kina sakani addu'a Allah yasa na iya miki"
  Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tace
  "Mummy kisa ya sake ni kawai" ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyan duk wani mai sauraro.
  Mummy a tsawace tace "Ka sake ta nace koh nayi fushi da kai, fushi na har abada"
  Hankalin sa neh yayi bala'in d'agawa muryan sa yana shaking ba wai dan yaso ba yace
  "Ni Issam na sake matata Salala saki d'aya, idan kin samu miji kiyi aure"
  A take Salala ta fita a d'akin tana kuka sosai, Mummy ma tana hawaye ta nuna masa k'ofa tace
  "Ka fita mini a gida"
Kallon ta yake da renannun idanuwan sa wanda sukayi jazur yace
  "Mothe..." Bai k'ara sa ba ta tare numfashin sa tace
  "I said OUT!!!!!!!"
  A sanyaye ya tashi ya bar wajen, side nasa direct ya wuce, ganin Salala tana kuka ya zauna kusa da ita yace
  "Me amfanin kukan da kikeyi bayan ke kika sa na sake ki"
  D'aga jajayun eyes nata tayi ta sauk'e su akan sa tace
  "Ka fad'a min good reason da zan zauna da wanda baya so nah?"
  "Koh sabida 'ya dake tsakanin mu"
  "Hakan na nufin sabida 'ya na zauna cikin kunci da bak'in ciki? Na tabbata 'yata baza tab'a so na zauna da wanda baya sona kuma bai d'auke ni a matsayin matar sa ba"
  "Shikenan Salala ya isa!". Ya tashi yabar wajen....

  _A  Bayan shekara d'aya_ (da shekara biyun dana fad'a muku shine ya kama shekaru uku kenan). Back To Asalin Labari

    Issam neh yashiga d'akin Mummy ya zauna ya gaishe ta, tun daga lokacin ba abun kirkin dake shiga tsakanin su sai gaisuwa, bayan sun gaisa zai tashi ya tafi tace
  " Son!" Nan ya tsaye cak dan rabon ta data kirasa da Son har ya manta
"Zauna mana"
  Zama yayi kansa a k'asa, tace
  "Gobe Salala zatazo Nigeria"
  "Allah kaimu"
"Ameen.... Zatazo ta gaishe ka, and kuma daga yanzu na baka izini kaje wajen  Fiddausi ku dai-dai ta"
  Take ya d'aga eyes nasa yana kallon ta he just can't believe abunda tace, murmushi tayi tace
  "I am serious Son, go don't loose her".
  Murmushi yayi yama kasa magana he is speechless rungume ta yayi ya fita a d'akin.......

   Washegari..... Ranar Aure

     Fido tasha gyaran jiki tayi kyau sosai, zuciyan tane yake mugun bugawa idan ta kalla agogo, d'aga sexy eyes nata tayi cike fal da hawaye tace
  "Yanzu k'arfe tara saura minti goma(8:50am)"
  Murmushi Eesha tayi tace
  "Karki damu k'awata nan da awa d'aya da minti goma zaki zama matar General Aliyu ki daina zumud'i time yanzu zai gudu"
"Mtsw Eesha zamud'i kuma? Auren nan fa ba yau neh na farko na ba, ina tausaya wa rayuwata zanyi  spending rest of my life da mutumin da bana so. No! nafi tausayawa Yaya Aliyu da zai aura macen da bata sonsa"
  Eesha zama tayi kusa da ita tace
  "Karki damu with time zaki fara son sa kuma ai jinin ki neh"
  Murmushi tayi tace
  "I hope so"

   Shamcy ce tashigo da gudu cikin d'akin tace
  "Adda Shamcy na had'u da Yaya Issam a corner'n layin gidan nan, ya tambaye ni me ake a gidan yaga taron jama'a na fad'a masa auren ki yau ya juya da motar sa ya koma"
Eesha taja tsaki tace "Yaushe muka rabu dake da har kika fita?"
"Wallahi Allah da gaske nake na fita wajen tela karb'an kaya nah d'inki ai, idan k'arya nake miki ki tambaye Yaya Khaleal"
Fido ta kama hannun ta tace
  "Karki min k'arya Shamcy ki fad'a min gaskia, idan har kika min k'arya zanyi fushi dake"
  "Wallahi fa nace miki Adda Fido Allah na gansa"

   Don't forget to share to your love ones!!!!

Vote!

  Comment

Don't be a silent reader!!!!

HAYAATEEY (Completed✔)Where stories live. Discover now