Kwance yake a gadon asibiti ya rame yayi duhu, kamar ba Issam wanda mata suke hauka akan sa ba, gefen sa Mummy ce zaune kan kujera ta rik'e hannun sa damuwa fal a fuskar ta. A tsaye kuma wani mutum neh rik'e da Cup yana addu'a yana tofawa cikin ruwan, bayan ya gama ya mik'a wa Mum yace
"Karb'i ki basa yasha, In Shaa Allah idan ana yawaita addu'a zai samu sauki, zan na zuwa ina masa addu'a and kuma yana tashiwan dare yana nafila, addu'oin da na basa yana karanta wa, zan wuce ana jirana, dan Allah ki tabbata yasha"
Karb'a Mum tayi tace
"Nagode sosai Mallam, In Shaa Allah zamu dage da addu'a"
"Ba komai Hajiya, ni zan wuce"
"Ka gaida gida''
" Gida zai ji" tareda da fita a d'akin.Mum mik'a masa tayi tace
"Ungo karb'a kasha Issam"
Juya kansa d'ayan gefen yayi yace
"Mum ki yarda dani yanxu sam bata raina na jima da fidda ita a cikin zuciya ta"
"Naji na yarda but dan Allah ka karb'a kasha"Mum ta taso zuwa inda ya juya tace
"My Son dan Allah ka karb'a kasha, shin bakayi Imani da qaddara ba?"
Shuru yayi bai amsa ba, tacigaba
*"What is meant for you, will reach you even if it is beneath two mountains. And what isn't meant for you, won't reach you even if it is between your two lips. Allah chose for you a spouse before you were even born"*Jikin sa yana kakkarwa ya kamo hannun Mum nasa ya rik'e gam yace
"Mother inason Fido, duk da tayi aure na d'auka sonta zai ragu amma kullum son ta yana multiplying acikin Zuciya nah, I don't really know how to explain this to you. Infacts words aiint enough to express how much I love her but ki yarda dani idan nace miki She's My HAYAAT, ITACE RAYUWA TA!"
"Shhhh My Son, a yanxu matar mutum kake magana, kayi istigfari karka yi sab'o, so ba hauka baneh, kata addu'a don shine maganin komai. Kasani matar mutum kabarinsa, ba wanda ya isa ya aura matar wani. Babu wanda ya isa!"A sannu da lallashi ta basa ruwan yasha.
_Bayan Wata Biyar_
Fido girki take a kitchen ta rame tayi baki sai ka rantse ba ita bace, gefen ta kuma Basma ce zaune akan keken ta, tayi girma sosai kamar wata 'yar shekara biyu. Basma ce tafara kuka gashi tana girki ta rasa yadda zata yi. D'aukan Basma tayi zuwa d'akin ta tahad'a mata Nan tabata tasha, da k'yar ta samu ta lallashi ta tayi shuru. Komawar ta kitchen taga an k'ara mata wutar girkin ta gas d'in naci sosai ga warin k'onan miya. Bud'e miyar da zatayi taga miyar ya k'one kurmus. Zuciyan tane yayi bala'in b'aciwa tasan kan tabar kitchen ta rage wutar. Fita tayi a kitchen d'in ta wuce d'akin Meena direct.
Meena, Teema da Ramlah neh zaune suna shewa. A tsawace Fido tace
"Uban waye ya k'ara mini wuta bayan na rage kan nabar kitchen d'in?"
"Uban ki" cewar Teema, kan tagama fad'a taji saukan mari mai kyau da lafiya a fuskar ta, Fido ta nuna mata yatsa tace
"Next time zan miki marin da yafi haka, ni sa'ar kice? Ni sa'ar kuce? Duk wanda ya k'ara tab'o ni a gidan nan wlh zan koya masa hankali 'yan iska kawai"
Ramla tace
"Kece babbar 'yar iska ai, wanda saura one week da auren ki kika kasa hak'uri kika kwana a gidan wani gardi"
"Shiyasa Miji nah har yau ya kasa had'a kwanciya da ita, me zaiyi da left over, second hand ai wlh.." Cewar Meena, bata k'arasa ba itama taji saukan mari mai rai da lafiya a fuskan ta. Fido tace
"Daga ke har mijin naki wallahi bana tsoron ku, shima daga yau na daina barin sa wallahi balle kannen sa, ku d'in banza" taja dogon tsaki tabar d'akin.Baki bud'e suke kallon ta, Ramla tace
"Wallahi bata isaba, zamu mata dukan gaske kan mubar gidan nan, wallahi baza taci bulus ba"
Meena tace
"Wallahi bata isa ta tab'a fata na nabar taba, tayi kad'an, sai ta raina kanta wallahi a yau d'in nan"Fitan Fido kenan taci karo da Eesha, nan take tayi gudu ta rungumeta ta fashe da kuka tace
"Eesha dan Allah ki taimaka mini, bazan iya zama a gidan nan ba, gidan nan idan banda bala'i da masifa ba abunda yake cikin gidan nan"
Eesha tayi hugging nata sosai tace
"Shhhh ki daina fad'an haka, duk abunda yayi farko toh hak'ika yanada karshe, muje d'akin ki"
![](https://img.wattpad.com/cover/118818216-288-k129051.jpg)
ВЫ ЧИТАЕТЕ
HAYAATEEY (Completed✔)
Любовные романыA story of twenty four young beautiful gurl name Fiddausi. Her Dad was killed by most hamdsomd guy in the country/ every girl's dream named ISSAM. All she ever pray is to avenge the death of her dear Father! Even though she's married but her fathe...