CHAPTER TWO

618 38 1
                                    


      Gudu sosai take kamar titin na ubanta tana sake sake a ranta, anya mutum tagani koh aljani, atake tace "No mutum neh" tare da bugan siterin motan ta, can tayi murmushi wanda ya bayyana dimple nata da fararen hak'oran ta tas tace "Ya Allah yanxu naga class d'ina, yanxu naga irin namijin da yakamata na aura, duk inda kake sai na nemo ka, sai ka soni, in my whole life ba namijin da ya d'aura ido akaina ba tare da yaji wani abu a QALB nasa  ba" haka ta cigaba da driving har ta iso cikin University Of Maiduguri, tana shiga ta wuce parking lot tayi parking motar ta, tafiya take kamar batason tab'a kasa har ta isa cikin faculty of science, direct Microbiology Lab tawuce tun kan tashiga take jin hayaniyan student, kas x3 k'aran high heel nata wanda yabawa students d'in shaidan lecturer su tashigo, tana shiga kaf lab d'in yayi tsit kamar basu suke hayaniya ba. Bayan ta nutsu ta ajiye jakar ta tace
"Sorry I am late" tafara musu lecture akan Mycology, batayi minti biyar ba taji waya yana ringing among the students, take ta k'ara murtuke fuska tace
"I guess this is the end of my lecture for the whole semester, I told you people time without number to switch off your goddamn freaking phone whenever ina cikin this this damn Lab, so you caused, till we met in my test and exams.... Bye" take ta d'au jakarta tafita a Lab d'in, zo kuga ihun students suna cewa we are sorry ma, wasu na dunduma wanda wayarsa yayi ringing ashar, wasu kuma suna zagin ta suna cewa 'yar k'arama da ita sai shegen fad'in rai kai k'ananan lectures akwai su da bak'in hali especially na Microbiology department.
      Tana fita ta wuce parking lot tashiga motar ta ta fisga da karfi tabar cikin makaranta, hankalin ta duk yana kan guy data had'u dashi

    Wannan kenan

Back to lbr

""Issam"" ta furta a hankali hawaye kwance akan fuskan ta, Tab'ata da kanwar ta tayi ta dawo daga dogon tunanin da ta fad'a, kanwarta tana kuka tana cewa
"Adda Fido sun kashe mana Daddy, Adda Fido ki duba Daddy fa baya breathing" wasu zafafen hawaye neh suka sauka kan kuncin ta atake ta rungume kanwar ta tana cewa
"Easy habibti, cool down Shamcy Dad bai mutu ba he is alive In Shaa Allah" tana shafa bayan ta

   Ogan b'arayin neh ya bushe da dariya yace
"Girl I never miss a target, ya jima da wulawa so sai kuyi hakuri" Issam ya cire bindigan sa ya saita akan Ogan su yace
"This is not our deal, bamuyi haka dakai ba how dare you" Ogan shima ya saita bindigan sa kan Issam yace
"Yeah naji bamuyi haka dakai ba, but munyi haka da Goner" Issam saka hannu yayi akai yace
"Ohh My God, how could he, how dare him" Ogan yace
"Duk d'aya kuke bird of the same feathers kaga tafiyar mu if you like ka zauna anan" take yayiwa sauran yaran sa hannu suka fita a gidan Issam ma yabi bayan su.

   Suna fita Fido da Kanwar ta suka fashe da sabon kuka, take su uku da mamar su suka d'aga Daddy'n suka sakashi a mota Fido ta fisga motar da karfi sai asibin NAKOWA Hosp,Suna shiga asibi nurses sukayo kansu, suna ganin bullet d'ayar Nurse d'in tace
"Sorry we can't help without a police"  Fido a tsawace tace
"WTF! what do you mean that you can't help sai mun kira police, can't you see he is dying" ta fad'a tana kuka, Nurse d'in tace
"Eh nagani but so sorry madam dole sai da sa hannun 'yan sanda"
"Excuse me! My name is not Madam, My Name is Fiddausi so please take note" take ta cire wayan ta tayi dialing number, ana picking tace
"Hello Yaya Ahmad its me Fido, kazo da police yanxu yanxu a nakowa hospital Daddy ba lafia" take tayi hanging call d'in tana zub da kwalla, ta rasa yazatayi sai safa da marwa takeyi a asibiti,  tana ganin wani doctor yafito acikin operation room taje takamasa tana kuka mai ban tausayi tace
"Please Please help my Dad, I can't live without him. I won't be able to bear my life without my Dad. Please help him!"
    Doctor ya juya ya tab'a Daddy yacewa Nurses su shigar dashi cikin Operation room, d'ayar Nurse d'in tace "but Doc" yace "shhh just shut up" haka suka shigar dashi cikin Operation room d'in suka kulle kofa. Wani saurayi neh yashigo wajen wanda ak'alla shekarun sa zasu kai talatin da biyu, dogo neh sosai bak'i  broad chest yana da dara daran ido sai dogon hanci da lips nasa moderate amma bak'i, kallo d'aya zaka masa kasan shi kyakkyawa neh amma kana kallon bakin sa zaka ganeh yana shan abu, tana ganin shi taje ta zube a gabansa tana kuka mei cin rai tana cewa
"Yaya Ahmad sun kashe mini Daddy, Yaya Ahmad I can't live without my Dad" Yaya Ahmad ya d'aga ta yace
"Haba baby'n Dad nata ki daina kuka, ki daina fad'an haka bashida kyau a musulunci, haba sai kace ba musulma ba kiyi imani da kaddara khairihi wa sharrihi kuma kisani EVERY SOUL SHALL TASTE DEATH" da kyar yasamu ya lallashe ta tayi shuru, mum da Shamcy kam sun gama kariya sunyi shuru, Fido ce zuciyan ta yake bugawa ita ba zama ba ita ba tsayuwa ba tana ta zirga zirga a wajen, Yaya Ahmad ya daka mata tsawa yace
"Will you stop moving around and gasping frantically like a lunatic"
"I can't Yaya, I just cant ! He's my other half, I love my Dad" a tsawace yace
"Just shut up gurl everybody loves his Dad so stop moving around like an insane lunatic"
Daidai lokacin wutan room d'in yakawo green, take duk suka zubawa kofan ido, doctor na bud'e kofan Fido taje takamasa tace
"Doc, tell me something"
"I am sorry we lost him, he is dead" cewar Doctor

HAYAATEEY (Completed✔)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang